Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 6/15 pp. 3-6
  • Abin da Muka Koya Daga Tsarkakkiyar Hidimarmu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Abin da Muka Koya Daga Tsarkakkiyar Hidimarmu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • HIDIMAR KULA DA DA’IRA
  • ZIYARTAR ƘANANAN RUKUNONI
  • MATSALAR SUFURI
  • ƘARFAFA ’YAN’UWA SU SOMA HIDIMA TA CIKAKKEN LOKACI
  • ‘Bulus Ya Yi Godiya Ga Allah Kuma Ya Sami Karfin Gwiwa’
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
  • Na Ji Dadin Koya da Kuma Koyar da Wasu Game da Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 6/15 pp. 3-6

Tarihi

Abin da Muka Koya Daga Tsarkakkiyar Hidimarmu

Olivier Randriamora ne ya ba da labarin

“Na iya ƙasƙanta, na kuwa iya yalwata: a cikin kowace matsala, a cikin dukan abu kuma, an fayace mini in saba da ƙoshi in saba da yunwa . . . Zan iya yin abu duka ta wurin Kristi da yake ƙarfafani.”—Filib. 4:12, 13.

WAƊANNAN kalmomin manzo Bulus sun ƙarfafa ni da matata Oly sosai. Kamar Bulus mun koyi mu dogara ga Jehobah sa’ad da muke hidima a ƙasar Madagascar.

Ni da Oly mun riga mun yi alkawarin aure a lokacin da Shaidun Jehobah suka fara nazarin Littafi Mai Tsarki da mahaifiyarta a shekara ta 1982. Sai ni ma na fara nazarin Littafi Mai Tsarki kuma daga baya, Oly ma ta fara yin haka tare da ni. Muka yi aure a shekara ta 1983 kuma muka yi baftisma shekara biyu bayan hakan, sai muka fara hidimar majagaba na ɗan lokaci nan take. Mun soma hidimar majagaba na kullum a watan Yuli ta shekara ta 1986.

A watan Satumba ta shekara ta 1987, mun soma hidima a matsayin majagaba na musamman. Mun yi hidimarmu na farko a wani ƙaramin gari da ke arewa maso yammacin ƙasar Madagascar kuma babu ikilisiya a wurin. Madagascar tana da kabilu 18 da kuma dangogi da yawa kuma al’adunsu sun bambanta sosai. Malagasy ce harshen da aka fi amfani da ita a ƙasar duk da cewa kowace kabila tana da harshenta dabam. Saboda haka, muka fara koyon harshen da ake yi a garin da muke hidima kuma hakan ya sa mutanen garin suka karɓe mu da hannu bibbiyu.

Da farko, ina ba da jawabi kowane ranar Lahadi kuma sai matata Oly ta tafa mini ita kaɗai saboda mu biyu ne kaɗai a taron. Muna kuma yin dukan sassan Makarantar Hidima ta Allah, kuma matata takan yi kamar tana magana da wani. Sa’ad da mai kula da da’ira ya ziyarce mu sai ya ce mu sauƙaƙa yadda muke taron da yake mu biyu ne kawai, hakan ya taimaka sosai!

Ba ma samun alawus a kai a kai domin littattafanmu da sauran abubuwan da ake aika mana daga ofishin reshe ba sa isa wurinmu da sauri. Saboda haka, mun koyi lallaɓawa da abin da muke da shi. Akwai ranar da ba mu da isashen kuɗin mota zuwa taron da’ira da za a yi a wani gari mai nisan mil 80 daga inda muke zama. Sai muka tuna da wata shawara da wani ɗan’uwa ya taɓa ba mu: “Ku gaya wa Jehobah matsalolinku tun da aikinsa ne kuke yi.” Saboda haka, muka yi addu’a kuma muka yi shawara cewa za mu taka da ƙafa. Amma kafin mu fara tafiya wani ɗan’uwa ya ziyarce mu kuma ba mu kyautar kuɗi, daidai kuɗin mota da zai kai mu taron!

HIDIMAR KULA DA DA’IRA

An naɗa ni mai kula da da’ira a watan Fabrairu na shekara ta 1991. A lokacin masu shela da suke rukunin sun kai 9, kuma guda 3 sun yi baftisma. Bugu da ƙari, mutane 50 suna halartar taronmu. Bayan an koyar da ni a aikin kula da da’ira, muka yi hidima a wata da’ira da ke birnin tarayya, Antananarivo. A shekara ta 1993, aka tura mu wata da’ira da ke gabashin ƙasar. Rayuwa a wurin ta bambanta sosai da na birni.

Mukan taka da ƙafa na tsawon mil 90 kuma muna bin kurmi don mu ziyarci ƙananan rukunoni. Mun rage yawan kayanmu sosai. Ko da yake, duk lokacin da jawabin mai kula da da’ira ya haɗa da nuna fim kamar yadda ake yi a wannan lokacin kayanmu sukan ƙaru. Matata takan ɗauki na’urar nuna fim sai in ɗauki batirin mota.

Muna tafiya da ƙafa na tsawon mil 25 a kowace rana don mu ziyarci wata ikilisiya. Muna bin tsaunuka da kogi da kuma hanya mai laƙa. Wani lokaci, mukan kwana a gefen hanya, amma yawancin lokaci muna neman masauki a ƙauyen da ke kusa. Wani lokaci, mukan kwana a gidajen mutanen da ba mu taɓa saninsu ba. Bayan mun samu masauki, sai mu soma dahuwa. Matata za ta karɓi aron tukunya kuma ta je kogi ko tafki ta ɗebo ruwa. Ni kuma in ari gatari in sara icen da za mu dafa abinci da shi. Duk waɗannan abubuwan suna ɗaukan lokaci. Wani lokaci sai mu sayi kaza mu yanka kuma mu gyara.

Bayan mun gama cin abinci, sai mu je mu ɗebi ruwan wanka. Wani lokaci muna kwana a cikin kicin. Idan an yi ruwa kuma sai mu kwana a tsaye saboda ɗakin na yoyo.

Mun tabbata cewa muna yi wa waɗanda suka ba mu masauki wa’azi. Sa’ad da muka isa da’irar, yadda ’yan’uwan suke nuna mana alheri da karimci yana burge mu sosai. Godiyar da suke nunawa don ziyararmu ya sa ba ma tunawa da wahalar da muke sha a tafiye-tafiyenmu.

Idan muka sauka a gidan ’yan’uwa, muna farin cikin taimaka musu da aikace-aikacen gida. Hakan yana sa su samu lokacin fita wa’azi tare da mu. Ba ma sa rai cewa waɗanda suka ba mu masauki za su tanadar mana da kayayyaki da kuma abinci masu tsada.

ZIYARTAR ƘANANAN RUKUNONI

Sa’ad da muke ziyarar ƙananan rukunoni, muna farin ciki cewa suna fita wa’azi sosai a makon tare da mu. Sau da yawa, ba ma samun lokacin ‘hutawa’ ko kaɗan. (Mar. 6:31) A wani waje, wasu ma’aurata sun gayyaci mutane 40, wato, dukan waɗanda suke nazarin Littafi Mai Tsarki da su zuwa gidansu saboda mu taimaka wajen yin nazari da su. Matata Oly da ’yar’uwar sun yi nazari da mutane 20, ni kuma da ɗan’uwan muka yi nazari da sauran mutane 20. Muna yin nazarin da su ɗaya bayan ɗaya. Can da rana muka ɗan dakata don mu samu damar yin taron ikilisiya, bayan haka muka ci gaba da nazarin. Mun gama nazarin nan da muka soma da safe wajen ƙarfe takwas na dare!

Sa’ad da muka ziyarci wani rukuni dabam, dukanmu mun soma tafiya zuwa wani ƙauye da misalin ƙarfe takwas na safe. Dukanmu muna sanye da tsofaffin tufafi. Bayan mun yi doguwar tafiya sai muka isa yankin da rana. Muka saka tufafinmu masu kyau kuma muka fara wa’azi gida-gida. Gidajen kaɗan ne kuma masu shelan suna da yawa. Saboda haka, a cikin minti 30 muka kammala wa’azi a dukan yankin. Sai muka kama tafiya zuwa ƙauyen da ke gaba. Bayan mun yi wa’azi a wajen, sai muka fara wata doguwar tafiya zuwa gida. Mun yi doguwar tafiya zuwa yankin amma wa’azin da muka yi na sa’a ɗaya ne kawai. Da farko, irin tsarin wa’azin nan ya sa ni da matata sanyin gwiwa. Amma, ’yan’uwan ba su yi gunaguni ba. Sun ci gaba da kasancewa da ƙwazo.

Akwai wani ƙaramin rukunin da ke ƙauyen Taviranambo, a kan wani tsauni. A nan muka samu wasu Shaidu waɗanda suke cikin iyali guda kuma suna zama a cikin ɗaki ɗaya. Suna yin taro a wani ƙaramin gida. Sai ɗan’uwan da ya ba mu masauki ya fara ƙwala kira, yana cewa “’yan’uwa!” Daga can gefen kuma sai muka ji amsa “E!” Sai wannan ɗan’uwan ya sake cewa, “mai kula da da’ira ya iso!” Aka sake amsawa, “To!” Ta hakan aka sanar da wasu da suke nesa har ila. Nan da nan mutane suka taru, sa’ad da muka fara taron, mutane fiye da ɗari sun riga sun zo.

MATSALAR SUFURI

A shekara ta 1996 aka mai da mu wata da’ira da ke kan duwatsu kusa da birnin Antananarivo. Wannan da’irar ma tana da nata ƙalubale. Ba a yawan samun motar haya zuwa karkarar da suke wannan da’irar. Mun yi shirin ziyartar wani rukuni a ƙauyen Beankàna da ke da nisan mil 150 daga birnin Antananarivo. Muka samu wata babbar motar da za ta bi ta ƙauyen da za mu je, sai muka tattauna kuɗin da za mu biya kuma muka shiga motar. Ban da mu akwai wasu fasinjoji 30 a ciki da kuma saman motar, wasu sun kwanta a saman wasu kuma sun tsaya a bayar motar.

Ba da daɗewa ba, sai motar ta lalace kamar yadda aka saba, kuma muka fara takawa. Bayan mun yi tafiya na wasu sa’o’i, sai wata babbar mota ta zo wucewa, tana cike da kuma mutane da kaya, amma duk da haka, direban ya tsaya ya ɗauke mu. Sai muka tsaya a cikin motar tun da yake babu wurin zama. Muna kan tafiya, sai muka isa wani kogi amma ba a gama gyaran gadan ba. Muka sake saukowa kuma muka ci gaba da tafiya da ƙafa, daga baya muka isa wani ƙauye da wasu majagaba na musamman suke zama. Ko da yake, ba mu yi shiri cewa za mu ziyarce su ba, mun fita wa’azi tare da su yayin da muke jira a gama gyaran gadan kuma mu samu wata mota da za ta kai mu inda za mu je.

Mun yi mako ɗaya kafin wata mota ta sake wucewa kuma muka ci gaba da tafiyarmu. Hanyar tana cike da manyan ramuka. Sau da yawa, motar tana mutuwa a cikin ruwa, sai mu sauko mu tura ta kuma ruwan tana kai mana gwiwa. A wasu lokatai, mukan faɗi a cikin ruwan. Bayan ƙarfe 12 na dare muka isa wani ƙaramin ƙauye sai muka sauka. Muka bar hanya, muka ci gaba da tafiya cikin gonakin shinkafa da ke cikin fadama mai ruwan lakar da ya kai kwankwasonmu, muka ci gaba da tafiya zuwa ƙauyen da za mu je ziyara.

Wannan ita ce ziyarar mu ta farko a wannan wurin, saboda haka, muka fara wa wasu mutane da ke aiki a gonakin shinkafa wa’azi kuma muka tambaye su inda ’yan’uwanmu suke zama a ƙauyen. Mun yi farin ciki sosai da muka fahimci cewa manoman shinkafar ’yan’uwanmu ne!

ƘARFAFA ’YAN’UWA SU SOMA HIDIMA TA CIKAKKEN LOKACI

A cikin waɗannan shekarun, mun yi farin ciki sosai sa’ad da muka ga waɗanda muka ƙarfafa suka shiga hidima ta cikakken lokaci. Sa’ad da muka ziyarci wata ikilisiya da ke da majagaba na kullum guda tara, muka ƙarfafa kowanne a cikinsu ya kafa maƙasudin taimaka wa mai shela ɗaya ya soma hidimar majagaba. Sa’ad da muka sake ziyarar su bayan watanni shida, majagaban sun ƙaru zuwa 22. Wasu majagaba mata guda biyu sun ƙarfafa mahaifinsu waɗanda dattawa ne su zama majagaba na kullum. Waɗannan ’yan’uwan suka ƙarfafa wani dattijo ya zama majagaba. Daga baya, aka naɗa dattijo na ukun ya zama majagaba na musamman. Sai shi da matarsa suka soma hidimar kula da da’ira. Sauran dattawa guda biyun fa? Yanzu ɗaya yana hidima a matsayin mai kula da da’ira, ɗayan kuma mai aikin gine-ginen Majami’an Mulki.

Muna wa Jehobah godiya kowace rana don taimakonsa. Mun san cewa ba za mu iya cim ma waɗannan abubuwan ba tare da taimakonsa ba. Hakika, wani lokaci muna gajiya kuma muna rashin lafiya, amma idan muka tuna da yadda hidimarmu ta yi albarka hakan yana sa mu farin ciki. Jehobah ne yake sa aikinsa ya yi nasara. Muna farin ciki cewa mun ɗan saka hannu a wannan aikin, yanzu muna hidima a matsayin majagaba na musamman. Babu shakka, mun koyi dogara ga Jehobah, wanda “yake ƙarfafa” mu.

[Bayanin da ke shafi na 6]

Mun koyi mu dogara ga Jehobah

[Taswira/Hoto a shafi na 4]

Ƙasar Madagascar, wadda da ake kira Big Red Island, ita ce tsibiri na huɗu mafi girma a duniya. Ƙasar marmara ce kuma tana cike da halittu masu ban al’ajabi

[’Hoto a shafi na 5]

Sufuri ne wani babbar matsala da muka fuskanta

[Hotona a shafi na 5]

Mun ji daɗin yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba