Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 9/1 pp. 8-12
  • Ayuba Mutumi Ne Mai Jimiri Da Aminci

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ayuba Mutumi Ne Mai Jimiri Da Aminci
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Batun Nuna Aminci da Kuma Gwajin Bangaskiya
  • Rashin Fahimi da Kuma Mummunar Shawara
  • Neman Taimako Sa’ad da Muke Fuskantar Tsanani
  • “Ka Yi Aminci”
  • Ayuba Ya Ɗaukaka Sunan Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • “Ba Zan Daina Tsare Mutuncina Ba!”
    Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu
  • “Sa Zuciya ga Yahweh”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Darussa Daga Littafin Ayuba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 9/1 pp. 8-12

Ayuba Mutumi Ne Mai Jimiri Da Aminci

“Ko ka lura da bawana Ayuba? babu mai-kama da shi cikin duniya, kamili ne, mutum mai-adalci, mai tsoron Allah, yana ƙin mugunta.”—AYUBA 1:8.

1, 2. (a) Waɗanne irin bala’i ne suka faɗa wa Ayuba? (b) Ka kwatanta rayuwar Ayuba kafin bala’in ya faɗa masa.

AKWAI wani mutum da ke da kusan kome a duniya, yana da dukiya, ya yi suna, yana da koshin lafiya, da kuma rayuwar iyali mai daɗi. Amma sai bala’i ya faɗa masa sau uku ba tare da ɓata lokaci ba. Cikin dare ɗaya, ya yi hasarar dukiyarsa. Bayan haka, wani irin hadari wanda ba a kowane lokaci yake faruwa ba, ya ɗauke rayukan duka ’ya’yansa. Ba da daɗewa ba, ya kamu da muguwar cuta wadda ta sa ƙuraje masu ciwo suka fito ko’ina a jikinsa. Wataƙila ka fahimci cewa Ayuba ne wannan mutumin, wanda mashahuri ne a cikin littafin Littafi Mai Tsarki da ke ɗauke da sunansa.—Ayuba, sura 1 da na 2.

2 Cikin baƙin ciki ya ce: “Da ma ina kamar yadda ni ke a da, cikin kwanakin baya.” (Ayuba 3:3; 29:2) Sa’ad da bala’i ya faɗa wa mutum, wanene ba zai yi sha’awar ranaku masu daɗi na dā ba? Ayuba ya yi rayuwa mai kyau, kuma an kāre shi daga bala’i. Manyan mutane suna ba shi daraja kuma suna neman shawara a wurinsa. (Ayuba 29:5-11) Yana da arziki, amma yana da ra’ayin da ya dace game da kuɗi. (Ayuba 31:24, 25, 28) Idan ya haɗu da gwauraye da marayu mabukata, yana taimaka musu. (Ayuba 29:12-16) Kuma ya kasance da aminci ga matarsa.—Ayuba 31:1, 9, 11.

3. Menene ra’ayin Jehobah game da Ayuba?

3 Ayuba ya yi rayuwa marar aibi domin ya bauta wa Allah. “Babu mai-kama da shi cikin duniya,” in ji Jehobah, “kamili ne, mutum mai-adalci, mai tsoron Allah, yana ƙin mugunta.” (Ayuba 1:1, 8) Duk da amincin Ayuba, bala’i ya lalata rayuwarsa mai daɗi. Duk abin da ya tara suka halaka, kuma an gwada halinsa mai kyau da azaba, baƙin ciki, da takaici.

4. Me ya sa abin taimako ne mu tattauna jarabar Ayuba?

4 Hakika, ba Ayuba ba ne kaɗai bawan Allah da ya taɓa fuskantar irin wannan bala’in. Yawancin Kiristoci a yau sun taɓa shaida irin waɗannan bala’in. Domin wannan dalilin, akwai tambayoyi biyu da suka cancanci a tattauna: Ta yaya ne tuna jarabtar Ayuba za ta iya taimaka mana sa’ad da muke fuskantar bala’i? Kuma ta yaya ne za ta iya koyar da mu mu ji tausayin waɗanda suke wahala?

Batun Nuna Aminci da Kuma Gwajin Bangaskiya

5. In ji Shaiɗan, me ya sa Ayuba ke bauta wa Allah?

5 Batun Ayuba ya bambanta. Ba da sanin Ayuba ba, Iblis ya ƙalubalanci dalilin da ya sa Ayuba ke bauta wa Allah. Sa’ad da ake wani taro a sama, Jehobah ya jawo hankali ga halayen Ayuba masu kyau, Shaiɗan ya ce: “Ba ka kewaye shi da shinge ba, da shi da gidansa, da dukan abin da ya ke da shi, a kowane sassa?” Da haka, Shaiɗan ya yi da’awar cewa sonkai ne ya sa Ayuba, da kuma dukan bayin Allah suke bauta wa Allah. Shaiɗan ya ce wa Jehobah: “Miƙa hannunka kaɗai yanzu, ka taɓa dukan abin da yake da shi, za ya la’anta ka a fuskarka!”—Ayuba 1:8-11.

6. Wane batu mai muhimmanci ne Shaiɗan ya tayar?

6 Wannan batun yana da muhimmanci. Shaiɗan ya ƙalubalanci yadda Jehobah yake amfani da ikon mallakarsa. Shin zai yiwu Allah ya yi mulkin sararin samaniya cikin ƙauna? Ko kuwa, kamar yadda Shaiɗan ya ce ne, sonkai ne dai zai yi nasara a ƙarshe? Jehobah ya ƙyale Iblis ya gwada Ayuba, domin yana da tabbaci a amincin bawansa. Da haka, Shaiɗan ya sa bala’i ya faɗa wa Ayuba a kai a kai. Sa’ad da Shaiɗan ya faɗi a hare-harensa na farko, ya jefi Ayuba da muguwar cuta. Iblis ya yi hasashen cewa “fata a bakin fata, hakika dukan abin da mutum ya ke da shi, ya bayar a bakin ransa.”—Ayuba 2:4.

7. A waɗanne hanyoyi ne bayin Allah a yau suke fuskantar jarabobi da suka yi kama da na Ayuba?

7 Ko da yake yawancin Kiristoci a yau ba sa shan wahaloli masu yawa kamar Ayuba, wahaloli iri-iri suna faɗa musu. Yawanci suna fuskantar tsanantawa ko kuwa matsaloli daga iyali. Talauci ko kuwa rashin lafiya yana iya jawo bala’i. Wasu sun saɗaukar da rayuwansu domin imaninsu. Hakika, kada mu yi tunanin cewa Shaiɗan ne yake jawo kowace matsalar da muke fuskanta. Wataƙila mu ne muka jawo wa kanmu wasu matsalolin domin kurakuranmu ko wani yanayin da muka gada. (Galatiyawa 6:7) Tsufa da tsarar bala’i suna shafar dukanmu. Littafi Mai Tsarki ya bayyana dalla-dalla cewa a yanzu, Jehobah ba ya kāre bayinsa daga waɗannan masifun ta hanyar mu’ujiza.—Mai-Wa’azi 9:11.

8. Ta yaya ne Shaiɗan zai so ya yi amfani da matsalolin da muke fuskanta?

8 Duk da haka, Shaiɗan yana iya yin amfani da wahalolin da muke fuskanta ya yi wa imaninmu zagon ƙasa. Manzo Bulus ya ce ya fuskanci ‘masuki cikin jikinsa, manzon Shaiɗan’ wanda ya yi ta ‘marinsa.’ (2 Korinthiyawa 12:7) Wataƙila wannan matsala ce ta jiki, kamar ciwon ido, ko kuwa wani abu dabam, Bulus ya fahimci cewa Shaiɗan zai iya yin amfani da matsala da kuma takaicin da yake fuskanta ya sa ya daina farin cikin da kuma aminci. (Misalai 24:10) A yau, Shaiɗan yana iya yin amfani da waɗanda suke cikin iyali, abokan makaranta, ko gwamnatin kama karya su tsananta wa bayin Allah a wasu hanyoyi.

9. Me ya sa bai kamata wahala ko tsanantawa ya zama abin mamaki ba a gare mu?

9 Ta yaya za mu iya fuskantar waɗannan matsalolin kuma mu yi nasara? Ta wajen ɗaukansu a matsayin cewa muna tsayin daka a ƙaunar da muke yi wa Jehobah da kuma biyayyarmu ga ikon mallakarsa. (Yaƙub 1:2-4) Ko da menene sanadin baƙin cikinmu, fahimtar muhimmancin amincinmu ga yin nufin Allah zai taimaka mana mu yi tsayin daka a ruhaniya. Manzo Bitrus ya rubuta wa Kiristoci: “Ƙaunatattu, kada ku ga abin mamaki ne tsanani mai-zafin nan da ke wurinku, wanda ke auko muku domin ya auna ku, sai ka ce wani baƙon al’amari ya same ku.” (1 Bitrus 4:12) Kuma Bulus ya ce: “Dukan waɗanda su ke so su yi rai mai-ibada cikin Kristi Yesu za su sha tsanani.” (2 Timothawus 3:12) Shaiɗan zai ƙalubalanci amincin Shaidun Jehobah, kamar yadda ya yi wa Ayuba. Hakika, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Shaiɗan yana ƙara kai hari a kan mutanen Allah a wannan zamani na ƙarshe.—Ru’ya ta Yohanna 12:9, 17.

Rashin Fahimi da Kuma Mummunar Shawara

10. Wane abu mai ban tausayi ne Ayuba ya fuskanta?

10 Ayuba ya fuskanci wani abu mai ban tausayi, wanda ba ma fatar mu shaida. Bai san dalilin da ya sa matsaloli suka faɗa masa ba. Ayuba cikin kuskure ya kammala cewa “Ubangiji ya bayas, Ubangiji ya karɓa.” (Ayuba 1:21) Wataƙila, Shaiɗan ne yake son ya cusa wa Ayuba ra’ayin cewa Allah ne ya jawo masa waɗannan matsaloli.

11. Ka bayyana yadda Ayuba ya ji game da bala’in da ya faɗa masa.

11 Ayuba ya yi sanyin gwiwa sosai, ko da yake ya ƙi ya la’anta Allah kamar yadda matarsa ta umurce shi. (Ayuba 2:9, 10) Ya ce, ‘mugaye sun fi ni jin daɗi.’ (Ayuba 21:7-9) Ya yi mamaki, ‘me ya sa Allah yake azabtar da ni?’ Akwai wasu lokatai da ya yi fatan ya mutu. Ya ce: “Da fa za ka yarda ka ɓoye ni cikin Lahira, ka ɓoye ni har lokacinda fushinka ya wuce!”—Ayuba 14:13.

12, 13. Ta yaya ne furcin da abokan Ayuba su uku suka yi ya shafe shi?

12 Ayuba yana da abokai guda uku da suka ziyarce shi don “su yi masa kuka, su ta’azantadda shi.” (Ayuba 2:11) Maimakon haka, sun zama “masu-ta’aziya na ban takaici.” (Ayuba 16:2) Ya kamata Ayuba ya amfana daga abokansa waɗanda ya kamata su rage masa nauyin wahalolinsa, amma waɗannan abokan sun daɗa riƙitar da Ayuba kuma sun ƙara masa takaici.—Ayuba 19:2; 26:2.

13 Wataƙila Ayuba ya tambayi kansa: ‘Me ya sa waɗannan abubuwan suka same ni? Me na yi da na cancanci waɗannan bala’in?’ Abokansa sun ba da amsoshin da ba gaskiya ba ne. Sun yi hasashen cewa Ayuba ne ya jawo wa kansa wahala domin ya yi mugun zunubi. “Marar-laifi ya taɓa lalacewa?” in ji Eliphaz. “Bisa ga ganina dai masu-kabtun mugunta, da masu-shibka ƙeta, su kan girbe abin da sun aika.”—Ayuba 4:7, 8.

14. Me ya sa bai kamata a ce mutum na wahala ne don dabi’a marar kyau?

14 Babu shakka, matsaloli na iya tasowa idan muka shuka abubuwa na jiki maimakon na ruhu. (Galatiyawa 6:7, 8) Duk da haka, a wannan zamanin, matsala na iya tasowa ko da wane irin hali ne muke da shi. Bugu da ƙari, ba za a iya cewa marasa laifi ba sa fuskantar bala’i ba. Yesu Kristi, “marar-ƙazamta, [wanda] raɓaɓɓe ne da masu-zunubi,” ya mutu a kan gungumen azaba, kuma manzo Yakubu ya mutu domin imaninsa. (Ibraniyawa 7:26; Ayukan Manzanni 12:1, 2) Tunani marar kyau na Eliphaz da abokansa biyu ya motsa Ayuba ya kāre sunansa mai kyau ya kuma dage a kan rashin laifinsa. Duk da haka, zargin da suka yi cewa Ayuba ya cancanci wahalar da yake sha, wataƙila shi ne ya canja ra’ayinsa game da adalcin Allah.—Ayuba 34:5; 35:2.

Neman Taimako Sa’ad da Muke Fuskantar Tsanani

15. Wane irin tunani ne zai taimaka mana sa’ad da muke fuskantar wahala?

15 Akwai darassin da za mu koya daga wannan? Muna iya ganin cewa masifu, rashin lafiya, ko tsanantawa abubuwa ne da ba su dace ba. Wasu mutane ba sa fuskantar yawancin irin waɗannan matsalolin. (Zabura 73:3-12) A wasu lokatai, muna bukatar mu yi wa kanmu waɗannan muhimman tambayoyi: ‘Ƙaunar da na ke yi wa Allah za ta motsa ni in bauta masa ko da menene zai faru? Ina son in ba Jehobah damar “mayarda magana ga wanda ya zarge [shi]?” ’ (Misalai 27:11; Matta 22:37) Kada mu ƙyale maganganun banza da wasu suke yi ya sa mu yi shakkar Ubanmu na samaniya. Wata Kirista mai aminci wadda ta fuskanci mugun rashin lafiya na shekaru da yawa ta ce: “Na sani cewa duk abin da Jehobah ya ƙyale, zan iya jimre shi. Na sani zai ba ni ƙarfin da nike bukata. Kuma ya sha yin haka.”

16. Ta yaya ne Kalmar Allah ta taimaka wa waɗanda suke fuskantar matsaloli?

16 Game da dabarun Shaiɗan kuwa, muna da fahimin da Ayuba ba shi da ita. “Ba mu cikin rashin sanin makiɗansa,” ko mugun dabarunsa. (2 Korinthiyawa 2:11) Bugu da ƙari, muna da isashen hikima wanda zai taimaka mana. A cikin Littafi Mai Tsarki, akwai labarun maza da mata masu aminci waɗanda suka jimre wa ire-iren wahaloli. Manzo Bulus wanda ya sha wahala fiye da yawancin Kiristoci ya rubuta: “Iyakar abin da aka rubuta a dā aka rubuta su domin koyarwarmu, domin ta wurin haƙuri da ta’aziyar litattafai mu zama da bege.” (Romawa 15:4) Wani Mashaidi da ke ƙasar Turai wanda aka jefa a kurkuku a lokacin yaƙin duniya na biyu domin imaninsa, ya yi musanyar abincinsa na kwana uku da Littafi Mai Tsarki. Ya ce, “Wannan musanyar ta kasance mai amfani! Duk da yunwar da nike ji, na sami abinci na ruhaniya da ya kiyaye ni da kuma wasu a waɗannan lokatai na wahala. Na ajiye wannan Littafi Mai Tsarki har yau.”

17. Waɗanne tanadi ne daga Allah zai iya taimaka mana mu jimre?

17 Ban da ta’aziyyar da muke samu daga Nassosi, muna da littattafai na Littafi Mai Tsarki masu yawa da suke yi mana ja-gora don jimre wa matsalolinmu. Idan ka duba littafin nan Watch Tower Publications Index, babu shakka, za ka ga labarin ɗan’uwa Kirista wanda ya taɓa fuskantar irin matsalar da kake fuskanta. (1 Bitrus 5:9) Za ka iya samun taimako idan ka tattauna yanayinka da dattawa masu juyayi ko wasu ƙwararrun Kiristoci. Fiye da komi, ta hanyar addu’a, kana iya samun taimako daga Jehobah da kuma ruhunsa mai tsarki. Ta yaya ne Bulus ya tsayayya wa ‘marin’ Shaiɗan? Ta wajen dogara ga ikon Allah. (2 Korinthiyawa 12:9, 10) Ya rubuta: “Na iya yin abu duka a cikin wannan da ya ke ƙarfafata.”—Filibbiyawa 4:13.

18. Ta yaya ne ’yan’uwa Kiristoci suke ba da ƙarfafa?

18 Saboda haka, za ka iya samun taimako, kuma kada ka yi jinkirin nemansa. “Idan ka yi suwu cikin ranar ƙunci, ƙarfinka kaɗanna ne,” in ji misalai. (Misalai 24:10) Kamar yadda gāra za ta iya sa gidan da aka yi da katako ya rushe, hakazalika, sanyin gwiwa zai iya yi wa amincinmu na Kirista zagon ƙasa. Don mu kawar da wannan haɗarin, Jehobah ya yi mana tanadin taimako ta hanyar ’yan’uwanmu bayin Allah. Wani mala’ika ya bayyana ga Yesu kuma ya ƙarfafa shi a daren da aka kama shi. (Luka 22:43) A kan hanyarsa ta zuwa Roma a matsayinsa na fursuna, Bulus “ya yi ma Allah godiya, ransa ya ƙarfafa,” sa’ad da ya haɗu da ’yan’uwa a Kasuwar Abiyus da Rumfa Uku. (Ayukan Manzanni 28:15) Wata Mashaidiya ’yar Jamus ta tuna irin taimakon da ta samu sa’ad da ta isa sansanin fursuna da ke Ravensbrück a matsayinta na matashiya da ke shakka. Ta ce, “Wata ’yar’uwa Kirista ta gan ni kuma ta yi mini maraba.” “Wata ’yar’uwa kuma ta kula da ni sosai, kuma ta zama kamar uwata ta ruhaniya.”

“Ka Yi Aminci”

19. Menene ya taimaka wa Ayuba ya tsayayya wa ƙoƙarce-ƙoƙarcen Shaiɗan?

19 Jehobah ya kwatanta Ayuba a matsayin mutum “mai-adilci.” (Ayuba 2:3) Duk da cewa ya yi sanyin gwiwa kuma bai fahimci dalilin da ya sa yake wahala ba, Ayuba bai taɓa jijjiga a kan batun aminci ba. Ayuba ya ƙi ya musanta duka abubuwan da ya yi rayuwa a kansu. Ya ce: “Har in mutu ba ni rabuwa da gaskiyata.”—Ayuba 27:5.

20. Me ya sa jimiri na da muhimmanci?

20 Irin wannan ƙudurin zai taimaka mana mu kasance da aminci a ƙarƙashin kowane irin yanayi, wato sa’ad da muke fuskantar gwaji, hamayya, ko wahala. Yesu ya gaya wa ikilisiyar da ke Samiruna: “Kada ka ji tsoron wahala da za ka sha: ga shi, Shaiɗan yana shiri ya jefa waɗansu daga cikinku a kurkuku, domin a gwada ku; [wahala, baƙin ciki, ko zalunci] kwana goma kuwa za ku sha ƙunci. Ka yi aminci har mutuwa, ni ma in ba ka rawanin rai.”—Ru’ya ta Yohanna 2:10.

21, 22. Wane sani ne zai iya ƙarfafa mu sa’ad da muka fuskanci ƙunci?

21 A wannan zamanin wanda Shaiɗan ne ke sarauta, za a gwada jimirinmu da amincinmu. Duk da haka, Yesu ya ba mu tabbacin cewa yayin da muke duba gaba, ba mu da wani dalili na jin tsoro. Abu mafi muhimmanci shi ne mu kasance da aminci. “Ƙuncinmu . . . na lokaci kaɗan,” ne in ji manzo Bulus, amma “daraja” ko kuwa sakamakon da Jehobah ya yi mana alkawarinsa, “madawwami gaba gaba ƙwarai” ne. (2 Korinthiyawa 4:17, 18) Ƙuncin da Ayuba ya fuskanta na ɗan lokaci ne idan aka haɗa da shekarun da ya mora kafin da kuma bayan gwajinsa.—Ayuba 42:16.

22 Duk da haka, wataƙila akwai wasu lokatai a rayuwarmu da za mu ga kamar gwajin ba su da iyaka, kuma kamar ba za mu iya jimre wa wahalar da muke sha ba. A talifi na gaba, za mu tattauna yadda labarin Ayuba zai iya koya mana ƙarin darussa game da jimiri. Za mu kuma duba hanyoyin da za mu iya taimaka wa waɗanda suke fuskantar wahala.

Yaya Za Ka Amsa?

• Wane batu mai muhimmanci ne Shaiɗan ya tayar game da amincin Ayuba?

• Me ya sa bai kamata wahala ya kasance abin mamaki ba?

• Ta yaya ne Jehobah yake taimaka mana mu jimre?

[Hotuna a shafi na 11]

Yin bincike, tattaunawa da ƙwararrun Kiristoci, da kuma faɗin abin da ke cikin zuciyarmu a addu’a za su iya taimaka mana mu jimre

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba