Ka Kusaci Allah
“Za Ka Yi Marmari”
ABIN baƙin ciki ne ƙwarai ka ga wanda kake ƙauna yana shan wahala har ya mutu. Irin wannan rashin yana sa mu baƙin ciki sosai. Sanin cewa Mahaliccinmu, Jehobah Allah, yana sane da baƙin cikinmu zai ƙarfafamu. Fiye da haka, yana ɗokin yin amfani da ikonsa na maɗaukaki don ya ta da matattu. Ka lura da irin begen da aka bayyana a kalmomin Ayuba, a Ayuba 14:13-15.
Ka yi la’akari da yanayin. Ayuba, mutumi ne wanda bangaskiyarsa ta yi fice, ya fuskanci jarraba masu tsananin gaske, waɗanda suka haɗa da asarar dukiyoyinsa, mutuwar dukan ’ya’yansa da yake ƙauna, da kuma mugun rashin lafiya. A cikin wannan azabar, ya yi kira ga Allah: “Da fa za ka yarda ka ɓoye ni cikin Lahira [kabari]!” (Aya 13) Ayuba ya ɗauki shiga kabari a matsayin ƙarshen shan wahala. A wurin, kamar dukiyar da Allah ya ɓoye, ba zai ƙara shan wahala da azaba ba.a
Ayuba zai ci gaba da kasancewa a kabari ne har abada? Ayuba ya gaskata cewa hakan ba zai faru ba. Ya ci gaba da addu’arsa: “Da . . . ka sanya mini rana, sa’annan ka tuna da ni!” Ayuba ya gaskata cewa zamansa a kabari na ɗan lokaci ne kawai kuma Jehobah ba zai manta da shi ba. Ayuba ya kamanta lokacin da zai yi a cikin kabari da [“aikin dole,” NW] wato, lokacin jira na dole. Har yaushe? “Har a karɓe ni in huta,” in ji shi. (Aya 14) Wannan hutawar tana nufin fitowa daga kabari, wato, tashin matattu!
Me ya sa Ayuba yake da tabbaci cewa zai samu wannan hutun? Domin ya san yadda Mahaliccinmu mai ƙauna yake ji game da masu bauta masa da aminci da suka mutu. Ayuba ya ce: “Za ka yi kira, ni ma in amsa maka: Za ka yi marmarin aikin hannuwanka.” (Aya 15) Ayuba ya yarda cewa Allah ne ya halicce shi. Wanda ke ba da rai kuma ya tsara Ayuba a cikin mahaifa, babu shakka zai iya ta da shi bayan ya mutu.—Ayuba 10:8, 9; 31:15.
Kalmomin Ayuba sun koya mana cewa Jehobah mai ƙauna ne: Kamar yadda Ayuba ya yi, Jehobah yana ƙaunar waɗanda suka miƙa kansu ga hannunsa, waɗanda suke ƙyale shi ya mulmula su su zama mutane masu daraja a idanunsa. (Ishaya 64:8) Jehobah yana ɗaukan bayinsa masu aminci da tamani. Ga masu aminci da suka mutu, yana da “marmari.” Kalmar Ibrananci da aka fassara “babu shakka tana ɗaya daga cikin kalmomi mafi ƙarfi sosai da ake amfani da su wajen nuna ɗoki,” in ji wani masani. Hakika, Jehobah yana tunawa da masu bauta masa kuma yana ɗokin ta da su daga matattu.
Abin godiya, a littafin Ayuba, wato, ɗaya daga cikin littattafai na farko na Littafi Mai Tsarki da aka rubuta, Jehobah ya bayyana nufinsa na ta da matattu.b Yana son ka sake haɗuwa da ƙaunatattunka da suka mutu. Wannan tunanin zai iya sa jimrewa da rashin ya kasance da sauƙi. Me zai hana ka ƙara koya game da wannan Allah mai ƙauna da kuma yadda za ka sa ya mulmula ka ka zama irin mutumin da zai ga cikawar nufinsa?
[Hasiya]
a Wani littafin bincike ya ce furucin Ayuba, “ka ɓoye ni,” yana iya nufin “ka kwantar da ni a ɓoye a matsayin ajiya mai tamani.” Wata majiya dabam ta ce waɗannan kalmomin suna nufin “ka ɓoye ni a matsayin dukiya.”
b Don ka ƙara koya game da alkawarin da ke cikin Littafi Mai Tsarki game da ta da matattu don su rayu a sabuwar duniya mai adalci, ka duba babi na 7 na littafin nan Menene Littafi Mai Tsarki Ainihi Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.