Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 4/1 pp. 30-31
  • Ka Kāre Bauta ta Gaskiya!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Kāre Bauta ta Gaskiya!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Makamantan Littattafai
  • Allah Mai Ƙyamar Rashin Adalci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Halakar Saduma Da Gwamarata
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Yesu ya Warkar da Mutane ta Hanyar Mu’ujiza
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Yesu Ya Sa Masu Sauraransa Sun Yi Mamaki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 4/1 pp. 30-31

Don Matasa

Ka Kāre Bauta ta Gaskiya!

Umurni: Ka yi wannan aikin a inda babu surutu. Sa’ad da kake karanta nassosin, ka sa kanka cikin yanayin. Ka yi tunanin yanayin a zuciyarka. Ka ji muryoyin mutanen. Ka ji yadda ainihin mutanen da ke ciki suka ji. Ka sa labarin ya kasance kamar yanzu yake faruwa.

Shimfiɗar ’yan wasa: Iliya, Ahab, da waɗansu annabawan Baal su 450

Taƙaitawa: Iliya ya nuna cewa Jehobah ya fi ƙarfin Baal.

1 KA YI TUNANI A KAN YANAYIN NAN.—KARANTA 1 SARAKUNA 18:17-40.

Ka zana hoto a kan fallen takarda da ke nuna inda kake tunanin cewa Iliya yake, tare da annabawan Baal, da bagadan.

Waɗanne ƙara ne kake “ji” sa’ad da ake hayaniyar da aka kwatanta a ayoyi 26 zuwa 29?

․․․․․

A ganinka, yaya Iliya ya ji sa’ad da yake yi wa annabawan Baal magana?

․․․․․

2 KA YI BINCIKE SOSAI.

Me ya sa Iliya yake bukatar gaba gaɗi don zuwa wajen Ahab kuma bayan haka ya je ya yi gwajin da ya wulakanta ɗarurruwan annabawan Baal? (Ƙarin haske: Karanta 1 Sarakuna 18:4, 13, 14.)

․․․․․

Ka yi amfani da littattafan bincike da kake da su don yin bincike game da bautar Baal. Alal misali, waɗanne abubuwa ne suke yi sa’ad da suke bautarsu? Ta yaya bautar Baal ta shafi Isra’ila?

․․․․․

Me, kake tsammani, ya sa Iliya ya sa aka tona rami kewaye da bagadin Jehobah kuma aka cika shi da ruwa?

․․․․․

3 KA YI AMFANI DA ABIN DA KA KOYA. KA RUBUTA ABIN DA KA KOYA GAME DA . . .

Gaba gaɗin da ake bukata don a kāre bauta ta gaskiya.

․․․․․

Albarkar da waɗanda suka nuna irin wannan gaba gaɗin za su samu.

․․․․․

DON ƘARIN AMFANI.

A waɗanne wuri ko wurare na rayuwa ne za ka iya nuna ƙarin gaba gaɗi wajen kāre bauta ta gaskiya?

․․․․․

4 WANE ƁANGAREN WANNAN LABARIN NE YA FI MA’ANA A GARE KA, KUMA ME YA SA?

․․․․․

Ka ƙara koya game da Littafi Mai Tsarki, a duniyar gizon www.watchtower.org DA www.jw.org

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba