Abin da ke Ciki
15 Ga Agusta, 2012
© 2012 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania. All rights reserved.
Na Nazari
TALIFOFIN NAZARI
24-30 GA SATUMBA, 2012
SHAFI NA 3 • WAƘOƘI: 65, 2
1-7 GA OKTOBA, 2012
Ka Nuna Halin da Ya Cancanci na ’Yan Mulkin!
SHAFI NA 11 • WAƘOƘI: 16, 98
8-14 GA OKTOBA, 2012
Ka Guji Faɗawa Cikin Tarkunan Iblis!
SHAFI NA 20 • WAƘOƘI: 61, 25
15-21 GA OKTOBA, 2012
Ka Yi Tsayayya da Shaiɗan Kuma Ka Guji Tarkunansa!
SHAFI NA 25 • WAƘOƘI: 32, 83
MANUFAR TALIFOFIN NAZARI
TALIFIN NAZARI NA 1 SHAFUFFUKA NA 3-7
Daniyel ya bayyana a annabcin da ya yi cewa a ‘kwanakin ƙarshe, ilimi na gaske’ zai ƙaru. (Dan. 12:4) Wannan talifin ya nuna yadda wannan annabcin ya cika a hanya mai kyau. Ya kuma ba da tabbaci cewa Yesu yana tare da waɗanda suke bauta wa Jehobah.
TALIFIN NAZARI NA 2 SHAFUFFUKA NA 11-15
Ka san ko su wane ne ainihi ’yan Mulkin. Wannan talifin ya bayyana abin da ake bukataa gare su. Ya kuma tattauna yadda suke nuna cewa suna ƙaunar ƙa’idojin Jehobah.
TALIFOFIN NAZARI NA 3, 4 SHAFUFFUKA NA 20-29
Shaiɗan yakan yi amfani da tarkuna dabam-dabam don ya hana mu bauta wa Jehobah. Waɗannan talifofin sun tattauna tarkuna biyar da Shaiɗan yake amfani da su: Na ɗaya, yin magana da garaje, na biyu tsoro da matsi, na uku, yawan jin laifi, na huɗu, son abin duniya, da na biyar yin zina.
A FITOWAR NAN
16 Taron Da Ya Bayyana Haɗin Kanmu Da Kuma Shirye-Shirye Masu Ban Sha’awa
30 Ka Tuna?
BANGO: Wani Mashaidi yana wa wani makiyayi wa’azi a yankin Bafatá a ƙasar Gini-Bisau
GINI-BISAU
YAWAN JAMA’A
1,515,000
MASU SHELA
120
NAZARIN LITTAFI MAI TSARKI DA AKE GUDANARWA
389