Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 7/15 p. 32
  • “Na Cika Muradina”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Na Cika Muradina”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Makamantan Littattafai
  • Na Yi Kusan Shekaru 70 Ina Bauta wa Jehobah a Cuba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Ki Gaya Masu Cewa Kina Kaunar Su
    Labarai
  • “Ba a Taɓa Nuna Mini Irin Wannan Ƙaunar Ba”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 7/15 p. 32

“Na Cika Muradina”

Shekaru 15 da suka wuce, Emilia tana hidima a matsayin majagaba na kullum. Da shigewar lokaci sai ta daina. Amma, kwanan nan, ta ga cewa ta fi yin farin ciki a lokacin da take hidimar majagaba, saboda haka, sai ta fara sha’awar sake zama majagaba.

Amma, aikin da Emilia take yi ba ya ba ta isashen lokaci kuma hakan ya sa ba ta farin ciki. Wata rana, ta ce a gaban abokan aikinta: “Da a ce za a iya rage mini sa’o’in da nake aiki da zan yi farin ciki!” Shugaban aikinta ta ji wannan batun kuma ta tambaye ta ko ta tabbata da abin da ta ce. Emilia ta ce haka ne. Amma, ana bukatar samun izinin darektan kamfanin don bisa ga tsarinsu, ya kamata kowane ma’aikaci ya ba da cikakken lokacinsa ga aikin. Sai ’yar’uwarmu ta shirya don ta yi magana da darektan kuma ta roƙi Allah ya ba ta gaba gaɗin yin magana da kuma natsuwa.

Sa’ad da take magana da darektan, Emilia ta yi magana da gaba gaɗi da dabara, kuma ta roƙa a rage mata yawan sa’o’in da take aiki. Ta bayyana cewa tana yin amfani da lokacin da ba ta aiki don taimaka wa mutane. Kuma ta ce ita Mashaidiyar Jehobah ce, kuma tana ƙarfafa mutane da maganar Allah. A wannan zamanin, mutane da yawa ba su san bambanci tsakanin nagarta da mugunta ba kuma suna bukatar ingantacciyar shawarar da ke Littafi Mai Tsarki don su yanke shawara mai kyau. Tana son ta samu lokaci don ta taimaka wa mutane, amma ba za ta yarda hakan ya rage ingancin aikin da take yi a kamfanin ba. Shi ya sa take bukatar a rage mata yawan sa’o’in da take aiki.

Darektan ya saurare ta kuma ya ce ya taɓa yin tunanin zama mai aikin taimako. Sai ya ce: “Don dalilin da kika bayar, zan amince da abin da kika faɗa. Amma, kin san cewa za a rage albashinki?” Emilia ta ce ta san da hakan, kuma idan da bukata, za ta sauƙaƙa rayuwarta. Ta ƙara cewa: “Babban muradina shi ne in yi abin da zai amfane mutane.” Darektan ya ce mata: “Waɗanda suke ba da kansu don su taimaki mutane suna burge ni sosai.”

Babu wanda aka taɓa rage masa sa’o’in aiki a kamfanin. Amma, an yarda Emilia ta yi aiki kwana huɗu a mako. Kuma abin mamaki shi ne, ba a rage mata albashi ba! Ta ce: “Na cika muradina, kuma yanzu zan iya yin hidimar majagaba kuma!”

Ka taɓa yin tunanin yin canje-canje a salon rayuwarka don ka soma hidimar majagaba ko kuma ka sake zama mai hidimar majagaba?

[Bayanin da ke shafi na 32]

Darektan ya ce mata: “Waɗanda suke ba da kansu don su taimaki mutane suna burge ni sosai”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba