Tattaunawa Tsakanin Wani Mutum da Mashaidin Jehobah—Shin Dukan Masu Adalci Za Su Je Sama Ne?
SHAIDUN JEHOBAH suna jin daɗin tattauna Littafi Mai Tsarki da mutane. Ka taɓa karanta wani abu a cikin Littafi Mai Tsarki da ka kasa fahimta? Kana son ka ƙara sanin wasu koyarwar Shaidun Jehobah ko kuma ka san dalilin da ya sa suka yi imani da wasu abubuwa? Idan haka ne, ka tambayi Shaidun Jehobah game da batun duk lokacin da ka haɗu da su. Za su yi farin ciki su tattauna waɗannan batutuwan da kai.
Tattaunawar da ke gaba misali ne na yadda Shaidun Jehobah suke yi wa mutane wa’azi. A ce wani Mashaidi mai suna Marcus ya ziyarci wani mutum mai suna Robert.
Mene Ne Waɗanda Za Su Je Sama Za Su Yi a Can?
Marcus: Kana ganin wane irin rayuwa ne masu adalci za su yi a nan gaba?
Robert: Ko da ana fama da wahaloli a nan duniya, na yi imani cewa Allah zai sāka wa masu adalci. Za su je sama.
Marcus: Wannan bege ne mai kyau. Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da abubuwa da dama da ake yi a sama kuma ya nuna cewa wasu mutane za su samu gatan zuwa sama. Kana ganin mene ne waɗanda za su je sama za su yi a can?
Robert: Za mu zauna tare da Allah muna yabon sa har abada.
Marcus: Lallai hakan yana da kyau. Amma kuma, Littafi Mai Tsarki ya tattauna gatan da waɗanda za su je sama za su mora da kuma aiki mai muhimmanci da za su yi.
Robert: Wane aiki ke nan?
Marcus: Aikin da littafin Ru’ya ta Yohanna 5:10 ya yi maganar sa. Ayar ta ce: “Ka [Yesu] maishe su su zama mulki da firistoci ga Allahnmu; suna kuwa mulki bisa duniya.” Robert, ka lura da aikin da ayar ta ce waɗanda za su je sama za su yi a can?
Robert: Wannan ayar ta nuna cewa za su yi sarauta bisa duniya.
Marcus: Hakan abu ne mai kyau, ko ba haka ba?
Za Su Sarauci Waɗanne Mutane Ne?
Marcus: To, tun da yake waɗanda za su je sama za su zama sarakuna, idan lallai za su yi sarauta, ba wajibi ba ne a samu talakawa? Zai yiwu ne mutane su yi sarauta amma babu talakawa?
Robert: Da wuya.
Marcus: Yanzu, tambayar da za ta biyo baya ita ce, Za su yi mulki bisa su wane ne?
Robert: Ina ganin za su yi sarautar mutanen da suka rage a duniya da ba su je sama ba tukuna.
Marcus: Da a ce dukan mutane za su je sama, da amsarka daidai ne. Amma ka yi la’akari da wannan. Shin zai iya zama cewa wasu mutane, wato, adilai ba za su je sama ba?
Robert: Ban taɓa jin haka ba.
Marcus: Na yi tambayar nan ne don abin da aka rubuta a Zabura 37:29. Don Allah ka karanta mana ayar.
Robert: To. Wurin ya ce: “Masu-adalci za su gāji ƙasan su zauna a cikinta har abada.”
Marcus: Na gode. Ina ne aka ce masu adalci za su zauna?
Robert: Ayar ta ce za su zauna a ƙasar, wato, a duniya ke nan.
Marcus: Hakika. Kuma zaman ba na ɗan lokaci ba ne. Ka lura cewa ayar ta ce za “su zauna a cikinta har abada.”
Robert: Wataƙila ayar tana nufin cewa masu adalci ba za su taɓa ƙarewa a duniya ba. Wato, wasu mutanen kirki da aka haifa za su sauya mu sa’ad da muka je sama bayan mun mutu.
Marcus: Mutane da yawa za su ɗauka cewa abin da ayar nan take nufi ke nan. Amma ba ka ganin cewa ayar tana nufin wani abu dabam?
Robert: Ban gane ba.
Aljanna a Duniya
Marcus: Yanzu, ka lura da wata aya a cikin Littafi Mai Tsarki da ta yi magana game da rayuwa a duniya nan gaba. Bari mu karanta Ru’ya ta Yohanna 21:4. Wannan ayar tana magana ne game da mutanen da za su yi rayuwa a nan gaba. Ayar ta ce: “[Allah] zai share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin ciki, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari sun shuɗe.” Babu shakka, wannan labari ne mai daɗi, ko ba haka ba?
Robert: Ƙwarai. Amma ina ganin wannan wurin yana magana ne game da yadda rayuwa za ta kasance a sama.
Marcus: E to, gaskiya ne cewa waɗanda za su je sama za su samu albarka kamar yadda aka ambata a wannan ayar. Amma ka sake duba ayar kuma. Me aka ce zai faru da mutuwa?
Robert: Ayar ta ce “mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba.”
Marcus: Hakika. Yanzu dai na tabbata ka san cewa idan aka ce wani abu ba zai ƙara kasancewa ba, abin ya taɓa faruwa. Ko ba haka ba?
Robert: Hakika!
Marcus: Shin, an taɓa yin mutuwa a sama ne? A nan duniya ne ake mutuwa, ko?
Robert: Lallai! Sai na yi bincike a kan wannan batun.
Marcus: Littafi Mai Tsarki ya ce wasu mutane masu kirki za su je sama amma ya sake cewa mutane da yawa za su zauna a nan duniya har abada. Wataƙila ka taɓa jin wannan sanannen kalamin: “Masu-albarka ne masu-tawali’u: gama su za su gāji duniya.”—Matta 5:5.
Robert: Ban taɓa jin haka ba.
Marcus: Idan masu tawali’u za su gaji duniya, wannan bai nuna cewa lallai za a samu waɗanda za su zauna a duniya ba? Waɗanda za su zauna a duniya za su more abubuwan da aka yi alkawarinsu a Ru’ya ta Yohanna. Za su ga gagarumin canji da za a yi a duniya don Allah zai kawar da dukan abubuwan da ba su da kyau, har da mutuwa.
Robert: Na gane abin da kake nufi amma ban gamsu ba.
Marcus: Dama da sauran bayani. Akwai ayoyi da dama da suka yi magana a kan yadda rayuwa za ta kasance a duniya a nan gaba. In kana da isashen lokaci, zan nuna maka wani nassi da nake so sosai.
Robert: E, ina da ɗan lokaci.
‘Mai Mugunta Ba Za Ya Ƙara Kasancewa Ba’
Marcus: Ɗazu, mun karanta Zabura 37, aya ta 29. Bari mu duba wasu ayoyi guda biyu na wannan zaburar. Za mu karanta aya ta 10 da ta 11. Don Allah ka karanta mana.
Robert: To. “Gama in an jima kaɗan, sa’annan mai-mugunta ba shi: Hakika, da anniya za ka duba wurin zamansa, ba kuwa za ya kasance ba. Amma masu-tawali’u za su gāji ƙasan; za su faranta zuciyarsu kuma cikin yalwar salama.”
Marcus: Na gode. Bisa ga aya ta 11, ina ne “masu-tawali’u” ko kuma nagargarun mutane za su zauna?
Robert: Ayar ta ce “za su gāji ƙasan.” Ina ganin wannan ayar tana cika a zamaninmu ne, domin a yanzu haka, mutanen kirki suna rayuwa a duniya.
Marcus: Haka ne kam. Amma, ka lura cewa wannan ayar ta ci gaba da cewa mutanen kirki za su more “yalwar salama.” Amma a yau, akwai salama ne a duniya?
Robert: A’a, babu salama.
Marcus: To, ta yaya wannan alkawarin zai cika? Bari in ba ka wannan misalin: A ce kana da gidan haya. Wasu cikin mutane masu hayan suna da kirki kuma suna kula da gidan, bugu da ƙari, suna ƙaunar waɗanda suke hayan tare. Za ka yi farin ciki cewa suna zaman haya a gidanka. Amma a ce wasu ’yan hayan ba su da kirki; suna ɓata gidan kuma ba sa zaman lafiya da maƙwabtansu. Mene ne za ka yi idan waɗannan masifaffun masu hayan sun ci gaba da ɓata gidan?
Robert: Zan kore su.
Marcus: Abin da Allah zai yi ga miyagun mutanen da ke duniya ke nan. Mu sake karanta aya ta 10. Wurin ya ce: “Mai-mugunta ba shi.” Ma’ana, Allah zai “kore” ko kuwa zai halaka miyagun mutanen da ba sa zaman lafiya da ’yan’uwansu. Sa’an nan mutanen kirki za su ji daɗin rayuwa a duniya cikin salama. Babu shakka, wannan koyarwar cewa mutanen kirki za su gaji duniya har abada dabam ne da abin da aka koya maka a dā can.
Robert: E, ban taɓa jin haka ba.
Marcus: Kuma kamar yadda ka ambata ɗazun, ba zai dace mu tattauna aya ɗaya ko biyu kawai a kan wannan batun ba. Hakika, muna bukata mu bincika ayoyi da dama daga Littafi Mai Tsarki da suka yi magana game da alkawarin da Allah ya yi wa mutane masu kirki. Amma, bisa ga ayoyin da muka karanta a yau, kana ganin zai yiwu ne wasu mutanen kirki su je sama, sauran mutane masu kirki kuma su zauna a nan duniya har abada?
Robert: Ba zan ce maka na’am ba. Amma kamar abin da muka karanta ke nan a Littafi Mai Tsarki. Ina bukatar yin bincike sosai a kan wannan batun.
Marcus: Sa’ad da kake yin bincike, wataƙila za ka samu wasu ƙarin tambayoyi. Alal misali, waɗanda suka yi rayuwa a zamanin dā fa? Sun je sama ne? Idan ba haka ba, ina suke a yanzu?
Robert: Waɗannan tambayoyi ne masu muhimmanci.
Marcus: Za mu tattauna hakan idan mun sake haɗuwa.
Robert: To. Sai an jima.