Na Samu Albarka Don Yin Canje-canje A Rayuwa
James A. Thompson ne ya ba da labarin
Sa’ad da aka haife ni a kudancin Amirka a shekara ta 1928, doka ta hana farar fata da baƙar fata su yi cuɗanya. Taka wannan dokar za ta iya sa a saka mutum cikin kurkuku ko kuma abin da ya fi hakan tsanani.
A WANNAN lokacin a wasu ɓangarorin Amirka, Shaidun Jehobah da farar fata ne da kuma baƙar fata suna da ikilisiyoyi da da’irori da kuma gundumomi dabam-dabam. A shekara ta 1937, mahaifi na ya zama bawan rukuni (wanda yanzu ake kiran mai tsara ayyukan rukunin dattawa) na ikilisiyar baƙar fata da ke birnin Chattanooga a jihar Tennessee. Henry Nichols ne bawan rukuni na ikilisiyar farar fata.
Ba na mantawa da wani dare sa’ad da nake matashi da na zauna a barandan da ke gidanmu kuma ina saurarawa sa’ad da Mahaifina da Ɗan’uwa Nichols suke magana. Ko da yake ban fahimci kome da suka yi magana a kai ba, ina jin daɗin kasancewa kusa da Mahaifina sa’ad da su biyu suke magana game da yadda za a fi yin aikin wa’azi da kyau a cikin irin wannan yanayin.
A farkon shekara ta 1930, bala’i ya faɗa wa iyalinmu. Mahaifiyata ta rasu sa’ad da take ’yar shekara 20. Babana kaɗai ya soma kula da yata Doris, ’yar shekara huɗu da kuma ni ɗan shekara biyu. Ko da yake Babana bai daɗe da yin baftisma ba, ya samu ci gaba sosai a ruhaniya.
Misalan da Suka Taimaka Mini a Rayuwa
A shekara ta 1933, Baba ya samu wata ’yar’uwa Kirista mai ruhaniya mai suna Lillie Mae Gwendolyn Thomas, kuma ba da daɗewa ba suka yi aure. Da Baba da Mama sun kafa mini da Doris misali mai kyau wajen bauta wa Jehobah da aminci.
A shekara ta 1938 an gaya wa ikilisiyoyi na Shaidun Jehobah su goyi bayan wata zartarwa cewa za a riƙa naɗa dattawa a cikin ikilisiyoyi daga hedkwatarmu da ke Brooklyn, New York, maimakon a zaɓe su a yankin. Sa’ad da wasu a birnin Chattanooga suka yi jinkirin amince da canjin, Baba ya sanar cewa ya goyi bayan canjin ƙungiyar da dukan zuciyarsa. Misalin amincinsa tare da haɗin kan Mama da dukan zuciyarta sun taimaka mini har wa yau.
Baftisma da kuma Hidima ta Cikakken Lokaci
A shekara ta 1940 mutane da yawa a cikin ikilisiyarmu sun yi hayar bas kuma suka yi tafiya zuwa taron gunduma a birnin Detroit, Michigan. Wasu da suke cikin bas ɗin tare da mu sun yi baftisma a wurin. Wasu sun yi mamaki abin da ya sa ban yi ba, tun da yake na soma wa’azi tun ina shekara biyar kuma ina da ƙwazo a hidima.
Sa’ad da suka gaya mini hakan, na amsa cewa “Ban fahimci dukan abin da yin baftisma ya ƙunsa ba.” Baba ya ji ni kuma ya yi mamaki. Tun daga lokacin, ya ƙara ƙoƙari sosai don ya taimake ni na fahimci abin da baftisma take nufi da kuma muhimmancinta. Wata rana da ake sanyin sosai, bayan wata huɗu a ranar 1 ga watan Oktoba, 1940, aka yi mini baftisma a cikin wani tafki da ke waje da birnin Chattanooga.
Sa’ad da nake ɗan shekara 14, na soma hidimar majagaba a lokacin hutun rani a makaranta. Na yi wa’azi a ƙananan garuruwa da ke jihar Tennessee da kuma jihar Georgia da ke kusa. Nakan tashi da sassafe, na ɗauki abincin rana kuma na shiga jirgin ƙasa ko kuma bas zuwa yankin da ƙarfe shida na safe. Nakan dawo wajen ƙarfe shida na yamma. Sau da yawa ina cinye abincin kafin rana ya yi. Ko da yake ina da kuɗi, ba zan iya shiga wani kanti na saya ƙarin abinci ba domin ni baƙar fata ne. Wata rana, na shiga wani kanti don na sayi ƙanƙara mai zaƙi (ice-cream) kuma aka ce na fita. Wata farar fata ta fito ta kawo mini ɗaya.
Yayin da na shiga makarantar sakandare, ƙungiyar ’yancin jama’a tana ƙara ƙarfi a Kudu. Ƙungiyoyi kamar National Association for the Advancement of Colored People [Hulɗar Ci Gaba na Mutane Masu wani Launi] suna ƙarfafa ɗalibai su yi siyasa. An aririce mu mu goyi bayansu. Makarantu da yawa na baƙar fata har da tamu, sun ƙuduri aniya su tallafa musu sosai. An matsa mini “na tallafa wa launin fatarmu” kamar yadda suka kira shi. Amma na ƙi, na bayyana cewa Allah ba ya wariya kuma ba ya son wani launin fata fiye da wani. Ina sauraron Allah ya yi maganin irin wannan rashin adalci.—Yoh. 17:14; A. M. 10:34, 35.
Ba da daɗewa ba bayan na kammala makarantar sakandare, sai na tsai da shawara na ƙaura zuwa Birnin New York. Amma, a hanya sai na tsaya a birnin Philadelphia, da ke Pennsylvania don na ziyarci abokai da na samu a lokacin da na halarci wani taron gunduma. A ikilisiyar da ke wajen ne na fara halartar taro da masu baƙar fata da kuma farar fata. A lokacin ziyararsa, mai kula mai ziyara ya kai ni gefe kuma ya gaya mini cewa an ba ni aiki a taro na gaba. Hakan ya sa ya yi mini sauƙi na tsai da shawara na zauna a wajen.
Wata matashiya mai suna Geraldine White, Gerri yadda nake kiranta daga baya tana cikin abokai da na samu a birnin Philadelphia. Ta san Littafi Mai Tsarki sosai kuma ta ƙware wajen tattaunawa da masu gida a hidimar ƙofa ƙofa. Abin da ya fi muhimmanci a gare ni shi ne cewa tana da maƙasudin zama majagaba kamar ni. Mun yi aure a ranar 23 ga Afrilu, 1949.
Gayyata Zuwa Gileyad
Burinmu da farko shi ne mu halarci makarantar Gileyad kuma mu yi hidima a matsayin masu-wa’azi na ƙasashen waje. Mun yi farin cikin daidaita yanayinmu don mu cancanci masu halartan makarantar Gileyad. Jim kaɗan, aka ƙaurar da mu zuwa garin Lawnside da ke birnin New Jersey; bayan haka muka je Chester, da ke Pennsylvania; sai kuma a ƙarshe muka je Birnin Atlantic, da ke New Jersey. Sa’ad da muke Birnin Atlantic, mun cancanta don zuwa makarantar Gileyad, da yake mun kai shekara biyu da yin aure. Amma ba a amsa mana ba. Me ya sa?
A farkon shekara ta 1950 zuwa 1959, an kwashi matasa maza da yawa don yin aikin soja kuma su yi faɗa da ake yi a Koriya. Masu kwashe mutane a Philadelphia suna gāba da Shaidun Jehobah don tsakatsakinmu. A ƙarshe, wani alƙali ya gaya mini cewa binciken da ma’aikatan ƙungiyar FBI suka yi game da tsakatsakina gaskiya ne. Saboda haka, a ranar 11 ga Janairu, 1952, sashen Presidential Appeal Board ya keɓe ni daga aikin soja a matsayina na mai hidima.
A watan Agusta na wannan shekara, ni da matata Gerri muka samu gayyatar halartar aji na 20 na makarantar Gileyad, wanda aka soma a watan Satumba. A lokacin makaranta, muna sa rai za a tura mu hidima a wata ƙasa. Yata Doris ta sauke karatu daga aji na 13 na makarantar Gileyad kuma tana hidima a ƙasar Brazil. Ni da Gerri mun yi mamaki da aka tura mu hidimar kula da da’ira, wato, muna ziyarar ikilisiyoyi na baƙar fata da ke jihar Alabama da ke kudancin ƙasar! Hakan ya ɗan sa mu baƙin ciki, don mun sa rai yin hidima a wata ƙasa.
Ikilisiya ta farko da muka kai ziyara tana birnin Huntsville. Da muka isa, mun tafi gidan wata ’yar’uwa Kirista inda za mu zauna. Yayin da muke sauke kayanmu, mun ji tana faɗa ta waya cewa “Yaran sun iso.” A lokacin, mu ’yan shekara 24 ne. Sa’ad da muke ziyarar wannan da’irar, ba mu manta da kalmar wannan ’yar’uwar cewa mu yara ne ba.
Sau da yawa ana kiran Kudu Bible Belt, domin yawancin mutane a wajen suna daraja Littafi Mai Tsarki sosai. Saboda haka, sau da yawa, muna soma tattaunawa da wannan gabatarwa guda uku:
(1) Gajeren kalami game da yanayin duniya.
(2) Maganin matsalar da Littafi Mai Tsarki ya faɗa.
(3) Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce dole ne mu yi.
Bayan haka, sai mu ba da littafin da ya dace da ke bayyana Littafi Mai Tsarki. Domin yadda muke samun nasara ta wajen yin amfani da wannan gabatarwa, an ba ni jawabi a Babban Taro na New World Society Assembly [Taro na Jam’iyyar Sabuwar Duniya], da aka yi a birnin New York a shekara ta 1953. A wajen na yi gwajin wannan gabatarwa guda uku.
Ba da daɗewa ba, a rani na shekara ta 1953, aka tura ni hidima a da’irar baƙar fata da ke Kudu a matsayin mai kula da gunduma. Yankinmu ya ƙunshi dukan wurare na jihar Virginia zuwa Florida har da yammancin jihar Alabama da kuma Tennessee. Hakika, masu kula masu ziyara suna bukatar su zama waɗanda za su iya daidaita a kowane irin yanayi. Alal misali, sau da yawa muna zama a gidaje da babu ruwan famfo a ciki ɗakin kuma muna yin wanka a cikin bāho da ke bayan kicin. Abin farin ciki ne cewa wurin ne ya fi ɗumi a gidan!
Ƙalubalen Wariyar Al’umma
Yin hidima a Kudu yana bukatar yin tunani da kuma basira don a yi abubuwa. Ba a barin baƙar fata su yi amfani da mawanka na jama’a. Saboda haka, matata Gerri za ta je wurin kuma ta bayyana cewa kayan na “Matar Thompson” ne. Mutane da yawa suna ganin ita baiwa ce kuma “Matar Thompson” uwar gida ce. Sa’ad da masu kula da gunduma suke nuna fim na The New World Society in Action, nakan kira kantin ta waya na gaya musu su ajiye wa “Malam Thompson” babban talabijin. Daga baya, sai na je kantin na ɗauki talabijin. A ko da yaushe muna nuna halin kirki kuma mu yi hidimarmu ba tare da matsala ba.
Da akwai wata irin wariya kuma da ake nuna wa mutane daga Arewa. A wani lokaci, wata jarida ta ba da rahoto cewa James A. Thompson, Ƙarami, na Watchtower Bible and Tract Society da ke New York zai ba da jawabi a babban taro. Wasu suna ganin hakan yana nufin cewa na fito daga birnin New York ne, kuma aka hana mu yin amfani da babban ɗaki da ke cikin wata makaranta. Sai na tafi wurin hukumar makarantar kuma na bayyana musu cewa na yi makaranta a birnin Chattanooga. Sai aka ba mu izinin yin taronmu na da’ira.
Hayaniya na wariyar al’umma ta yi tsanani a tsakiyar shekara ta 1950 zuwa 1959, kuma a wasu lokatai ana yin faɗa. A taron gunduma da yawa da aka yi a shekara ta 1954, wasu Shaidu sun yi fushi cewa ba a ba baƙar fata jawabi ba. Mun ƙarfafa ’yan’uwanmu masu baƙar fata su yi haƙuri. A rani na gaba aka ba ni jawabi. Bayan hakan, aka ba ƙarin ’yan’uwa masu baƙar fata da ke Kudu jawabi a tsarin ayyuka.
Da shigewar lokaci aka daina faɗar ƙabilanci a Kudu, kuma ikilisiyoyi suka soma yin taro tare. Hakan yana bukatar a mai da masu shela zuwa wasu ikilisiyoyi da kuma daidaita yankuna na ikilisiya da kuma hakkin ’yan’uwa masu kula. Wasu baƙar fata da kuma farar fata ba sa son sabon shirin. Amma, yawancin mutane ba sa yin wariya, kamar Ubanmu na samaniya. Mutane da yawa sun zama abokai na kud da kud duk da launin fatarsu. Iyalinmu ta fuskanci hakan a shekara ta 1930 zuwa 1949 yayin da nake girma.
Sabuwar Hidima
A watan Janairu na shekara ta 1969, ni da Gerri muka samu gayyata mu tafi ƙasar Guyana da ke Amirka ta Kudu, kuma mun amince da hakan da farin ciki. Da farko muka tafi Brooklyn, New York inda na samu koyarwar kula da aikin wa’azi a ƙasar Guyana. Mun isa wurin a watan Yuli 1969. Bayan mun yi shekara 16 a aikin ziyara, yin gyara ne mai girma mu je mu kasance a wuri ɗaya. A yawancin kwanaki, Gerri tana hidimar fage a matsayin mai wa’azi a wata ƙasa, ni kuma ina aiki a ofishin reshe.
Aiki na ya ƙunshi yin kome har da yanka ciyayi da kuma aika littattafai zuwa ga ikilisiyoyi 28 da kuma saƙonni zuwa hedkwata da ke Brooklyn. Ina yin aiki sa’o’i sha huɗu zuwa sha biyar kowacce rana. Aikin ya yi mana yawa, amma mun ji daɗin aikinmu. Sa’ad da muka isa wurin, masu shela 950 ne a ƙasar Guyana; amma yanzu akwai fiye da masu shela 2,500.
Ko da yake mun ji daɗin yanayin wurin da ’ya’yan itace masu daɗi da kuma kayan lambu, ainihin farin cikinmu shi ne mutane masu tawali’u da suke son gaskiya suna koya game da Mulkin Allah. Sau da yawa Gerri tana yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane 20 a kowanne mako, kuma yawancin waɗanda muka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su sun ci gaba da nazarin har sun yi baftisma. Da shigewar lokaci, wasu suka zama masu hidimar majagaba da dattawan ikilisiya da kuma waɗanda suka je makarantar Gileyad don kasance masu-wa’azi a ƙasashen waje.
Ƙalubale, Musamman na Rashin Lafiya
A shekara ta 1983 iyayena da suke ƙasar Amirka sun bukaci mai taimako. Doris da Gerri da kuma ni muka yi taro na iyali don mu tsai da shawara. Doris, wadda ta yi hidima ta shekara 35 a matsayin mai wa’azi a ƙasashen waje a Brazil ta ba da kai ta dawo don ta kula da su. Ta ce, me ya sa mutane biyu za su bar aikin wa’azi a ƙasar waje da yake mutum ɗaya ma zai iya yin aikin? Tun rasuwar iyayenmu, Doris ta zauna a birnin Chattanooga kuma tana hidima a matsayin majagaba na musamman.
Bincike ya nuna cewa ina da ciwon daji a shekara ta 1995 da haka na dawo ƙasar Amirka. Mun zauna a birnin Goldsboro, da ke Arewancin Carolina, domin hakan ba shi da nisa daga iyalina da ke Tennessee da kuma wurin da Gerri take a Pennsylvania. Da yake na sami sauƙi daga ciwon dajin, muna yin hidima a ikilisiyar Goldsboro a matsayin majagaba na musamman marasa ƙarfi.
Yayin da nake tunawa da hidima ta cikakken lokaci na fiye da shekara 65 da muka yi, ina godiya cewa Jehobah ya albarkace ni da Gerri don canje-canjen da muka yi don mu bauta masa. Kalamin Dauda gaskiya ne: “Kai, ya [Jehobah], amintacce ne ga waɗanda ke da aminci”!—2 Sam. 22:26, Littafi Mai Tsarki.
[Hotona a shafi na 3]
Mahaifina da kuma Ɗan’uwa Nichols sun ƙafa mini misali mai kyau
[Hotona a shafi na 4]
Ni da Gerri, mun shirya zuwa makarantar Gileyad a shekara ta 1952
[Hotona a shafi na 5]
Bayan da muka sauke karatu a makarantar Gileyad, an tura mu yin hidimar masu kula masu ziyara a Kudu
[Hoto a shafi na 6]
Masu kula masu ziyara da matansu suna shirin halartar taron gunduma na baƙar fata da kuma farar fata a shekara ta 1966
[Hoto a shafi na 7]
Mun yi farin ciki a hidimar da muka yi a ƙasar Guyana