Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 6/15 pp. 18-19
  • ‘Ka Taho da Littattafan Nan, Musamman Fatun Nan Masu Rubutu’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Ka Taho da Littattafan Nan, Musamman Fatun Nan Masu Rubutu’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Kiristoci Suka Yi Amfani da Naɗaɗɗun Littattafai
  • Mene ne Za Mu Iya Koya Daga Misalin Bulus?
  • Darussa Daga Wasiƙu zuwa ga Tassalunikawa da Timothawus
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Mecece Ranar Shari’a?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Ka Sami Ci Gaba A Ruhaniya Ta Wajen Bin Misalin Bulus
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 6/15 pp. 18-19

‘Ka Taho da Littattafan Nan, Musamman Fatun Nan Masu Rubutu’

DA WAƊANNAN kalamai na sama, manzo Bulus ya aririce Timotawus wanda ke aikin wa’azi tare da shi a ƙasashen waje ya kawo masa wasu littattafai. Waɗanne irin naɗaɗɗun littattafai da fatu ne Bulus yake maganarsu? Me ya sa ya faɗi hakan? Kuma mene ne za mu iya koya daga wannan aika?

Sa’ad da Bulus ya rubuta waɗannan kalaman a tsakiyar ƙarni na farko A.Z., an riga an raba littattafai 39 na Nassosin Ibrananci zuwa littattafai 22 ko kuma 24, waɗanda yawanci cikinsu wataƙila suna cikin naɗaɗɗun littattafai dabam dabam. Farfesa Alan Millard ya rubuta cewa “masu arziki suna iya sayan” waɗannan naɗaɗɗun littattafai ko da yake suna da tsada. Wasu suna da aƙalla guda a cikinsu. Alal misali, Habasha bābā yana da wani naɗaɗɗen littafi a karusarsa kuma yana “karatun annabi Ishaya.” ‘Yana sarauta da yawa ƙarƙashin Kandis, sarauniyar Habashawa kuma kayan ajiyarta duka suna hannunsa.’ Babu shakka, yana da arziki sosai da yake yana da littattafan Nassosi.—A. M. 8:27, 28.

Sa’ad da yake aika saƙo zuwa wurin Timotawus, Bulus ya rubuta: “Sa’ad da za ka taho, ka zo da alkyabban nan da na bari a wurin Karbus a Taruwasa, da kuma littattafan nan, tun ba ma fatun nan masu rubutu ba.” (2 Tim. 4:13, Littafi Mai Tsarki) Hakan ya nuna cewa Bulus yana da littattafai masu yawa. A cikin duk littattafan da Bulus yake da su, Kalmar Allah ce ta fi muhimmanci a gare shi. Game da kalmar nan “fatu” da ke cikin wannan ayar, masanin Littafi Mai Tsarki, A. T. Robertson ya lura cewa: “Wataƙila waɗannan littattafai na Tsohon Alkawari ne, littattafan fatu sun fi na ganyen papyrus tsada.” Tun yana matashi, an karantar da Bulus “a wurin sawayen Gamaliel” wanda ya koyar da Doka ta hannun Musa kuma dukan mutanen sun ɗaukaka shi. Saboda haka, daidai ne Bulus ya sayi naɗaɗɗun littattafai na Kalmar Allah.—A. M. 5:34; 22:3.

Yadda Kiristoci Suka Yi Amfani da Naɗaɗɗun Littattafai

Amma, yawancin mutane ba su da Nassossi Masu Tsarki. Yaya yawancin Kiristoci a wannan zamanin suka ji da kuma karanta Kalmar Allah? Za mu iya fahimtar wani abu daga wasiƙa ta farko da Bulus ya rubuta wa Timotawus. Ya rubuta: “Ka maida hankali ga karatu, da gargaɗi, da koyarwa, har na zo.” (1 Tim. 4:13) Yin karatu a gaban jama’a sashe ne na taron ikilisiyoyin Kirista, al’ada ce na mutanen Allah tun daga zamanin Musa.—A. M. 13:15; 15:21; 2 Kor. 3:15.

A matsayin dattijo, Timotawus yana bukatar ya ‘yi karatu’ a gaban jama’a, kuma hakan zai taimaki waɗanda ba su da Nassossi. Hakika, a lokacin da yake karanta Kalmar Allah a gaban jama’a duka suna saurarawa don su ji duk kalmomin, kuma iyaye da yara sun tattauna abin da aka karanta musu a taron a gida.

Takardun Tekun Gishiri na Ishaya da aka fi sani ya kai tsawon kafa 24. Naɗaɗɗen littafin zai yi nauyi, tun da yake yana da sanda a gefe-gefen kuma sau da yawa yana da bango. Wataƙila yawancin Kiristoci ba sa iya ɗaukan da yawa zuwa wa’azi. Ko da Bulus yana da wasu naɗaɗɗun littattafan Nassossi don yin amfani da su, wataƙila bai iya ɗeban dukan takardunsa sa’ad da yake yin tafiye-tafiyensa ba. Babu shakka ya bar wasu takardun wurin abokinsa Karbus a garin Taruwasa.

Mene ne Za Mu Iya Koya Daga Misalin Bulus?

Kafin ya yi wannan roƙon, Bulus da aka saka a kurkuku a lokaci na biyu, ya rubuta: “Na yi yaƙi mai-kyau, na kure fagen . . . Saura an ajiye mini rawanin adalci.” (2 Tim. 4:7, 8) Wataƙila ya rubuta waɗannan kalaman a misalin shekara ta 65 A.Z. sa’ad da Nero yake tsananta wa Kiristoci. Ya sha wuya sosai a fursuna a wannan lokacin. Hakika, ya fahimci cewa hukuncinsa ya kusa. (2 Tim. 1:16; 4:6) Hakika, Bulus ya nuna cewa yana son takardunsa su kasance kusa da shi. Ko da yake yana da tabbaci cewa ya yi yaƙi mai-kyau har ƙarshe, ya yi marmari ya ci gaba da ƙarfafa kansa ta wurin nazarin Kalmar Allah.

Wataƙila Timotawus yana a Afisa sa’ad da ya samu aikan da Bulus ya yi masa. (1 Tim. 1:3) Daga Afisa zuwa Roma ta Taruwasa aƙalla mil 1,000 ne. Kuma a cikin wannan wasiƙar, Bulus ya aririce Timotawus: “Ka yi hanzari ka zo kafin” lokacin ɗari. (2 Tim. 4:21) Littafi Mai Tsarki bai bayyana ba ko Timotawus ya sami kwalekwalen da zai kai shi Roma a lokacin da Bulus yake bukata.

Mene ne za mu iya koya daga roƙon da Bulus ya yi cewa a aiko masa da ‘littattafan nan, musamman fatun nan masu rubutu’? Ya ci gaba da marmarin karanta Kalmar Allah a mawuyacin lokaci a rayuwarsa. Wannan ne dalilin da ya sa ya kasance a faɗake a ruhaniya da ƙwazo da kuma ya ba da ƙarfafa ga mutane.

A yau, mu masu albarka ne idan muna da namu kofi na cikakken Littafi Mai Tsarki! Wasu cikinmu suna da su da dama da kuma wasu juyi. Kamar Bulus, muna bukatar mu kasance da marmari ga Kalmar Allah don mu samu zurfafan fahimta na Nassosi. A cikin hurarrun wasiƙu goma sha huɗu da Bulus ya samu gatan rubutawa, wasiƙa ta biyu ga Timotawus ita ce ta ƙarshe. Roƙon da ya yi ya bayyana ne a ƙusan ƙarshen littafin. Hakika, aikan da Bulus ya yi wa Timotawus na ‘ya taho da littattafan nan, musamman fatun nan masu rubutu,’ yana ɗaya daga cikin rubutunsa na ƙarshe.

Shin kana marmarin yin yaƙi mai-kyau na imani har ƙarshe, kamar yadda Bulus ya yi? Shin kana son ka kasance da ƙwazo a hidimar Jehobah, kuma ka kasance a shirye ka yi aikin wa’azi muddin Ubangijinmu yana so mu yi hakan? Shin me ya sa ba za ka yi kamar yadda Bulus ya ƙarfafa Kiristoci su yi ba? “Ka maida hankali da kanka, da kuma koyarwarka” ta wurin yin marmari da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki kullum, da mutane da yawa yanzu suke da shi fiye da dā kuma ya fi fatu masu rubutu sauƙin ɗauka.—1 Tim. 4:16.

[Taswira/​Hotona a shafi na 18, 19]

(Don ganin cikakken rubutun, ka duba littafin)

Afisa

Taruwasa

Roma

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba