Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 5/15 pp. 16-20
  • Wane Ne Ya Fi Muhimmanci A Rayuwarka?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Wane Ne Ya Fi Muhimmanci A Rayuwarka?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Batun da Ya Taso a Lambun Adnin
  • Batun da Ya Taso a Zamanin Ayuba
  • Amsa Mai Kyau da Yesu Ya Ba Da
  • Amsarmu ga Tambayar
  • Wane Irin Mutum Ne Ya Kamata Ka Zama
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ayuba Ya Ɗaukaka Sunan Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Rayuwa a Hanyar da Take Faranta wa Allah Rai
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Ayuba Mutumi Ne Mai Jimiri Da Aminci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 5/15 pp. 16-20

Wane Ne Ya Fi Muhimmanci A Rayuwarka?

“Kai kaɗai ne Maɗaukaki bisa dukan duniya.”—ZAB. 83:18.

1, 2. Me ya sa sanin sunan Jehobah kawai ba zai sa mu samu ceto ba?

WATAƘILA lokaci na farko da ka ga sunan nan Jehobah shi ne lokacin da aka nuna maka shi a cikin Zabura 83:18. Wataƙila ka yi mamaki sa’ad da ka karanta waɗannan kalaman: “Domin su sani kai, wanda sunanka Jehovah ne, kai kaɗai ne Maɗaukaki bisa dukan duniya.” Babu shakka, tun lokacin, ka yi amfani da wannan nassin don ka taimaka wa mutane su san ƙaunataccen Allahnmu, Jehobah.—Rom. 10:12, 13.

2 Ko da yake yana da muhimmanci mutane su san sunan Jehobah, amma ba shi ke nan ba. Ka lura da abin da marubucin wannan zaburar ya nanata da yake da muhimmanci don mu samu ceto sa’ad da ya ce: “Kai kaɗai ne Maɗaukaki bisa dukan duniya.” Hakika, Jehobah ne ya fi muhimmanci a dukan sararin samaniya. Yana da iko ya bukaci dukan halittunsa su ba da kai gare shi, tun da yake shi ne ya Halicci kome. (R. Yoh. 4:11) Muna da dalilai masu kyau na yi wa kanmu wannan tambayar, ‘Wane ne ya fi muhimmanci a rayuwata?’ Yana da muhimmanci mu mai da hankali sosai don bincika amsarmu ga wannan tambayar!

Batun da Ya Taso a Lambun Adnin

3, 4. Ta yaya Shaiɗan ya yi nasara wajen rinjayar Hauwa’u, kuma da wane sakamako?

3 Abin da ya faru a lambun Adnin ya nuna muhimmancin wannan tambayar. A wurin mala’ika mai tawaye wanda daga baya aka kira shi Shaiɗan Iblis ya rinjayi mace na farko, Hauwa’u, ta fi daraja sha’awarta fiye da umurnin Jehobah na kada su ci daga ’ya’yan itacen. (Far. 2:17; 2 Kor. 11:3) Ta faɗa wa wannan jarrabar, kuma da hakan ta nuna rashin biyayya ga ikon mallaka na Jehobah. Hauwa’u ba ta ɗauki Jehobah a matsayin Wanda ya fi muhimmanci a rayuwarta ba. Amma yaya Shaiɗan ya yi nasara wajen rinjayar Hauwa’u?

4 Shaiɗan ya yi amfani da dabaru da yawa sa’ad da yake tattaunawa da Hauwa’u. (Karanta Farawa 3:1-5.) Da farko, Shaiɗan bai yi amfani da sunan Jehobah ba. Ya dai ambata “Allah” kaɗai. Akasin haka, marubucin Farawa ya yi amfani da ainihin sunan na Ibrananci na asali, wato, Jehobah a farkon aya ta wannan surar. Na biyu, maimakon ya yi magana a kan abin da Allah ya ‘dokace’ su, Shaiɗan ya yi tambaya game da abin da Allah ya ‘ce.’ (Far. 2:16) Ta hanyar wayo, wataƙila Shaiɗan ya yi ƙoƙari ya rage muhimmanci wannan umurnin. Na uku, ko da yake da Hauwa’u yake magana, ya yi amfani da jam’in wakilin sunan nan “ku.” Ta yin hakan, wataƙila ya yi ƙoƙari ya sa ta yi alfahari, ta wajen sa ta ɗauki kanta da muhimmanci, kamar ita ce kakakin kanta da kuma na maigidanta. Da wane sakamako? Hakika, Hauwa’u ta yi fahariya ta wajen yin magana a madadin kanta da kuma maigidanta, ta ce wa macijin: ‘Daga ’ya’ya na itatuwan gona an yarda mana mu ci.’

5. (a) Shaiɗan ya sa Hauwa’u ta mai da hankalinta ga mene ne? (b) Mene ne Hauwa’u ta nuna ta wajen cin ’ya’yan itacen da aka ce kada su ci?

5 Shaiɗan ya kuma murguɗe gaskiyar. Yana nufin cewa bai dace ba da Allah ya dokace Adamu da Hauwa’u cewa kada su ‘ci daga dukan itatuwa na gona.’ Kuma, Shaiɗan ya sa Hauwa’u ta yi tunani game da kanta da kuma yadda za ta iya kyautata rayuwarta don ta zama “kamar Allah.” Daga baya, ya sa ta mai da hankali ga itacen da kuma ’ya’yansa maimakon ga dangantakarta da Wanda ya ba ta kome. (Karanta Farawa 3:6.) Abin baƙin ciki, ta wajen cin ’ya’yan itacen, Hauwa’u ta nuna cewa ba Jehobah ba ne ya fi muhimmanci a rayuwarta ba.

Batun da Ya Taso a Zamanin Ayuba

6. Ta yaya Shaiɗan ya ƙalubalanci amincin Ayuba, kuma wane zarafi ne aka ba wa Ayuba?

6 Ƙarnuka bayan hakan, Ayuba mai aminci ya samu zarafin nuna Wanda ya fi muhimmanci a rayuwarsa. Sa’ad da Jehobah ya gaya wa Shaiɗan cewa Ayuba mai adalci ne, Shaiɗan ya amsa: “A banza ne Ayuba ya ke tsoron Allah?” (Karanta Ayuba 1:7-10.) Shaiɗan bai musunci biyayyar Ayuba ga Allah ba. Maimakon haka, ya zargi muradinsa. Da wayo, ya zargi Ayuba cewa ba ya bauta wa Jehobah saboda ƙauna, amma saboda son kai. Amma Ayuba ne kaɗai zai iya amsa wannan zargin, saboda haka aka ba shi zarafin yin hakan.

7, 8. Waɗanne jarrabobi ne Ayuba ya fuskanta, kuma mene ne ya nuna ta jimrewarsa cikin aminci?

7 Jehobah ya ƙyale Shaiɗan ya haddasa wa Ayuba masifu da yawa, ɗaya bayan ɗaya. (Ayu. 1:12-19) Ta yaya Ayuba ya aikata ga wannan yanayinsa da ya canja? An gaya mana cewa bai “yi zunubi ba, ba ya kuwa saɓi Allah ba.” (Ayu. 1:22) Amma duk da haka, Shaiɗan bai ƙyale ba. Ya kuma yi gunaguni: “Ai, fata a bakin fata, hakika dukan abin da mutum ya ke da shi, ya bayar a bakin ransa.”a (Ayu. 2:4) Shaiɗan ya ce idan Ayuba da kansa ya sha wuya, zai yanki shawara cewa Jehobah bai fi muhimmanci a rayuwarsa ba.

8 Ciwo mai ƙyama da matsi daga matarsa cewa ya la’anta Allah ya mutu ya raunana Ayuba sosai. Daga baya, masu ta’aziyyar ƙarya guda uku suka zarge shi cewa yana mugunta. (Ayu. 2:11-13; 8:2-6; 22:2, 3) Amma, Ayuba ya ci gaba da kasancewa da aminci duk da dukan wahalarsa. (Karanta Ayuba 2:9, 10.) Ta jimrewarsa cikin aminci, ya nuna cewa Jehobah ne ya fi muhimmanci a rayuwarsa. Ayuba ya kuma nuna cewa zai yiwu mutum ajizi ya yi iya ƙoƙarinsa ya amsa zargin ƙarya na Iblis.—Gwada Misalai 27:11.

Amsa Mai Kyau da Yesu Ya Ba Da

9. (a) Ta yaya Shaiɗan ya yi ƙoƙari ya gwada Yesu da abin da yake bukata? (b) Yaya Yesu ya aikata ga wannan gwajin?

9 Ba da daɗewa ba bayan Yesu ya yi baftisma, Shaiɗan ya yi ƙoƙari ya rinjayi Yesu ya biɗi sha’awoyin kansa maimakon ya sa Jehobah ya zama Wanda ya fi muhimmanci a rayuwarsa. Iblis ya jarrabci Yesu sau uku. Da farko, ya yi ƙoƙari ya rinjayi Yesu da abinci, ya ce masa ya mai da duwatsu gurasa. (Mat. 4:2, 3) Yesu ya yi azumi na kwanaki arba’in kuma yana bala’in jin yunwa. Saboda haka, Iblis ya aririce shi ya yi amfani da ƙarfinsa a hanyar da ba ta dace ba don ya ƙosar da kansa. Ta yaya Yesu ya aikata? Ba kamar Hauwa’u ba, Yesu ya mai da hankali ga Kalmar Jehobah kuma ya ƙi jarrabar nan da nan.—Karanta Matta 4:4.

10. Ta yaya Shaiɗan ya gwada Yesu cewa ya dira daga hasumiyar haikali?

10 Shaiɗan ya kuma yi ƙoƙari ya rinjayi Yesu ya nuna son kai. Ya ƙalubalanci Yesu ya dira ƙasa daga hasumiyar haikalin. (Mat. 4:5, 6) Mene ne Shaiɗan ya so ya cim ma? Shaiɗan ya faɗa cewa idan Yesu ya dira kuma bai ji rauni ba, hakan zai nuna cewa shi “Ɗan Allah ne.” Babu shakka, Iblis ya so Yesu ya cika damuwa da sunansa, har ya nuna matsayinsa. Shaiɗan ya san cewa mutum zai iya yin abu saboda fahariya don kada a raina shi. Shaiɗan ya yi amfani da wani nassi yadda bai dace ba, amma Yesu ya nuna cewa yana da cikakken fahimi na Kalmar Jehobah. (Karanta Matta 4:7.) Ta ƙin wannan gwajin, Yesu ya kuma nuna cewa Jehobah ne ya fi muhimmanci a rayuwarsa.

11. Me ya sa Yesu ya ƙi tayin Shaiɗan na dukan mulkokin duniya?

11 A gwajinsa na ƙarshe, Shaiɗan ya nuna wa Yesu dukan mulkokin duniya. (Mat. 4:8, 9) Nan da nan Yesu ya ƙi wannan tayin. Ya ankara cewa karɓar wannan zai nuna cewa ya ƙi ikon mallaka na Jehobah, wato, ikon Allah na Maɗaukaki Duka. (Karanta Matta 4:10.) A dukan waɗannan gwaje-gwaje, Yesu ya amsa Shaiɗan ta wajen yi masa ƙaulin nassosi da suke ɗauke da sunan Jehobah.

12. Wace matsala mai wuya ce Yesu ya fuskanta sa’ad da ya kusan ƙarshen hidimarsa a duniya, kuma mene ne muka koya daga shawarar da ya tsai da?

12 Gab da ƙarshen rayuwarsa a duniya, Yesu ya fuskanci shawara mai wuya da zai tsai da. A shekarun da ya yi hidima gabaki ɗaya, ya nuna cewa yana son ya ba da ransa a matsayin hadaya. (Mat. 20:17-19, 28; Luk 12:50; Yoh. 16:28) Amma dai, Yesu ya san cewa za a yi masa zargin ƙarya, a yi masa hukuncin ƙarya da dokar Yahudawa kuma a kashe shi a matsayin mai saɓo. Waɗannan abubuwan sun dame shi sosai. Ya yi addu’a: “Ya Ubana, idan ya yiwu, ka bar wannan ƙoƙo ya shuɗe mani.” Sai ya ci gaba: “Amma dai, ba nawa nufi za a bi ba, sai naka.” (Mat. 26:39) Hakika, amincin Yesu har mutuwa ya nuna Wanda ya fi muhimmanci a rayuwarsa!

Amsarmu ga Tambayar

13. Waɗanne darussa ne muka koya daga misalin Hauwa’u da Ayuba da kuma Yesu Kristi?

13 Mene ne muka koya? Mun koya daga batun Hauwa’u cewa waɗanda suka faɗa wa sha’awoyin son kai ko kuma girman kai suna nuna cewa ba Jehobah ba ne ya fi muhimmanci a rayuwarsu. Akasin haka, mun koya daga misalin aminci na Ayuba cewa har ajizai za su iya nuna cewa Jehobah ne farko a rayuwarsu ta wajen jimre wa wahala cikin aminci, ko da ba su fahimci ainihin dalilin ba. (Yaƙ. 5:11) Na ƙarshe, misalin Yesu ya koya mana mu yi shirin shan kunya kuma kada mu cika damuwa da matsayinmu. (Ibran. 12:2) Amma ta yaya za mu iya yin amfani da waɗannan darussan?

14, 15. Ta yaya yadda Yesu ya bi da gwaji ya bambanta da na Hauwa’u, kuma ta yaya za mu yi koyi da Yesu? (Ka ba da kalami a kan hoton da ke shafi na 18.)

14 Kada ka ƙyale gwaje-gwaje su sa ka mance da Jehobah. Hauwa’u ta ƙyale hankalinta ya kafu a gwajin da aka yi mata. Ta lura cewa ’ya’yan itacen “yana da kyau domin ci, abin sha’awa ne kuma ga idanu, itacen kuma abin marmari ne domin bada hikima.” (Far. 3:6) Wannan ya saɓa wa yadda Yesu ya bi da gwaje-gwaje uku da ya fuskanta! Bai ƙyale gwajin ya sa ya manta da sakamakon karya dokar Allah ba. Ya mai da hankali ga Kalmar Allah kuma ya yi amfani da sunan Jehobah.

15 Idan muna fuskantar gwaje-gwaje don yin abin da ke ɓata wa Jehobah rai, ya kamata mu mai da hankalinmu ga me? Idan mun mai da hankali ga gwajin, hakan zai sa sha’awa marar kyau ta ƙaru sosai. (Yaƙ. 1:14, 15) Muna bukatar mu ɗauki mataki nan da nan don mu kawar da irin wannan sha’awar, ko da hakan zai yi gaggawa kamar cire wata gaɓa na jikinmu. (Mat. 5:29, 30) Kamar Yesu, muna son mu mai da hankali ga sakamakon ayyukanmu, wato, yadda zai shafi dangantakarmu da Jehobah. Wajibi ne mu tuna da abin da Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki ta ce. Yin hakan ne kawai zai nuna cewa Jehobah ne ya fi muhimmanci a rayuwarmu.

16-18. (a) Mene ne zai iya sa mu sanyin gwiwa? (b) Mene ne zai taimake mu mu jimre da yanayi masu cike da masifu?

16 Kada ka taɓa ƙyale masifun da suka faru maka su sa ka yi fushi da Jehobah. (Mis. 19:3) Masifu suna shafar mutanen Jehobah yayin da muke matso kusa sosai da ƙarshen wannan muguwar duniya. Ba ma bukatar kāriya ta mu’ujiza a wannan lokacin. Duk da haka, kamar Ayuba, za mu iya yin sanyin gwiwa sa’ad da muka rasa ƙaunatattunmu ko kuma muke shan wahala.

17 Ayuba bai fahimci dalilin da ya sa Jehobah ya ƙyale wasu abubuwa su faru ba, kuma hakan zai iya faruwa da mu. Wataƙila mun samu labari cewa wasu ƙaunatattun ’yan’uwa sun mutu sanadin girgizar ƙasa, kamar wanda ya faru a ƙasar Haiti, ko kuma wasu bala’i. Ko kuma mun samu labarin wani ɗan’uwa mai aminci da ya faɗa hannun masu nuna ƙarfi ko kuma ya mutu sanadin hatsari mai tsanani. Ko kuma za mu iya fuskantar wasu yanayi marar kyau ko kuma rashin gaskiya. Baƙin ciki zai iya sa mu yi tunani: ‘Ya Jehobah? Me ya sa wannan ya faru mini? Wane laifi ne na yi?’ (Hab. 1:2, 3) Mene ne zai taimaka mana mu jimre a irin waɗannan lokatan?

18 Muna bukatar mu yi hankali don kada mu ji cewa irin waɗannan aukuwar sun nuna cewa Jehobah ba ya amincewa da mu. Yesu ya nanata wannan gaskiyar sa’ad da yake yin magana a kan masifu biyu da suka faru a zamaninsa. (Karanta Luka 13:1-5.) Masifu da yawa suna faruwa ne saboda ‘sa’a, da kuma tsautsayi.’ (M. Wa. 9:11) Amma ko da mene ne ya jawo matsalar mu, za mu iya jimrewa idan muka mai da hankalinmu ga “Allah na dukan ta’aziyya.” Zai ba mu ƙarfin da muke bukata don mu ci gaba da kasancewa da aminci.—2 Kor. 1:3-6.

19, 20. Mene ne ya taimaki Yesu ya jimre da yanayin cin mutunci, kuma me zai taimaka mana mu yi hakan?

19 Kada ka taɓa mai da hankali ainun ga fahariya da tsoron jin kunya. Halin Yesu na tawali’u ya taimake shi ya ‘wofinta kansa kuma ya ɗauki surar bawa.’ (Filib. 2:5-8) Ya jimre da yanayin cin mutunci da yawa domin ya dogara ga Jehobah. (1 Bit. 2:23, 24) Ta yin hakan, Yesu ya sa Jehobah farko a rayuwarsa, kuma hakan ya sa an ɗaukaka shi zuwa matsayi mai girma. (Filib. 2:9) Yesu ya kuma ƙarfafa almajiransa su yi koyi da halinsa.—Mat. 23:11, 12; Luk 9:26.

20 Wasu gwaje-gwaje ga bangaskiyarmu za su iya sa mu ji kunya a wasu lokatai. Amma duk da haka, ya kamata mu kasance da gaba gaɗi kamar manzo Bulus, wanda ya ce: “Sabili da wannan fa ina shan waɗannan al’amura: duk da haka ban ji kunya ba; gama na san wanda na ba da gaskiya gare shi, na kuwa kawar da shakka yana da iko ya tsare ajiya da na danƙa masa zuwa wacan rana.”—2 Tim. 1:12.

21. Mene ne ƙudurinka duk da cewa mutanen duniya suna son kansu?

21 Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa mutane za su zama “masu-son kansu” a zamaninmu. (2 Tim. 3:2) Shi ya sa mutanen da ba sa ɗaukan Jehobah farko a rayuwarsu suke ko’ina. Kada mu taɓa ƙyale irin wannan ra’ayi na son kai ya shafe mu! Maimakon haka, ko da muna fuskantar gwaji, masifu ko cin mutunci, bari kowannenmu ya ƙuduri aniya ya nuna cewa lallai Jehobah ne ya fi muhimmanci a rayuwarsa!

[Hasiya]

a Wasu masanan Littafi Mai Tsarki suna ji cewa wataƙila wannan furucin “ai, fata a bakin fata” yana nufin cewa Ayuba zai yarda yaransa da dabbobinsa su rasa fatunsu, ko rayukansu, muddin shi bai rasa nasa fata ko rai ba. Wasu kuma suna ji cewa furucin ya nanata cewa mutum zai yarda ya rasa wasu fatu idan ba zai rasa ransa ba. Alal misali, mutum zai iya ɗaga hannu sama don ya kāre naushin da aka kai wa kansa, da hakan, ya rasa fata don ya kāre fatansa. Ko da mene ne ma’anar wannan fasahar magana, babu shakka, yana nufin cewa Ayuba zai yi farin cikin rasa kome muddin bai rasa ransa ba.

Me Za Mu Iya Koya Daga . . .

• yadda Shaiɗan ya ruɗi Hauwa’u?

• yadda Ayuba ya aikata sa’ad da yake shan wahala?

• abin da ya fi muhimmanci ga Yesu?

[Hoton da ke shafi na 17]

Hauwa’u ba ta saka dangantakarta da Jehobah farko a rayuwarta ba

[Hoton da ke shafi na 18]

Yesu ya ƙi gwaje-gwajen Shaiɗan kuma ya mai da hankali ga yin nufin Jehobah

[Hotuna da ke shafi na 20]

Yin wa’azi a tanti zuwa tanti bayan girgizar ƙasa a ƙasar Haiti

Za mu iya dogara ga “Allah na dukan ta’aziyya,” a lokatan wahala

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba