Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 4/15 pp. 22-26
  • Jehobah Ya San Yadda Zai Ceci Mutanensa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Ya San Yadda Zai Ceci Mutanensa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • YA TSIRA DAGA RIGYAWA
  • AN CECE SU A JAR TEKU
  • SUN TSIRA DAGA HALAKAR URUSHALIMA
  • AN ƘARFAFA MU DON NAN GABA
  • Jirgin Nuhu
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Labarin Nuhu da Ambaliya, Tatsuniya Ce?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Ya Yi “Tafiya Tare da Allah”
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Tambayoyi Daga Masu Karatu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 4/15 pp. 22-26

Jehobah Ya San Yadda Zai Ceci Mutanensa

“Ubangiji ya san yadda za ya ceci masu-ibada daga cikin jaraba.”—2 BIT. 2:9.

ME YA SA ZA MU KASANCE DA GABA GAƊI CEWA JEHOBAH:

Ya san daidai yadda abubuwa za su faru don su cika nufinsa?

Zai yi amfani da ikonsa don ya ceci bayinsa?

Ya san yadda abubuwa za su kasance a lokacin ƙunci mai-girma?

1. Mene ne zai faru a duniya a lokacin “ƙunci mai-girma”?

ALLAH zai halaka duniyar Shaiɗan farat ɗaya, sa’ad da mutane ba su yi zato ba. (1 Tas. 5:2, 3) A “ranar Ubangiji,” duniya da mutanen da ke cikinta za su rikice. (Zaf. 1:14-17) Za a sha wahala sosai kuma zai zama lokacin baƙin ciki “irin da ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har yanzu.”—Karanta Matta 24:21, 22.

2, 3. (a) Mene ne mutanen Allah za su fuskanta a lokacin “ƙunci mai-girma”? (b) Mene ne zai ƙarfafa mu don mu jimre abin da zai faru a nan gaba?

2 Yayin da “ƙunci mai-girma” ya kusan kammalawa, “Gog, na ƙasar Magog” zai kai wa mutanen Allah hari. A lokacin, “babbar rundunar yaƙi ƙwarai” za su kai wa mutanen Allah hari “kamar hadari garin a rufe ƙasan.” (Ezek. 38:2, 14-16) Babu ƙungiyar ɗan Adam da za ta taimaki mutanen Jehobah. Amma mutanen Allah za su bukaci su dogara ga Jehobah don su samu ceto. Mene ne za su yi sa’ad da abokan gabansu suka zo su halaka su?

3 Idan kana bauta wa Jehobah, shin kana da bangaskiya cewa Jehobah zai iya ceton mutanensa kuma zai yi hakan a lokacin ƙunci mai girma? Manzo Bitrus ya rubuta: “Ubangiji ya san yadda zai ceci masu-ibada daga cikin jaraba, ya tsare marasa-adalci kuma ƙarƙashin hukunci har zuwa ranar shari’a.” (2 Bit. 2:9) Yin bimbini a kan yadda Jehobah ya ceci mutanensa a dā zai ƙarfafa mu don mu jimre abin da zai faru nan gaba. Bari mu tattauna misalai uku da za su sa mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai iya ceton mutanensa.

YA TSIRA DAGA RIGYAWA

4. Mene ne ake bukatar a yi kafin Rigyawar?

4 Ka yi la’akari da labarin Rigyawa na zamanin Nuhu. Ana bukatar a yi wasu abubuwa kafin Rigyawar. Za a gina babban jirgi kuma a shigar da dabbobin cikin jirgin. Littafin Farawa bai faɗa ba cewa Jehobah ya jira har aka gama gina jirgin kafin ya faɗi lokacin da za a yi Rigyawar. Don ba ya bukatar ya damu ko za a gama gina jirgin a lokacin da ya kamata. Allah ya zaɓi lokacin da daɗewa kafin ya gaya wa Nuhu ya gina jirgin. Ta yaya muka san hakan?

5. Mene ne Jehobah ya sanar a littafin Farawa 6:3, kuma a wacce shekara ce ya yi wannan sanarwar?

5 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Jehobah ya tsai da shawara kuma ya sanar da hakan a cikin sama. A Farawa 6:3, ya ce: “Ruhuna ba zai riƙa jayayya da mutum har abada ba, gama shi kuma nama ne: amma kwanakin ransa shekara ɗari da ashirin za su zama.” Sa’ad da Jehobah ya furta waɗannan kalmomin, ba ya nufin tsawon shekarar ’yan Adam. Amma yana sanar da lokacin da zai hukunta miyagun mutane a duniya.a Rigyawar ta soma a shekara ta 2370 K.Z. Babu shakka, Allah ya yi wannan sanarwar a shekara ta 2490 K.Z. Nuhu ɗan shekara 480 ne a lokacin. (Far. 7:6) Sa’ad da Nuhu yake ɗan shekara 500, wato, a shekara ta 2470 K.Z., Nuhu ya soma haifan ’ya’yansa. (Far. 5:32) A wannan lokacin, shekara ɗari ne ya rage kafin a soma rigyawar. Amma Jehobah bai bayyana wa Nuhu aiki na musamman da zai yi ba, wato na ceton ’yan Adam. Shekara nawa ne Jehobah zai jira kafin ya faɗa wa Nuhu?

6. A wane lokaci ne Jehobah ya sanar wa Nuhu cewa ya gina jirgin?

6 Wataƙila Jehobah ya jira shekaru da yawa bayan Nuhu ya haifi ’ya’yansa kafin ya sanar masa da abin da yake son ya yi. Me ya sa muka ce hakan? Littafi Mai Tsarki ya ce yaran Nuhu sun riga sun yi girma kuma sun yi aure kafin Allah ya ce Nuhu ya gina jirgin. Jehobah ya gaya masa: “Amma zan tsai da alkawarina da kai; za ka shiga cikin jirgi kuma, da kai, da ’ya’yanka, da matarka, da matayen ’ya’yanka tare da kai.” (Far. 6:9-18) Zai yiwu a ce Allah ya sanar da Nuhu ya gina jirgin shekara 40 ko 50 kafin a yi Rigyawar.

7. (a) Ta yaya Nuhu da iyalinsa suka nuna bangaskiya? (b) A wane lokaci ne Allah ya gaya wa Nuhu ainihin lokacin da rigyawar za ta soma?

7 Sa’ad da Nuhu da iyalinsa suke gina jirgin, babu shakka sun yi tunani a kan yadda Allah zai kawo rigyawar da kuma lokacin da zai yi hakan. Amma ko da yake ba su san waɗannan abubuwan ba, sun kasance da bangaskiya kuma sun ci gaba da gina jirgin. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Nuhu ya yi; bisa ga abin da Allah ya umurce shi duka, haka ya yi.” (Far. 6:22) Jehobah ya gaya wa Nuhu cewa za a soma rigyawar bayan kwana bakwai. Hakan ya ba Nuhu da iyalinsa isashen lokaci don su shigar da dabobbi cikin jirgin. Saboda haka, sa’ad da aka soma rigyawar “a shekara ta ɗari shidda ta zamanin Nuhu, cikin wata na biyu, kan rana ta goma sha bakwai ga wata,” Nuhu ya riga ya kammala kome.—Far. 7:1-5, 11.

8. Ta yaya labarin Rigyawar ya sa mu kasance da tabbaci cewa Jehobah ya san sa’ad da zai ceci mutanensa?

8 Labarin Rigyawa ta zamanin Nuhu ya nuna cewa Jehobah ya san daidai lokacin da kuma hanya mafi kyau da zai ceci mutanensa. Yayin da muke daɗa yin kusa da ƙarshen wannan zamanin, za mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai cika dukan ƙudurinsa a daidai ‘ranan da sa’an’ da ya ƙayyade don hakan.—Mat. 24:36; karanta Habakkuk 2:3.

AN CECE SU A JAR TEKU

9, 10. Ta yaya Jehobah ya yi amfani da mutanensa don ya ɗana wa Masarawa tarko?

9 Labarin Rigyawar ya koya mana cewa Jehobah yana sarrafa lokacin da abubuwa suke faruwa don ya cika nufinsa. Misali na biyu da za mu tattauna ya nuna dalilin da ya sa za mu iya dogara ga Jehobah don ya ceci mutanensa. Zai yi amfani da ikonsa marar iyaka don ya ceci mutanensa kuma ya tabbata cewa nufinsa ya cika. Abin da ya faru ke nan sa’ad da aka ceci Isra’ilawa daga ƙasar Masar.

10 Kusan Isra’ilawa miliyan uku ne suka fita daga ƙasar Masar. Jehobah ya sa suka biyo hanyar da Fir’auna zai yi tunani cewa ba su san hanya ba kuma sun rikice. (Karanta Fitowa 14:1-4.) Saboda haka, Fir’auna ya biyo su a guje kuma ya tarar da su a Jar Teku. Isra’ilawa ba su da hanyar fita. (Fit. 14:5-10) Amma, Isra’ilawa ba sa cikin haɗari. Me ya sa? Domin Jehobah yana a shirye ya cece su.

11, 12. (a) Ta yaya Jehobah ya yi faɗa don mutanensa? (b) Mene ne sakamakon wannan faɗan kuma mene ne wannan labarin ya koya mana game da Jehobah?

11 “Umudi na hadari” da ke wa Isra’ilawa ja-gora ya koma bayan Isra’ilawa kuma ya soma tare Fir’auna da rundunarsa kuma suka kasance cikin duhu. Umudin yana sa Masarawa su kasance cikin duhu, amma yana sa Isra’ilawa su kasance cikin haske. (Karanta Fitowa 14:19, 20.) Jehobah ya yi amfani da iskan gabas mai ƙarfi don ya busar da tekun. Babu shakka, wannan ya ɗan ɗauki lokaci. Da yake Isra’ilawa suna tafiya a ƙasa, ba su yi sauri sosai ba. Amma Rundunar Masarawa suna yi gudu sosai domin suna yi amfani da karusa. Amma duk da haka, Masarawa ba su isa inda Isra’ilawa suke ba domin Jehobah ne yake kāre su. “Ya gigita dāgar Masarawa. Ya cire ƙafafun karusansu, sai da ƙyar su ke korassu domin nauyi.”—Fit. 14:21-25.

12 Sa’ad da Isra’ilawa suka gama ketare tekun, sai Jehobah ya gaya wa Musa: “Miƙe hannunka bisa teku, domin ruwaye su koma bisa Masarawa, bisa karusansu, da bisa mahayansu.” Sa’ad da Masarawa suka nemi su ja da baya don kada ruwan ya shanye su sai Jehobah “ya halakar da Masarawa a tsakiyar teku.” Babu wanda ya tsira. “Ba ya rage ko guda ɗaya a cikinsu ba.” (Fit. 14:26-28) Hakan ya nuna cewa yana da iko ya ceci mutanensa daga kowanne irin yanayi.

SUN TSIRA DAGA HALAKAR URUSHALIMA

13. Wane umurni ne Yesu ya bayar kuma wataƙila mabiyansa sun yi mamaki a kan me?

13 Misali na uku da za mu tattauna shi ne abin da ya faru a ƙarni na farko sa’ad da rundunar Romawa suka kai wa Urushalima hari. Wannan misalin ya nuna cewa Jehobah ya san daidai yadda abubuwa za su kasance don nufinsa ya cika. Jehobah ya yi amfani da Yesu don ya ba Kiristocin da ke Urushalima da kuma ƙasar Yahuda umurni kafin a halaka biranen a shekara ta 70 A.Z. Yesu ya ce: “Sa’anda fa kun ga ƙyamar lalata, wadda aka ambace ta ta bakin annabi Daniyel, tana tsaye a cikin tsatsarkan wuri . . . , sa’annan waɗanda ke cikin Yahudiya su gudu zuwa duwatsu.” (Mat. 24:15, 16) Amma ta yaya mabiyan Yesu za su san cewa wannan annabcin ya soma cika?

14. Wace aukuwa ce ya sa mabiyan Yesu suka fahimci ma’anar umurninsa?

14 Mabiyan Yesu sun soma fahimtar kalaman Yesu sosai shekaru da yawa bayan ya furta su. A shekara ta 66 A.Z., rundunar ƙasar Roma a ƙarƙashin ja-gorar Cestius Gallus sun zo Urushalima don su sa Yahudawa su daina tawayen da suke yi. Sa’ad da Yahudawa da suke tawaye suka ɓoye a cikin haikalin, sai rundunar ƙasar Roma suka soma halaka ganuwar haikalin. Waɗannan Kiristocin da suka tuna da maganar Yesu sun san abin da ke faruwa. Sun fahimci cewa Romawa masu bautar gumaka da suka shiga cikin haikalin Urushalima “ƙyamar lalata” ce da ke “tsaye a cikin [ganuwar] tsatsarkan wuri.” Lokaci ya yi da mabiyan Yesu za su soma “gudu zuwa duwatsu.” Amma yaya za su iya fita daga cikin birnin da an riga an kange? Abu mai ban al’ajabi yana gab da faruwa.

15, 16. (a) Wane kashedi ne Yesu ya ba da kai tsaye kuma me ya sa yake da muhimmanci mabiyansa su yi biyayya ga kashedin? (b) Mene ne muke bukata mu yi don mu samu ceto?

15 Babu gaira ba dalili, Cestius Gallus da rundunarsa suka fita daga Urushalima kuma suka koma gidajensu. Sai ’yan tawayen suka bi su a guje. Da yake Romawa da kuma Yahudawa masu tawaye sun fita daga cikin birnin, sai mabiyan Yesu suka samu damar guduwa. Yesu ya riga ya gaya musu cewa su fita daga cikin birnin nan da nan ba tare da kwashe kayansu ba. (Karanta Matta 24:17, 18.) Suna bukatar su ɗauki mataki ba tare da ɓata lokaci ba. Domin bayan ’yan kwanaki kaɗan, ’yan tawayen suka dawo kuma suka soma tilasta wa mutanen Urushalima da Yahuda cewa su shiga rukuninsu. Faɗa ta ɓarke tsakanin ’yan tawayen da kuma ’yan birnin. Kuma fita daga birnin ya daɗa wuya sosai. Amma sa’ad da Romawa suka dawo a shekara ta 70 A.Z., babu wanda ya samu wurin fita kuma daga birnin. (Luk 19:43) Duk wanda bai fita daga birnin ba ya shiga cikin tarko. Amma Kiristocin da suka yi biyayya ga umurnin Yesu kuma suka fita daga birnin sun samu ceto. Sun shaida cewa Jehobah ya san yadda zai ceci mutanensa. Wane darassi ne za mu iya koya daga wannan labarin?

16 A lokacin ƙunci mai-girma, Kiristoci za su bukaci yin biyayya ga Kalmar Allah da kuma ƙungiyarsa. Alal misali, umurnin da Yesu ya ba mabiyansa cewa su “gudu zuwa duwatsu” ya shafe mu a yau domin za a ce mu ma mu yi hakan a lokacin ƙunci mai-girma. Ba mu san ainihin yadda za mu yi gudun ba.b Amma za mu iya kasance da tabbaci cewa Jehobah zai bayyana mana ma’anar wannan umurnin idan lokacin ya yi. Za a cece mu idan muka yi koyi da umurnin da aka ba mu a lokacin. Saboda haka ya kamata mu tambayi kanmu: ‘Shin ina yin biyayya ga umurnin da Jehobah yake ba mutanensa yanzu? Shin ina yin biyayya nan da nan ko kuwa ina yin jinkiri?’—Yaƙ. 3:17.

AN ƘARFAFA MU DON NAN GABA

17. Mene ne muka koya daga annabcin Habakkuk na farmakin da Gog zai kai wa bayin Allah?

17 Yanzu bari mu tattauna game da farmakin Gog da muka ambata a farkon wannan talifin. Kamar Ezekiel, Habakkuk ya yi magana game da wannan lokacin. Ya ce: “Na ji, cikina kuma ya yi rawa, leɓunana suka yi makerketa da jin muryan; ruɓewa ta shigo cikin ƙasussuwana, na yi rawa a matsayina; in huta, ina jiran ranar wahala; sa’anda ta afko ma mutanen da ke kawo masa yaƙi da runduna.” (Hab. 3:16) Habakkuk ya ji tsoro sosai sa’ad da ya ji cewa maƙiya za su kawo wa mutanen Allah farmaki. Yadda Habakkuk ya aikata ya nuna yadda za mu ji sa’ad da Gog da mabiyansa suka kawo mana farmaki. Wataƙila za mu ji tsoro. Za mu iya kasancewa kamar Habakkuk kuma mu dogara cewa Jehobah zai ceci mutanensa.—Hab. 3:18, 19.

18. (a) Me ya sa bai kamata mu ji tsoro sa’ad da maƙiyanmu suka kawo mana farmaki ba? (b) Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

18 Misalai uku da muka tattauna sun nuna sarai cewa Jehobah ya san yadda zai ceci bayinsa. Nufinsa zai cika kuma zai halaka maƙiyansa. Idan muna son mu rera yabo ga Jehobah sa’ad da hakan ya faru, wajibi ne mu kasance da aminci har ƙarshe. Ta yaya Jehobah yake taimaka mana mu kasance da aminci a yau? Abin da za mu tattauna a talifi na gaba ke nan.

[Hasiya]

a Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Disamba, 2010, shafuffuka na 30-31.

b Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Mayu, 1999, shafi na 25.

[Hoto a shafi na 24]

Shin Isra’ilawa sun kasance cikin haɗari don rundunar Fir’auna?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba