Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w16 Fabrairu pp. 14-19
  • Ka Kasance da Aminci ga Jehobah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Kasance da Aminci ga Jehobah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • SA’AD DA MUKE GANI CEWA WANI MAI IKO BAI CANCANCI BIYAYYARMU BA
  • SA’AD DA MUKE TSAI DA SHAWARA A KAN WANDA ZA MU KASANCE DA AMINCI A GARE SHI
  • SA’AD DA WANI ƊAN’UWA YA YI MANA MUMMUNAR FAHIMTA KO KUMA YA YI MANA RASHIN ADALCI
  • SA’AD DA CIKA ALKAWARINMU YAKE DA WUYA
  • Sun Kulla Abota ta Kwarai
    Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu
  • Jonathan Mai Karfin Hali da Aminci
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Jonathan​—“Babu Abin da Zai Iya Hana” Jehobah
    Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu
  • Ka Koyi Darasi Daga Amintattun Bayin Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
w16 Fabrairu pp. 14-19
Jonathan yana magana da Dauda

Ka Kasance da Aminci ga Jehobah

“Ubangiji ya zauna tsakanina da kai, tsakanin zuriyata da zuriyarka, har abada.”—1 SAMA’ILA 20:42.

WAƘOƘI: 125, 62

MECE CE AMSARKA?

  • Ta yaya Jonathan, ɗan Sarki Saul ya kasance da aminci ga Jehobah?

  • Ta yaya za mu kasance da aminci ga Allah sa’ad da muke gani cewa wani mai iko bai cancanci biyayyarmu ba?

  • Ta yaya za mu iya kasancewa da aminci ga Jehobah sa’ad da wasu suka yi mana mummunar fahimta ko kuma rashin adalci?

1, 2. Me ya sa abotar Jonathan da Dauda misali ne mai kyau na aminci?

BABU shakka, yadda Dauda ya kasance da ƙarfin zuciya ya burge Jonathan sosai. Dauda ya kashe wani ƙaton mutum mai suna Goliath kuma ya kawo wannan “kan Bafilistin” ɗin ga mahaifin Jonathan, wato Sarki Saul na Isra’ila. (1 Sama’ila 17:57) Jonathan ya san cewa Allah yana tare da Dauda. Tun daga lokacin, Jonathan da Dauda suka zama abokai na kud da kud. Sun yi alkawari cewa za su kasance da aminci ga juna. (1 Sama’ila 18:​1-3) Jonathan ya kasance da aminci ga Dauda a dukan rayuwarsa.

2 Ko da yake, Jonathan ya san cewa Jehobah ya zaɓa Dauda ya zama sarkin Isra’ila a nan gaba, ya ci gaba da kasancewa da aminci ga Dauda. Sa’ad da Saul yake ƙoƙarin ya kashe Dauda, Jonathan ya damu game da abokinsa. Da yake Jonathan ya san cewa Dauda yana wani daji da ke garin Horesh sai ya je wurin don ya ƙarfafa Dauda ya dogara ga Jehobah. Saboda haka, Jonathan ya je wurin don. Jonathan ya gaya wa Dauda: “Kada ka ji tsoro: gama hannun Saul ubana ba za ya same ka ba: za ka zama sarki kuma bisa Isra’ila, ni kuma zan zama na biyunka.”​—⁠1 Sama’ila 23:​16, 17.

3. Mene ne ya fi muhimmanci ga Jonathan, kuma ta yaya muka san da hakan? (Ka duba hoton da ke shafi na 14.)

3 Muna son mutane masu aminci. Amma, shin muna son Jonathan domin ya kasance da aminci ga Dauda ne? A’a, kasancewa da aminci ga Allah ya fi muhimmanci ga Jonathan. Hakika, shi ya sa ya kasance da aminci ga Dauda kuma bai yi kishin Dauda ba ko da yake zai zama sarki a maimakonsa. Jonathan ya taimaka wa Dauda ya dogara ga Jehobah. Dukansu sun kasance da aminci ga Jehobah da kuma junansu. Sun cika alkawarin da suka yi cewa: “Ubangiji ya zauna tsakanina da kai, tsakanin zuriyata da zuriyarka, har abada.”​—⁠1 Sama’ila 20:⁠42.

4. (a) Mene ne zai sa mu yi farin ciki sosai kuma mu sami gamsuwa? (b) Mene ne za a tattauna a wannan talifin?

4 Wajibi ne mu kasance da aminci ga iyalinmu da abokanmu da ‘yan’uwanmu da ke cikin ikilisiya. (1 Tasalonikawa 2:​10, 11) Amma, abin da ya fi muhimmanci shi ne mu kasance da aminci ga Jehobah domin shi ya ba mu rai! (Ru’ya ta Yohanna 4:11) Za mu yi farin ciki sosai kuma mu sami gamsuwa idan muka kasance da aminci ga Jehobah. Ƙari ga haka, mun san cewa wajibi ne mu kasance da aminci ga Allah ko da yin hakan yana da wuya. A wannan talifin, za mu tattauna yadda misalin Jonathan zai taimaka mana mu kasance da aminci ga Jehobah a ɓangarori huɗu: (1) sa’ad da muke gani wani mai iko bai cancanci mu yi masa biyayya ba, (2) sa’ad da muke tsai da shawara a kan wanda za mu kasance da aminci a gare shi, (3) sa’ad da wani ɗan’uwa mai iko ya yi mana mummunar fahimta mu ko kuma ya yi mana rashin adalci, (4) sa’ad da cika alkawarinmu yake da wuya.

SA’AD DA MUKE GANI CEWA WANI MAI IKO BAI CANCANCI BIYAYYARMU BA

5. Me ya sa yake da wuya mutanen Isra’ila su kasance da aminci ga Allah sa’ad da Saul yake sarauta?

5 Jonathan da mutanen Isra’ila suna cikin wani yanayi mai wuya. Mahaifin Jonathan, wato Sarki Saul ya yi rashin biyayya kuma Jehobah ya ƙi shi. (1 Sama’ila 15:​17-23) Duk da haka, Allah ya ƙyale Saul ya ci gaba da sarauta shekaru da yawa. Shi ya sa ya yi wa mutanen wuya su kasance da aminci ga Allah, da yake sarkin da aka zaɓa ya zauna a kan “kursiyin Ubangiji” yana aikata mugunta.​—⁠1 Labarbaru 29:⁠23.

6. Mene ne ya nuna cewa Jonathan ya kasance da aminci ga Jehobah?

6 Jonathan ya kasance da aminci ga Jehobah. Alal misali, ka yi la’akari da abin da Jonathan ya yi da ya nuna yana da aminci ba da daɗewa ba bayan Saul ya soma yin rashin biyayya ga Allah. (1 Sama’ila 13:​13, 14) A wannan lokacin, sojoji masu yawa na Filistiyawa suka zo da karusai 30,000 don su kai wa Isra’ilawa hari. Saul yana da sojoji 600 kawai, kuma shi da Jonathan ne kaɗai suke da makamai. Amma Jonathan bai ji tsoro ba. Ya tuna da kalmomin annabi Sama’ila cewa: “Ubangiji ba za ya [yashe] jama’arsa ba sabili da sunansa mai-girma.” (1 Sama’ila 12:22) Jonathan ya gaya wa wani soja: “Ba abin da za ya hana Ubangiji shi yi . . . ceto ta hannun masu-yawa ko ta hannun kaɗan.” Saboda haka, shi da sojan suka kai wa wani rukuni Filistiyawa hari kuma suka kashe mutane 20 a cikinsu. Jonathan yana da bangaskiya kuma Jehobah ya albarkace shi. Jehobah ya sa aka yi girgizan ƙasa kuma Filistiyawa suka tsorata. Sai suka kai wa junansu hari kuma suka kashe juna, wannan ya sa Isra’ilawa suka ci yaƙin.​—⁠1 Sama’ila 13:​5, 15, 22; 14:​1, 2, 6, 14, 15, 20.

7. Ta yaya Jonathan ya bi da mahaifinsa?

7 Ko da yake Saul ya ci gaba da yi wa Jehobah rashin biyayya, Jonathan ya yi wa mahaifinsa biyayya a duk lokacin da hakan ya yiwu. Alal misali, sun yi yaƙi tare don su ceci mutanen Jehobah.​—⁠1 Sama’ila 31:​1, 2.

8, 9. A wace hanya ce muke kasancewa da aminci ga Allah idan muka yi biyayya ga masu mulki?

8 Kamar Jonathan, za mu iya kasancewa da aminci ga Jehobah ta wajen yin biyayya ga gwamnatin ƙasar da muke ciki a duk lokacin da hakan ya yiwu. Jehobah ya ƙyale waɗannan “masu-mulki” su shugabance mu, kuma yana bukatar mu yi musu biyayya. (Karanta Romawa 13:​1, 2.) Shi ya sa ya kamata mu yi wa wani ma’aikatan gwamnati biyayya ko a lokacin da ba ya bin doka ko kuma muna gani bai cancanci mu yi masa biyayya ba. Hakika, ya kamata mu yi biyayya ga dukan waɗanda Jehobah ya ba su iko su shugabance mu.​—⁠1 Korintiyawa 11:3; Ibraniyawa 13:⁠17.

Wata ‘yar’uwa tana salama da mijinta wanda yake shirin fita ya buga wasan golf kafin ta fita wa’azi da yaranta maza biyu

Wata hanya da za mu nuna amincinmu ga Jehobah ita ce ta yi wa abokin aurenmu ladabi, ko ba ya bauta wa Jehobah (Ka duba sakin layi na 9)

9 Wata ‘yar’uwa a Amirka ta Kudu mai suna Olga ta kasance da aminci ga Jehobah ta wajen yi wa mijinta biyayya ko da yake yana yi mata wulaƙanci.[1] (Ka duba ƙarin bayani.) A wani lokaci ba ya mata magana, a wani lokaci kuma yana mata baƙar magana domin ita Mashaidiyar Jehobah ce. Kuma ya gaya mata cewa zai bar ta ya tafi da yaran. Amma Olga ba ta rama “mugunta da mugunta” ba. Ta yi iya ƙoƙarinta don ta zama matan kirki. Tana dafa masa abinci da wanke kayansa da kuma kula da wasu a cikin iyalinsa. (Romawa 12:17) Ƙari ga haka, idan ta sami dama, takan bi shi sa’ad da yake so ya ziyarci danginsa da kuma abokansa. Alal misali, sa’ad da yake son ya tafi wani birni don jana’izar mahaifinsa, ta shirya kome da suke bukata don tafiyar, kuma ko da yake an yi jana’izar a cikin coci, ta jira shi a waje. Bayan shekaru da yawa, mijin Olga ya daina wulaƙanta ta domin haƙuri da biyayya da ta yi masa a kowane lokaci. Yanzu, yana ƙarfafa ta ta halarci taro kuma yana kai ta taro, a wani lokaci ma yana halartan taro tare da ita.​—⁠1 Bitrus 3:⁠1.

SA’AD DA MUKE TSAI DA SHAWARA A KAN WANDA ZA MU KASANCE DA AMINCI A GARE SHI

10. Ta yaya Jonathan ya san wanda ya kamata ya kasance da aminci a gare shi?

10 Sa’ad da Saul ya ce zai kashe Dauda, Jonathan yana bukatar ya tsai da shawara mai wuya. Yana so ya kasance da aminci ga mahaifinsa, amma kuma yana son ya kasance da aminci ga Dauda. Jonathan ya san cewa Allah yana tare da Dauda ba Saul ba, saboda haka, ya zaɓa ya kasance da aminci ga Dauda. Ya gargaɗi Dauda ya ɓoye kuma ya gaya wa Saul dalilin da ya sa bai kamata ya kashe Dauda ba.​—⁠Karanta 1 Sama’ila 19:​1-6.

11, 12. Ta yaya ƙaunarmu ga Allah take taimaka mana mu tsai da shawarar kasancewa da aminci a gare shi?

11 Wata ‘yar’uwa mai suna Alice daga Ostereliya tana bukatar ta tsai da shawara ga wanda za ta kasance da aminci a gare shi. Sa’ad da take nazarin Littafi Mai Tsarki, ta gaya wa ‘yan gidansu abubuwan da take koya. Ƙari ga haka, ta gaya musu za ta daina yin bikin Kirsimati tare da su, kuma ta bayyana dalilin da ya sa za ta yi hakan. Da farko, ‘yan gidansu sun yi baƙin ciki, amma daga baya sun yi fushi da ita sosai. Suna ganin cewa Alice ta yi watsi da su. Sai mahaifiyarta ta ce ba ta son ta ƙara ganin ta. Alice ta ce: “Na yi mamaki kuma na yi baƙin ciki sosai domin ina matuƙar ƙaunar ‘yan gidanmu. Duk da haka, na ƙudura niyya in ƙaunaci Jehobah da Ɗansa da dukan zuciyata, kuma na yi baftisma a taron da’ira na gaba.”​—⁠Matta 10:⁠37.

12 Kada mu yarda wani abu, kamar son wani rukunin wasanni ko makaranta ko kuma ƙasar da muke zaune a ciki ya fi ibadarmu ga Jehobah muhimmanci. Alal misali, Henry yana jin daɗin yin wani wasa da ake kira chess da rukunin makarantarsu kuma yana son ya ci wasan neman zakara wa makarantarsu. Amma, domin yana wasan chess a kowane ƙarshen mako, ba ya fita wa’azi ko kuma halartan taro yadda ya kamata. Henry ya ce ya lura cewa ya saka harkokin makaranta kan gaba fiye da ibadarsa ga Allah. Saboda haka, ya tsai da shawara ya daina wasan chess da yake wa makarantarsu.​—⁠Matta 6:⁠33.

13. Ta yaya kasancewa da aminci ga Allah zai taimaka mana mu jimre da matsaloli a cikin iyalinmu?

13 A wani lokaci, zai yi wuya a kasance da aminci ga dukan mambobin iyalinmu a lokaci ɗaya. Alal misali, Ken ya ce: “Ina son in riƙa ziyarar mahaifiyata da ta tsufa a kai a kai kuma ta zo ta zauna tare da mu a wani lokaci. Amma, mahaifiyata da matata ba sa shiri.” Ya ci gaba da cewa: “Idan har ina son in faranta wa ɗaya rai dole sai na sa ɗayan baƙin ciki.” Ken ya yi tunani a kan abin da Littafi Mai Tsarki ya ce kuma ya fahimci cewa a wannan yanayin ya kamata ya faranta wa matarsa rai kuma ya kasance da aminci a gare ta. Saboda haka, sai ya tsai da wata shawara da ta faranta wa matarsa rai. Ya bayyana wa matarsa dalilin da ya sa ya kamata ta so mahaifiyarsa. Ya kuma bayyana wa mahaifiyarsa dalilin da ya sa ya kamata ta riƙa daraja matarsa.​—⁠Karanta Farawa 2:24; 1 Korintiyawa 13:​4, 5.

SA’AD DA WANI ƊAN’UWA YA YI MANA MUMMUNAR FAHIMTA KO KUMA YA YI MANA RASHIN ADALCI

14. Ta yaya Saul ya yi wa Jonathan rashin adalci?

14 Za mu kasance da aminci ga Jehobah idan wani ɗan’uwa da ke ja-gora a cikin ikilisiya ya yi mana rashin adalci. Allah ne ya naɗa Sarki Saul, duk da haka bai bi da ɗansa yadda ya dace ba. Bai fahimci dalilin da ya sa Jonathan yake ƙaunar Dauda ba. Saboda haka, sa’ad da Jonathan ya yi ƙoƙari ya taimaki Dauda, Saul ya yi fushi sosai, kuma ya kunyantar da ɗansa a gaban mutane da yawa. Amma, duk da haka, Jonathan ya yi wa mahaifinsa biyayya. Ƙari ga haka, ya kasance da aminci ga Jehobah da kuma Dauda, wanda Allah ya zaɓa ya zama sarkin Isra’ila daga baya.​—⁠1 Sama’ila 20:​30-41.

15. Me ya kamata mu yi idan wani ɗan’uwa ya yi mana rashin adalci?

15 ‘Yan’uwan da suke ja-gora a cikin ikilisiyoyi a yau suna ƙoƙari su bi da kowa yadda ya dace. Amma waɗannan ‘yan’uwa ajizai ne, shi ya sa ba za su fahimci dalilin da ya sa muka yi wani abu a wani lokaci ba. (1 Sama’ila 1:​13-17) Saboda haka, idan aka yi mana rashin adalci ko kuma ba a fahimce mu ba, bari mu kasance da aminci ga Jehobah.

SA’AD DA CIKA ALKAWARINMU YAKE DA WUYA

16. A waɗanne yanayi ne za mu kasance da aminci ga Allah kuma ba za mu yi son kai ba?

16 Saul yana son Jonathan ya zama sarki a maimakon Dauda. (1 Sama’ila 20:31) Amma, Jonathan yana ƙaunar Jehobah kuma ya kasance da aminci a gare shi. Saboda haka, maimakon ya zama mai son kai, Jonathan ya zama abokin Dauda kuma ya cika alkawarinsa a gare shi. Hakika, duk wani amintacce mai ƙaunar Jehobah yana “cika alkawuran da ya yi ko ta halin ƙaƙa.” (Zabura 15:​4, Littafi Mai Tsarki) Za mu cika alkawuran da muka yi domin muna da aminci ga Allah. Alal misali, idan muka yi yarjejeniya na kasuwanci, za mu yi abin da muka yi alkawarinsa ko da hakan yana da wuya. Kuma idan muna fuskantar matsaloli a aurenmu, za mu nuna ƙaunarmu ga Jehobah ta wajen kasancewa da aminci ga mijinmu ko kuma matarmu.​—⁠Karanta Malakai 2:​13-16.

Wani mutum ya yi yarjejeniyar kasuwanci da wasu ma’aurata kuma daga baya ya gano cewa zai yi masa wuya ya cika alkawarinsa

Idan muka yi yarjejeniya na kasuwanci, za mu yi abin da muka yi alkawari za mu yi domin muna da aminci ga Allah (Ka duba sakin layi na 16)

17. Ta yaya wannan nazarin ya taimaka maka?

17 Ya kamata mu kasance da aminci ga Allah ko da a mawuyacin yanayi ne, kamar Jonathan. Saboda haka, bari mu kasance da aminci ga ‘yan’uwanmu sa’ad da suka ɓata mana rai. Sa’annan za mu sa Jehobah farin ciki, kuma hakan ne zai fi sa mu farin ciki. (Misalai 27:11) Muna da tabbaci cewa zai albarkace mu kuma ya kula da mu. A talifi na gaba za mu za mu koyi darasi daga wasu mutane a zamanin Dauda, da suka kasance da aminci da kuma waɗanda ba su yi hakan ba.

^ [1] (sakin layi na 9) An canja wasu sunaye.

MA’ANAR WASU KALMOMI

  • Kasancewa da aminci ga Jehobah: Muna ƙaunar Jehobah kuma muna yi masa biyayya a kowane lokaci. A mawuyacin yanayi, muna tunanin abin da Jehobah yake so mu yi kuma mu yi masa biyayya domin muna ƙaunarsa fiye da kowa ko kuma wani abu

  • “Masu mulki”: Gwamnatoci da ma’aikatansu da Jehobah ya ba su iko a kanmu. Yana so mu daraja su kuma mu yi musu biyayya idan abin da suke so mu yi ya jitu da umurnin da Jehobah ya ba mu

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba