Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 3/15 pp. 20-23
  • Kada Ka Yasar da ’Yan’uwanka Masu Bi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kada Ka Yasar da ’Yan’uwanka Masu Bi
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Hakkinmu ga ’Yan’uwa Masu Bi
  • Alhini na Rayuwa Ya Nauyaya Su
  • Kimantawa da Ya Yi Daidai
  • Ta Yaya ‘Za Ka Sa Hanyarka ta Yi Nasara’?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • “Ku Yi Ta Gina Juna”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Za Ka Iya Taimaka wa ‘Yan’uwa a Ikilisiyarku?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Ka Kusaci Jehobah da Kuma ’Yan’uwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 3/15 pp. 20-23

Kada Ka Yasar da ’Yan’uwanka Masu Bi

“A CIKIN shekaru goma, kasuwanci na duniya ya janye hankalinmu sosai, kuma muna more ɗan wadata. Ko da yake an yi renonmu a cikin gaskiya, mun daina bauta wa Jehobah kuma mun ji cewa ba mu da ƙarfin dawowa,” in ji Jarosław da matarsa, Beata.a

Wani ɗan’uwa, Marek, ya tuna: “Saboda canje-canje na zaman jama’a da na siyasa a ƙasar Poland, na yi hasarar aiki ɗaya bayan ɗaya. Na yi sanyin gwiwa. Ina tsoron soma nawa kamfani domin ban iya kasuwanci ba. A ƙarshe na soma kamfani na, ina tunanin cewa wannan zai taimaka mini na biya bukatun iyalina da kyau ba tare da mugun sakamako ga ruhaniya ta ba. Da shigewar lokaci, na ga cewa ba zai kasance hakan ba.”

A duniya inda abubuwa suke daɗa tsada kuma rashin aiki yana ƙaruwa, wasu mutane sun daɗa kasance da alhini kuma a sakamakon haka sun tsai da shawarwari da ba su dace ba. ’Yan’uwa da yawa sun tsai da shawara su yi aiki bayan lokaci, sun karɓi ƙarin aiki, ko kuma sun soma nasu kasuwanci ko idan ba su iya kasuwanci ba. Suna ganin cewa ƙarin kuɗi zai taimaka wa iyalin kuma ba zai shafi dangantakarsu da Jehobah ba. Duk da haka sa’a da tsautsayi da kuma tattalin arziki da ke canjawa suna iya ɓata shiri da aka yi da nufin kirki. A sakamako, wasu sun faɗa cikin tarkon haɗama kuma sun ƙyale biɗe-biɗen dukiya ya shafi hidimarsu ga Jehobah.—M. Wa. 9:11, 12.

Wasu ’yan’uwa maza da mata sun shaƙu cikin biɗe-biɗen duniya da har ba su da lokacin nazari na kansu da halartar tarurruka ko kuma hidima. A bayane yake cewa hakan yana shafan ruhaniyarsu da kuma dangantakarsu da Jehobah. Suna iya yasar da wata dangantaka mai muhimmanci, wato, gaminsu da waɗanda “suke cikin iyalin imani” da su. (Gal. 6:10) Wasu suna janyewa daga ’yan’uwanci na Kirista a hankali. Ka yi la’akari sosai da fannin wannan batun.

Hakkinmu ga ’Yan’uwa Masu Bi

A matsayin ’yan’uwa maza da mata, muna da lokatai da yawa na nuna ƙauna ga juna. (Rom. 13:8) A cikin ikilisiyarku, wataƙila ka ga ‘talakawa da suke kuka’ don taimako. (Ayu. 29:12) Wasu suna iya rasa abin biyan bukata masu muhimmanci. Manzo Yohanna ya tuna mana zarafin da wannan yake kawowa. “Wanda ya ke da dukiyar duniya, yana kuwa ganin ɗan’uwansa da tsiya, ya hana masa tausayi, ƙaƙa ƙaunar allah tana zaune a cikinsa?”—1 Yoh. 3:17.

Mai yiwuwa ka biya irin waɗannan bukatu kuma ka taimaki wasu sosai. Amma, son ’yau’uwanci ba kawai ba da taimako na zahiri ba. Wasu suna iya neman taimako domin sun kaɗaita ko sun yi sanyin gwiwa. Suna iya jin ba su cancanci bauta wa Jehobah ba ko suna shan wahala daga rashin lafiya mai tsanani ko kuma sun yi rashin wani wanda suke ƙauna. Hanya ɗaya da za mu iya ƙarfafa su ita ce ta wajen saurara da kuma yin magana tare da su, da hakan za mu iya kula da bukatunsu na sosuwar zuciya da na ruhaniya. (1 Tas. 5:14) Hakan sau da yawa na ƙarfafa gamin ƙauna da ’yan’uwanmu.

Dattawa da ke cikin ikilisiya musamman suna da matsayi na saurarawa cikin juyayi, su nuna fahimi, kuma su ba da gargaɗi na nassi cikin ƙauna. (A. M. 20:28) Ta wannan hanyar, masu kula suna koyi da manzo Bulus, wanda yake ‘marmari da kuma ƙaunar’ ’yan’uwansa maza da mata na ruhaniya.—1 Tas. 2:7, 8.

Amma, idan Kirista ya bijire daga garken, mene ne zai faru ga hakkinsa ga ’yan’uwansa masu bi? Masu kula ma suna fuskantar gwajin biɗan abubuwan duniya. Idan Kirista ya faɗa wa irin wannan gwajin kuma fa?

Alhini na Rayuwa Ya Nauyaya Su

Kamar yadda aka ambata, yin aiki tuƙuru don mu biya bukatun iyalinmu sau da yawa na kawo alhini kuma zai iya raunana yadda muke ɗaukan ƙa’idodi na Kirista. (Mat. 13:22) Marek, da aka ambata ɗazu, ya bayyana: “Sa’ad da ba na samun ci gaba a kasuwanci na, sai na tsai da shawara na nemi aiki mai kyau a wata ƙasa. Na tafi yin aiki na watanni uku, sai na sake yi na watanni uku, kuma hakan ya ci gaba, ina dawo gida na ɗan lokaci. Matata da ba mai bi ba ce ta sha wahalar sosuwar zuciya don hakan.”

Ba rayuwar iyali ta kawai ba ce ta sha wahala. Marek ya ci gaba. “Ban da yin aiki na dogon lokaci a zafin rana, ina tare da mugayen mutane da suke ƙoƙari su cuci wasu. Suna aikatawa kamar ’yan daba. Na yi baƙin ciki kuma an mallake ni. Da yake ba ni da lokacin kula da kaina, sai na soma shakkar iyawa ta na yi wa mutane hidima.”

Mummunan sakamako na shawarwarin Marek ya kamata ya motsa mu mu yi tunani. Ko idan zuwa wata ƙasa zai magance matsalar rashin kuɗi, zai kawo wasu matsaloli. Alal misali, mene ne zai faru ga zaman lafiya na ruhaniya da sosuwar zuciya na iyalinmu? Shin irin wannan ƙaura zai sa mu yanke zumunci da ikilisiya? Ba zai hana mu yi wa ’yan’uwanmu masu bi hidima ba?—1 Tim. 3:2-5.

Amma, yadda wataƙila ka gano, ba sai mutum ya yi aiki a wata ƙasa ba kafin ya shaƙu a aikin karɓan albashi ba. Ka yi la’akari da Jarosław da Beata. “Hakan ya soma ba da saninmu ba,” in ji shi. “A matsayin amarya da ango, mun buɗe kantin cin abinci a wuri mai kyau. Tun da yake muna samun riba sosai, muka tsai da shawara mu faɗaɗa kasuwancinmu. Amma ba mu da isashen lokaci, saboda haka ba ma zuwan taron Kirista a kai a kai. Ba da daɗewa ba, na daina hidimar majagaba da kuma hidima a matsayin bawa mai hidima. Da yake muna farin ciki game da riba da muke samu, muka buɗe babban kanti kuma muka soma tarayya da wanda ba mai bi ba. Ba da daɗewa ba, na soma tafiya ƙasar waje don na karɓi kwangilar miliyoyin daloli. Ba na zaman gida, kuma gamin da ke tsakani na da iyalina ya soma taɓarɓarewa. A ƙarshe, mun shaƙu sosai da kasuwancinmu da ke kawo mana riba da a hankali mun daina bauta wa Jehobah. Tun da yake ba ma cuɗanya da ikilisiya, ba ma tunani ma game da ’yan’uwanmu.”

Wane darasi za mu iya koya daga wannan? Ƙoƙarin samun abin duniya zai iya rinjayar Kirista, ya sa ya gamsu da kansa, har ya yi hasarar “tufafinsa,” wato halinsa na Kirista. (R. Yoh. 16:15) Hakan zai sa mu yanke zumunci da ’yan’uwa da za mu iya taimaka musu a dā.

Kimantawa da Ya Yi Daidai

Muna iya yin tunani, ‘Hakan ba zai faru da ni ba.’ Duk da haka, ya kamata kowannenmu ya yi tunanin ainihin abin da ake bukata a rayuwa. Bulus ya rubuta, “Ba mu shigo da kome cikin duniya ba, ba kuwa za mu iya fita cikinta da kome ba; amma da ya ke muna da abinci da sutura, da su za mu yi wadar zuci.” (1 Tim. 6:7, 8) Hakika, yanayin rayuwa ya bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa. Abin da za a ɗauka ba shi da tsada a ƙasar da ta bunƙasa zai iya zama alatu a ƙasashe da yawa.

Ko yaya yanayin rayuwa yake a inda muke da zama, ka yi la’akari da kalaman Bulus na gaba: “Waɗanda suna so su zama mawadata su kan fāɗa cikin jaraba da tarko da sha’awoyi dayawa na wauta da ɓarna, irin da kan dulmaya mutane cikin hallaka da lalacewa.” (1 Tim. 6:9) Ana ɓoye tarko daga abin da ake son a kama. An ƙera shi yadda zai kama abu farat ɗaya. Ta yaya za mu kāre kanmu don kada ‘sha’awoyi da ke ɓarna’ su kama mu?

Idan muka tsara abubuwa da suka fi muhimmanci, hakan zai motsa mu mu nemi ƙarin lokaci don bauta wa Jehobah, har da yin nazari na kanmu. Irin wannan nazari tare da addu’a yana iya taimaka wa Kirista ya “zama kamili, shiryayye sarai” don ya taimaka wa mutane.—2 Tim. 2:15; 3:17.

Da shigewar wasu shekaru, dattawa masu ƙauna sun yi ƙoƙari su gina da kuma ƙarfafa Jarosław. Hakan ya sa ya yi canje-canje sosai. Ya ce: “A wani tattaunawa mai muhimmanci da suka yi, dattawa suka yi ƙaulin misali na Nassi na saurayi mai arziki wanda yake son ya yi rayuwa har abada amma ba ya shirye ya bar dukiyoyinsa. Da basira suka tambaye shi abin da ya koya daga wannan bayanin. Wannan ya taimake ni na fahimci inda nake bukata na yi gyara!”—Mis. 11:28; Mar. 10:17-22.

Jarosław ya yi tunani sosai a kan yanayinsa kuma ya tsai da shawara ya daina sa hannu a manyan kasuwanci. Cikin shekara biyu, da shi da iyalinsa suka sake ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah. Yanzu yana yi wa ’yan’uwansa hidima a matsayin dattijo. Jarosław ya ce: “Sa’ad da ’yan’uwa suka shaƙu cikin kasuwanci har suka yi banza da ruhaniyarsu, ina amfani da misali na na kwatanta yadda ba abin hikima ba ce mutum ya yi cuɗanya da bai dace ba da marasa bangaskiya. Ba shi da sauƙi mutum ya ƙi zarafin samun abin duniya kuma ya guji ayyukan rashin gaskiya.”—2 Kor. 6:14.

Marek shi ma ya koyi darasi ta hanya mai wuya. Ko da yake aikin da ya yi a ƙasar waje ya taimake shi ya samu kuɗin biyan bukatun iyalinsa, amma dangantakarsa da Allah da kuma ’yan’uwansa ta sha wuya. Da shigewar lokaci, ya sake bincika abubuwa da suka fi muhimmanci a gare shi. “Shekaru da yawa, yanayina ya yi kama da na Baruch na zamanin dā wanda ya ci gaba ‘da biɗa wa kansa manyan abu.’ A ƙarshe, na gaya wa Jehobah dukan alhini na, kuma yanzu ina jin na sake samun ruhaniyata.” (Irm. 45:1-5) Marek yanzu yana burin biɗan “nagarin aiki” na mai kula a cikin ikilisiya.—1 Tim. 3:1.

Marek ya ba waɗanda suke tunanin tafiyar ƙasar waje domin su nemi aikin da ake samun kuɗi sosai wannan shawara: “Sa’ad mutum yake ƙasar waje, yana da sauƙi ya faɗa cikin tarkunan wannan muguwar duniya. Rashin sanin yaren wurin yana hana tattaunawa da mutane. Kana iya komawa gida da kuɗi, amma kana da raunuka na ruhaniya da zai daɗe kafin ka warke.”

Kasancewa da daidaita tsakanin aiki da hakkinmu ga ’yan’uwanmu zai taimaka mana mu faranta wa Jehobah rai. Kuma zai iya ba da misali da zai iya motsa wasu su tsai da shawara mai kyau. Waɗanda suka yi sanyin gwiwa suna bukatar tallafawa da juyayi da misali mai kyau na ’yan’uwansu maza da mata. Dattawan ikilisiya da wasu mutane da suka manyanta za su iya taimaka wa ’yan’uwa masu bi su kasance da daidaita kuma su guji damuwa ainun game da alhini na rayuwa.—Ibran. 13:7.

Hakika, kada mu taɓa yasar da ’yan’uwanmu masu bi ta wajen taƙurewa a aikin samun kuɗi. (Filib. 1:10) Maimakon haka, bari mu zama ‘mawadata ga Allah,’ yayin da muke saka al’amura na Mulki farko a rayuwarmu.—Luk 12:21.

[Hasiya]

a An canja wasu sunayen.

[Hotuna da ke shari na 21]

Shin aikinka yana hana ka halartar taro kuwa?

[Hotuna da ke shari na 23]

Kana daraja zarafin da kake da shi na taimaka wa ’yan’uwanka na ruhaniya?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba