Ka Bi Kristi, Kamiltaccen Shugaba
SHUGABANIN ’yan Adam sukan saɓa alkawarin da suka yi wa waɗanda suke goyon bayansu. Amma ba haka shugabancin Kristi yake ga waɗanda suke goyon bayansa ba. Yesu ya ce: “Ku zo gareni, dukanku da ku ke wahala, masu-nauyin kaya kuma, ni kuwa in ba ku hutawa. Ku ɗaukar wa kanku karkiyata, ku koya daga wurina; gama ni mai-tawali’u ne, mai-ƙasƙantar zuciya: za ku sami hutawa ga rayukanku.” (Mat. 11:28, 29) Shugabancin Yesu yana ba da gamsuwa da farin ciki. Yana ƙaunar taliki da tsiyayyu, kuma yana gayyatarsu su kasance a ƙarƙashin karkiyarsa. Mene ne bin shugabancin Yesu ya ƙunsa?
Manzo Bitrus ya rubuta: “Kristi kuma ya sha azaba dominku, yana bar maku gurbi, domin ku bi sawunsa.” (1 Bit. 2:21) Me ya sa yake da muhimmancin mu bi shugabancin Yesu? A ce ku da yawa kuna son ku ketare fagen da aka shuka boma-bomai a ƙasa kuma ɗaya cikinku ne kawai ya san yadda zai ketare wurin lafiya. Shin ba za ku bi sawunsa sosai ba? Hakazalika, rayuwarmu ta nan gaba ta dangana ga bin sawun Yesu sosai. Yin hakan ya haɗa da saurara da kuma yin biyayya ga umurninsa da kuma haɗa kai da waɗanda ke wakiltarsa.
Ka Ji Kuma Ka Yi Biyayya
Kusan ƙarshen Huɗubarsa a kan Dutse, Yesu ya ce: “Kowanene fa mai-jin waɗannan zantattuka nawa, yana kuwa aikata su, za a kwatanta shi da mutum mai-hikima, wanda ya gina gidansa bisa pa: Ruwa ya sabko, rigyawa ta zo, iska ta hura, ta buga gidan nan; ba ya faɗi ba: gama an kafa shi bisa pa.”—Mat. 7:24, 25.
Yesu ya ce wanda ke saurara kuma yake yin biyayya ga maganarsa “mai-hikima” ne. Shin muna nunawa ta cikakkiyar biyayyarmu cewa muna daraja kuma muna godiya ga misalin Yesu, ko kuwa muna zaɓar dokokin Yesu waɗanda suke da sauƙin bi kaɗai? Yesu ya ce: “Kullum ina aika abin da ya gamshe [Allah].” (Yoh. 8:29) Bari mu yi ƙoƙari mu yi koyi da misalinsa.
A ƙarni na farko, manzannin sun kafa misali mai kyau na ba da kai ga shugabancin Kristi. A wani lokaci, Bitrus ya ce wa Yesu: “Ga mu, mun bar abubuwa duka, mun bi ka.” (Mar. 10:28) Hakika, manzannin sun daraja shugabancin Yesu sosai har sun yarda su bar abubuwa duka don su bi shi.—Mat. 4:18-22.
Ka Ba da Haɗin Kai ga Wakilan Kristi
Gab da mutuwarsa, Yesu ya ambata wata hanya da za mu iya bin shugabancin sa. Ya ce: “Wanda ya karɓi kowanene da na ke aikowa, ni yake karɓa.” (Yoh. 13:20) Hakika, Yesu ya kira wakilansa shafaffu “’yan’uwan[sa].” (Mat. 25:40) Bayan da Yesu ya tashi daga matattu kuma ya koma cikin sama, an naɗa “’yan’uwan[sa]” su wakilce shi, suna aiki a “madadin Kristi” a matsayin jakadu da suke gayyatar mutane su sulhunta da Jehobah Allah. (2 Kor. 5:18-20) Ba da kai ga shugabancin Kristi ya haɗa da ba da kai ga “’yan’uwan[sa].”
Ya dace mu bincika yadda muke aikatawa ga shawarar Nassosi da ake ba da a cikin littattafai da ke bayyana Littafi Mai Tsarki. Muna tunawa da zantuttukan Kristi, ta yin nazarin Nassosi da kuma halartar tarurrukan ikilisiya. (2 Bit. 3:1, 2) Muna nuna godiyarmu ga abinci na ruhaniya da ake tanadarwa ta yin amfani da shi a kai a kai. Yaya ya kamata mu aikata idan an maimaita wasu shawara a wasu lokatai? Alal misali, Kalmar Allah ta shawarce Kiristoci su yi aure “cikin Ubangiji” kaɗai. (1 Kor. 7:39) Fiye da ƙarni guda, an tattauna wannan batun a kai a kai a cikin Hasumiyar Tsaro. Babu shakka, ’yan’uwan Kristi suna nuna kulawarsu ga dangantakarmu da Jehobah ta buga talifofi game da wannan da kuma wasu hurarrun batutuwa. Yin biyayya ga waɗannan tunasarwar hanya ɗaya ce da take nuna cewa muna bin kamiltaccen Shugabanmu, wato, Yesu Kristi.
Misalai 4:18 ya ce: “Tafarkin mai-adalci yana kama da haske na ketowar alfijir, wanda ya ke haskakawa gaba gaba har zuwa cikakkiyar rana.” Ana samun ci gaba ta shugabancin Yesu. Wata hanyar kuma da za mu ba da kai ga “’yan’uwan” Kristi ita ce ta amincewa da kowacce gyara da aka yi ga fahiminmu na gaskiyar Nassosi da “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ya wallafa.—Mat. 24:45.
Muna kuma nuna haɗin kanmu ga “’yan’uwan” Kristi ta wajen ba da kai ga masu kula a ikilisiyar Kirista. Manzo Bulus ya ce: “Ku yi biyayya da waɗanda ke shugabanninku, ku sarayar da kanku gare su: gama suna yin tsaro sabili da rayukanku.” (Ibran. 13:17) Alal misali, dattijo zai iya ƙarfafa mu a kan muhimmancin yin Bauta ta Iyali da yamma a kai a kai ko kuma zai iya ba da shawarwari a kan wasu fannoni na hidimarmu ta fage. Mai kula mai ziyara zai iya ba mu wasu shawarwari na Nassosi game da wani fanni na rayuwarmu a matsayin Kirista. Idan mun yi biyayya ga waɗannan shawarwarin, muna nuna cewa muna bin Shugabancin Yesu.
Duniyar nan ba ta da shugabanci mai kyau. Amma abin farin ciki ne mu bi shugabancin Kristi na ƙauna! Bari mu yi iya ƙoƙarin mu yi biyayya ga Shugabanmu kuma mu ba da haɗin kai ga waɗanda yake amfani da su a yau.
[Hotuna da ke shafi na 27]
Kuna amincewa da shawara ta Nassi na kada ku auri waɗanda ba masu bi ba ne?