Cin Amana Hali Ne Da Ke Nuna Muna Kwanaki Na Ƙarshe!
“Hali mai-tsarki, mai-adalci, marar-abin zargi da muka nuna maku.”—1 TAS. 2:10.
KA FAƊI MUHIMMAN DARUSSAN DA KA KOYA:
․․․․․
Waɗanne darussa ne muka koya daga yadda Delilah da Absalom da kuma Yahuda Iskariyoti suka ci amanar wasu?
․․․․․
Ta yaya za mu yi koyi da yadda Jonathan da Bitrus suka kasance da aminci?
․․․․․
Ta yaya za mu iya kasancewa da aminci ga matarmu ko mijinmu da kuma Jehobah?
1-3. (a) Wane abu da ke faruwa a yau ne ya nuna cewa muna rayuwa a kwanaki na ƙarshe, kuma mene ne hakan yake nufi? (b) Waɗanne tambayoyi uku ne za mu amsa?
DELILAH da Absalom da Yahuda Iskariyoti suna da wane nasaba? Dukansu sun ci amanar wani. Delilah ta ci amanar masoyinta, Alƙali Samson. Absalom ya ci amanar mahaifinsa, Sarki Dauda. Yahuda ya ci amanar Ubangijinsa, Yesu Kristi. Waɗannan cin amanar sun jawo babbar matsala ga waɗanda ya shafa. Amma, me ya sa wannan ya shafe mu sosai?
2 Wani marubuci ya ce cin amana yana cikin abubuwan da suke shafar mutane sosai a yau. Bai kamata hakan ya ba mu mamaki ba. Sa’ad da Yesu yake ba da annabcin abubuwan da za su faru a kwanaki na ƙarshe, ya ce: “Da yawa za su . . . ci amanar juna.” (Mat. 24:3, 10; Littafi Mai Tsarki) ‘Cin amana’ yana nufin yin ƙulle-ƙulle don maƙiyin wani ya kama shi, wato rashin aminci. Rashin amincin da ya zama ruwan dare yana nuna cewa muna rayuwa a “kwanaki na ƙarshe.” Manzo Bulus ya annabta cewa mutane za su zaman “marasa aminci, . . . masu cin-amana.” (2 Tim. 3:1, 2, 4, NW) ’Yan fim da marubuta sukan mai da cin amana abin da mutum zai iya yi don ya burge mutane ko kuma don soyayya. Amma waɗannan littattafai da fina-finai ba sa faɗan gaskiya, domin a gaske wannan halin yana jawo baƙin ciki. Waɗannan ayyukan alamu ne cewa muna kwanaki na ƙarshe.
3 Waɗanne darussa ne za mu iya koya daga Littafi Mai Tsarki game da mutanen da suka kasance da rashin aminci a zamanin dā? Me za mu koya daga mutanen da suka kasance da aminci? Kuma ga waye ne ya kamata mu kasance da aminci? Bari mu tattauna amsoshin.
KASHEDI DAGA ABUBUWAN DA SUKA FARU A DĀ
4. Ta yaya Delilah ta ci amanar Samson kuma me ya sa hakan mugunta ne?
4 Misali na farko da za mu tattauna shi ne na Delilah, mai yaudara wadda ita da Alƙali Samson suke soyayya. Samson yana son ya ja-goranci yaƙin da mutanen Allah suke son su yi da Filistiyawa. Wataƙila sarakuna biyar na Filistiyawa sun san cewa Delilah ba ta ƙaunar Samson da gaske. Sun ba ta kuɗi da yawa don ta bincika abin da ya sa Samson yake da ƙarfi domin su kashe shi. Sai ta ci gaba da matsa masa “da maganganunta, ta kuwa tsananta masa.” A ƙarshe, “ransa ya ɓaci har bakin mutuwa.” Ya ce mata ba a taɓa yanke gashi kansa ba kuma idan an yanke gashinsa, zai rasa ƙarfinsa.a Da yake ta san sirrinsa yanzu, Delilah ta sa aka yanke gashin Samson sa’ad da yake barci a kan cinyarta. Sai ta miƙa shi ga maƙiyansa don su wulakanta shi. (Alƙa. 16:4, 5, 15-21) Abin da ta yi mugunta ne sosai! Delilah ta ci amanar masoyinta saboda kwaɗayi.
5. (a) Ta yaya Absalom ya ci amanar Dauda kuma mene ne hakan ya nuna game da Absalom? (b) Yaya Dauda ya ji game da yadda Ahitofel ya ci amanarsa?
5 Wani maci amana na biyu shi ne Absalom. Yana son iko da kuma matsayi sosai kuma yana son ya yi wa mahaifinsa, Sarki Dauda juyin mulki. Abu na farko da Absalom ya yi shi ne “ya sace zukatan mazaje na Isra’ila.” Ya yi kamar yana son mutanen kuma ya yi musu alkawarin ƙarya. Yakan rungume su kuma ya yi musu sumba, yana yi kamar yana ƙaunarsu da gaske. (2 Sam. 15:2-6) Absalom ya kuma sa aminin Dauda mai suna Ahitofel ya ci amanar Dauda kuma ya yi tawaye da shi. (2 Sam. 15:31) A littafin Zabura ta 3 da 55, Dauda ya bayyana yadda wannan cin amanar ta ɓata masa rai sosai. (Zab. 3:1-8; karanta Zabura 55:12-14.) Wannan ƙulle-ƙulle da Absalom ya yi ga sarkin da Allah ya naɗa bai dace ba. Wannan cin amanar ta nuna cewa ya ƙi da ikon Allah na zaɓar wanda ya dace ya zama sarki. (1 Laba. 28:5) Absalom bai yi nasara ba, kuma Dauda ya ci gaba da yin sarauta a matsayin sarkin da Jehobah ya naɗa.
6. Ta yaya Yahuda ya ci amanar Yesu kuma yaya ake yin amfani da sunansa a yau?
6 Yanzu bari mu yi magana game da yadda Yahuda Iskariyoti ya ci amanar Yesu. A Idin Ƙetarewa na ƙarshe da Yesu ya yi da almajiransa 12, ya gaya musu: “Hakika, ina ce maku, ɗaya daga cikinku za ya bashe ni.” (Mat. 26:21) Daga baya a daren nan, Yesu ya gaya wa Bitrus da Yaƙub da Yohanna a lambun Jathsaimani cewa: “Ga shi, wanda ya bashe ni yana kusa.” Sai Yahuda ya zo lambun tare da mutanen, “ya zo wurin Yesu, ya ce, A gaishe ka, Rabbi; ya yi ta yi masa sumba.” (Mat. 26:46-50; Luk 22:47, 52) Yahuda ya ci amanar “jini marar-aibi” kuma ya miƙa Yesu ga maƙiyansa. Amma me ya sa Yahuda ya yi hakan? Domin za a ba shi azurfa talatin. (Mat. 27:3-5) Tun daga lokacin, mutane suna yin amfani da sunan nan Yahuda sa’ad da suke kwatanta mutum maci-amana, musamman wanda ya ci amanar abokinsa.
7. Wane darassi ne za mu iya koya daga abin da ya faru da (a) Absalom da Yahuda da kuma (b) Delilah?
7 Mene ne muka koya daga waɗannan misalan? Absalom da Yahuda sun mutu a hanya marar kyau domin sun ci amanar mutanen da Jehobah ya naɗa. (2 Sam. 18:9, 14-17; A. M. 1:18-20) Duk sa’ad da mutane suka ji sunan nan Delilah, suna tunawa da yadda ta ci amanar masoyinta. (Zab. 119:158) Ya kamata mu mai da hankali don kada mu riƙa son matsayi domin hakan zai iya ɓata dangantakarmu da Jehobah! Waɗannan darussa masu kyau ne da za su taimaka mana mu ƙi wannan hali na rashin aminci.
KA YI KOYI DA MASU AMINCI
8, 9. (a) Me ya sa Jonathan ya ce zai kasance da aminci ga Dauda? (b) Ta yaya za mu iya yin koyi da Jonathan?
8 Littafi Mai Tsarki ya ba da misalin mutane da yawa da suka kasance da aminci. Za mu tattauna abin da za mu iya koya daga biyu cikinsu. Za mu soma da wani da ya kasance da aminci ga Dauda. Ya kamata Jonathan, ɗan fari na Sarki Saul ya zama sarki bisa ƙasar Isra’ila. Amma maimakon Jonathan, Jehobah ya zaɓi Dauda. Jonathan ya amince da zaɓin da Jehobah ya yi kuma bai yi ƙishinsa ba. Jonathan “ya ƙaunace [Dauda] kamar ransa,” kuma ya yi masa alkawari cewa zai kasance da aminci a gare shi. Ya nuna cewa ya amince da Dauda ta wajen ba shi kyautar tufafinsa da takobinsa da bakansa da ɗamararsa. (1 Sam. 18:1-4) Jonathan ya yi iya ƙoƙarinsa don ya ƙarfafa Dauda. Ya ma saka kansa cikin haɗari don ya kāre Dauda daga harin da Saul yake son ya kai masa. Cikin aminci, Jonathan ya gaya wa Dauda: “Za ka zama sarki kuma bisa Isra’ila, ni kuma zan zama na biyunka.” (1 Sam. 20:30-34; 23:16, 17) Shi ya sa Dauda ya rera waƙa bayan rasuwar Jonathan don nuna baƙin cikinsa da kuma ƙaunar da yake masa.—2 Sam. 1:17, 26.
9 Jonathan ya san wanda ya kamata ya nuna wa aminci. Ya kasance da cikakken aminci ga Mai-ikon Mallaka, Jehobah, kuma ya goyi bayan sarkin da Allah ya naɗa. Hakazalika a yau, ko da ba a ba mu gata na masamman a cikin ikilisiya ba, ya kamata mu goyi bayan ɗan’uwan da Jehobah ya naɗa don ya yi ja-gora a cikin ikilisiya.—1 Tas. 5:12, 13; Ibran. 13:17, 24.
10, 11. (a) Me ya sa Bitrus ya kasance da aminci ga Yesu? (b) Ta yaya za mu iya yin koyi da Bitrus kuma mene ne hakan ya kamata ya motsa mu mu yi?
10 Misali mai kyau na biyu da za mu tattauna shi ne na manzo Bitrus, wanda ya ce zai kasance da aminci ga Yesu. Yesu ya bayyana wa almajiransa yadda yin imani ga jikinsa da jininsa suke da muhimmanci. Kuma zai miƙa su don hadaya a madadin ’yan Adam. Wannan kwatanci ne kawai, amma almajiransa sun yi zato cewa zahiri ne. Domin hakan, suka bar shi. (Yoh. 6:53-60, 66) Bayan haka, sai Yesu ya tambayi almajiransa sha biyu: “Ku kuma kuna so ku tafi?” Amma sai Bitrus ya amsa, “Ubangiji, wurin wa za mu tafi? kai ne da maganar rai na har abada. Mu kuwa mun rigaya mun bada gaskiya, kuma mun sani kai ne Mai-tsarki na Allah.” (Yoh. 6:67-69) Shin wannan amsar da Bitrus ya ba da ya nuna cewa ya fahimci dukan abin da Yesu ya ce? Da ƙyar. Amma duk da haka, Bitrus ya tsai da shawara cewa zai kasance da aminci ga shafaffen Ɗan Allah, Yesu Kristi.
11 Bitrus bai yi tunani ba cewa Yesu ya san cewa abin da ya faɗa ba daidai ba ne kuma zai yi gyara a nan gaba. Bitrus ya kasance da aminci kuma ya san cewa Yesu yana da “maganar rai na har abada.” Wannan ya shafe mu ma a yau. Yaya muke aikatawa sa’ad da muka karanta wani abu a cikin littattafanmu na Kirista wanda “bawan nan mai-aminci mai-hikima” ya wallafa da ke da wuyar fahimta ko kuma bai jitu da ra’ayinmu ba? Ya kamata mu yi ƙoƙari don mu fahimci ma’anar. Bai kamata mu sa rai cewa za a yi gyaran da zai jitu da ra’ayinmu ba.—Karanta Luka 12:42.
KA KASANCE DA AMINCI GA MATARKA KO MIJINKI
12, 13. Mene ne yake jawo cin amana tsakanin ma’aurata kuma me ya sa shekarar mutum ba hujja ba ce?
12 Cin amanar wani a ko wacce hanya mugunta ce. Bai kamata mu ƙyale cin amana ya shafi salama da haɗin kai na iyalin Kirista da kuma ikilisiya ba. Bari mu tattauna yadda za mu iya ƙarfafa amincinmu ga matarmu ko mijinmu da kuma Allahnmu.
13 Cin amana mafi sa baƙin ciki ita ce zina. Mutumin da ya yi zina kuma ya mai da hankali ga wata ya ci amanar matarsa. Kuma matar da aka ci amanarta za ta kaɗaita, kuma hakan zai canja rayuwarta gabaki ɗaya. Me ya sa hakan yake faruwa da mutane biyu da suke son juna a dā? Hakan yana somawa sa’ad da ma’aurata suka soma yin nisa da juna. Wani farfesan ilimin halayyar zaman jama’a, Gabriella Turnaturi ya bayyana cewa “cin amana za ta iya faruwa idan sun daina iya ƙoƙarinsu don su ƙarfafa dangantakarsu.” Kuma hakan zai iya faruwa da mutanen da suka daɗe da yin aure. Alal misali, wani mutum ɗan shekara 50 da ya yi aure na tsawon shekara 25 ya saki matarsa da ba ta yi masa laifi ba domin ya auri wata dabam. Wasu sun ce abin da ke faruwa da mutum ke nan sa’ad da ya kai wannan shekarar. Amma hakan ba hujja ba ce. Cin amanar aboki ko abokiyar aurenmu rashin aminci ne.b
14. (a) Yaya Jehobah yake ji game da waɗanda suke cin amanar abokiyar aurensu? (b) Mene ne Yesu ya ce game da cin amana?
14 Yaya Jehobah yake ji game da wanda ya saki matarsa ba tare da ta yi zina ba? Allah yana “ƙyamar kisan aure.” Ya tsauta wa waɗanda suke wulakanta matarsu kuma suka sake su. (Karanta Malakai 2:13-16.) Kamar Ubansa, Yesu yana ƙyamar cin amanar aboki ko abokiyar aure. Ya ce mutum ba zai iya ƙyale matarsa ba kuma ya yi kamar bai yi wani laifi ba.—Karanta Matta 19:3-6, 9.
15. Ta yaya waɗanda suka yi aure za su iya ƙarfafa amincinsu ga juna?
15 Ta yaya waɗanda suka yi aure za su kasance da aminci ga juna? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka yi murna da matar [ko mijin] kuruciyarka” kuma, “Ka zauna da farinciki tare da mace [ko miji] wadda ka ke ƙaunatta.” (Mis. 5:18; M. Wa. 9:9) Yayin da shekarun ma’auratan yake ƙaruwa, wajibi ne su yi iya ƙoƙarinsu don dangantakarsu ta yi ƙarfi a kowacce hanya. Mene ne yin hakan yake nufi? Ma’aurata suna bukata su kusaci juna ta wajen yi wa juna kirki suna kula da juna suna kuma kasancewa da juna sosai. Suna bukatar su sa ƙwazo sosai don su kāre aurensu da kuma dangantakarsu da Jehobah. Kuma ma’aurata za su iya cim ma hakan ta wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki tare da yin wa’azi tare da kuma yin addu’a tare don Jehobah ya albarkace su.
KA KASANCE DA AMINCI GA JEHOBAH
16, 17. (a) Ta yaya za a iya gwada amincinmu ga Jehobah a cikin iyali da kuma ikilisiya? (b) Wane misali ne ya nuna cewa yin biyayya da dokar Allah na kada a yi cuɗanya da duk wanda aka wa yankan zumunci yana kawo sakamako mai kyau?
16 Akwai wasu a cikin ikilisiya da suka yi zunubi mai tsanani kuma aka musu horo mai “zafi, domin su zama sahihai cikin imani.” (Tit. 1:13) An yi wa wasu cikinsu yankan zumunci saboda halinsu. Amma, “waɗanda sun wāsu ta wurinsa,” horon ya taimaka musu su soma bauta wa Jehobah kuma. (Ibran. 12:11) Mene ne za mu yi idan an yi wa danginmu ko abokinmu yankan zumunci? Yadda muka aikata a wannan lokacin zai nuna ko amincinmu ga mutumin ne ko kuma ga Allah. Jehobah yana kallonmu don ya ga ko za mu yi biyayya ga dokarsa na kada mu yi cuɗanya da duk wanda aka wa yankan zumunci.—Karanta 1 Korintiyawa 5:11-13.
17 Ka yi la’akari da wannan misalin da ya nuna amfanin da ake samu idan waɗanda suke cikin iyali sun ƙi yin cuɗanya da danginsu da aka wa yankan zumunci. An yi wa wani matashi yankan zumunci fiye da shekara goma. Kuma a waɗannan shekarun, mahaifinsa da mahaifiyarsa da kuma ’yan’uwansa maza huɗu sun daina “tarayya” da shi. A wasu lokaci zai so ya kasance tare da su, amma sun kasance da aminci. Ba su yi cuɗanya da shi ba. Bayan da aka sake dawo da shi, ya ce ya yi kewar iyalinsa sosai musamman daddare sa’ad da ya kaɗaita. Ya ce da iyalinsa sun yi cuɗanya da shi ko da na ɗan lokaci ne da hakan ya gamshe shi. Amma, ba su yi cuɗanya da shi ba. Kuma wannan ne abu ɗaya da ya sa ya daidaita dangantakarsa da Jehobah. Ya kamata ka tuna da wannan misalin duk sa’ad da ka fuskanci matsin karya dokar da Allah ya ba mu cewa kada mu yi cuɗanya da danginmu da aka wa yankan zumunci.
18. Bayan mun tattauna misalan masu aminci da kuma waɗanda suka cin amana, mene ne ƙudurinka?
18 Muna rayuwa ne a cikin duniya mai cike da mutane marasa-aminci da masu cin amana. Amma a cikin ikilisiyar Kirista, akwai mutane masu aminci da za mu iya yin koyi da su. Yadda suke rayuwa ya nuna cewa suna da “hali mai-tsarki, mai-adalci, marar-abin zargi.” (1 Tas. 2:10) Bari kowannenmu ya yi iya ƙoƙarinsa don ya kasance da aminci ga Allah da kuma mutane.
[Hasiya]
a Dangantakar Samson da Jehobah a matsayinsa na Banazare ne ya sa yake da ƙarfi, ba gashinsa ba. Gashinsa alama ce ta wannan dangantakar.
b Don ƙarin bayani game da aboki ko abokiyar aure da ya kasance da rashin aminci, ka duba talifin nan “Jimrewa da Cin Amana na Abokin Aure” a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuni, 2010, shafuffuka na 29-32.
[Hoto a shafi na 10]
Ko da wasu mutane sun yashe Yesu, amma Bitrus ya kasance da aminci ga shafaffen Ɗan Allah