Akwai Wanda Za a Iya Amince da Shi?
BAYAN faɗuwar Berlin a shekara ta 1989, wasu asirai sun tonu. Alal misali, Lydiaa ta gano cewa a lokacin mulkin kama-karya na Jamus ta Gabas, Stasi, ko kuma Ƙungiyar ’Yan Tsaro na Ƙasa, suna da fayil da ke ɗauke da rahoton asirinta. Ko da yake Lydia ta yi mamaki cewa suna da fayil na rahoton asirinta, to, ta ma fi mamaki da ta ji wanda ya ba Stasi rahoton—mijinta ne. Wanda ta tabbata da shi ƙwarai ne ya ci amanarta.
Robert, wani tsoho ne da ya “daraja, ya so, kuma ya amince” da likitarsa ƙwarai, in ji jaridar The Times ta London. An ce likitar “mai alheri ne kuma mai juyayi.” Sai farat ɗaya Robert ya mutu. Ciwon zuciya ce, ko kuma gazawar jiki? A’a. Gwanaye sun kammala cewa likitar ya ziyarci Robert a gidansa, kuma ba da sanin Robert da iyalinsa ba, likitar ya yi masa allurar dafi. A bayyane yake cewa wanda Robert ya amince da shi ƙwarai ne ya kashe shi.
Lydia da Robert sun shaida mummunar sakamakon cin amana ƙwarai. A wasu yanayi sakamakon bai da muni haka. Amma, batun cewa wanda muka sani ne ke cin amanarmu ba sabon abu ba ne. Wani rahoto da wata ƙungiyar ƙirge ta Jamus ta bayar, a cikin littafinsu da ake kira Allensbacher Jahrbuch der Demoskopie 1998-2002, ta bayyana a wani bincike cewa waɗanda mutane kashi 86 bisa ɗari suka amince da su ne suka ci amanarsu. Wataƙila kai ma irin wannan ya faru maka. Saboda haka, bai kamata mu yi mamakin cewa jaridar Swiss Neue Zürcher Zeitung ta ba da rahoto a shekara ta 2002 cewa a ƙasashe da yawa da suka bunƙasa, “amince da juna yana ta raguwa na shekaru da yawa yanzu.”
Koyon Riƙe Amana Yana da Wuya, Amma Cin Amana da Sauƙi Yake
Mecece amana? In ji wani ƙamus, amana tana nufin gaskata da mutum cewa mai gaskiya ne sahihi kuma ba zai yi maka lahani da ganga ba. Koyon riƙe amana yana da wuya, amma cin amana da sauƙi yake. Abin mamaki ne da yake wa mutane wuya su amince da wasu saboda sun ga an ci amanarsu? In ji wani bincike da aka yi a Jamus a shekara ta 2002, “matasa 1 cikin 3 ne suke amince da wasu mutane.”
Muna iya tambaya: ‘Za mu iya amince da wani kuwa? Ya cancanta ne mu amince da wani da zai ci amanarmu kawai?’
[Hasiya]
a An canja sunayen.
[Bayanin da ke shafi na 3]
Wani bincike ya nuna cewa waɗanda mutane kashi 86 bisa ɗari suka amince da su ne suka ci amanarsu.