Wasiƙa Daga Mexico
“Jehobah Yana Ƙaunarmu Kuwa Duk da Cewa Muna Zaune Ne a Ƙauyukan da ke Nesa?”
MELESIO, wanda ke yin yaren mutanen O’dam, yana saukowa daga saman tsaunuka a loto-loto don neman aikin yi. Ya halarci taron Kirista kuma ya ɗauki littattafan da suke bayyana Littafi Mai Tsarki don ya ba mutanensa. Ya roƙi Kiristocin ko wani zai iya ziyartarsu daga cikinsu kuma ya koya musu Littafi Mai Tsarki.
Mutanen O’dam, waɗanda wata ƙabila ce da ke ware daga sauran mutane, suna da zama a tsaunukan Sierras a tsakiyar arewacin Mexico, wadda take da nisan mil 150 (kilomita 240) daga ikilisiyar Shaidun Jehobah mafi kusa. Wasu daga cikinmu sun yanke shawarar mu ziyarce su.
Sai muka samo motar a-kori-kura, tanti, da jakunkunan yin barci, muka ɗauki isashen abinci da māi da za mu yi amfani da shi cikin kwanaki uku, sai muka kama hanya daga birnin Durango. Tun daga ƙarfe huɗu na asuba, sai da muka yi tafiyar awa takwas a kan wata hanya mai ƙura da ke kan tudu zuwa inda hanyar ta ƙare. Wannan ita ce mashigin yankin mutanen O’dam. A gabanmu akwai wani kwazazzabo mai zurfi da wani tsauni.
Mun bar a-kori-kurar a wani ƙauye da ke ware, kuma muka yi tafiyar awa uku da kafa, muka kai kayanmu zuwa gidin kwazazzabon. A nan ne muka yā da zango, muka tara itacen hura wuta don mu kori namun daji, wasu daga cikin mu suna yin barcin awa uku kuma su tashi don su karɓi waɗanda suke hura wutar domin su ma su kwanta su yi barcin awa uku.
Washegari da safe, muka soma hawan tudun. Akwai hanyoyi da yawa, kuma mun ɓace sau da yawa. Wani daga cikinmu yana jin yaren O’dam kaɗan, saboda haka, mun sanar da saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki a gidajen da ke kan hanya. Mun yi mamaki sa’ad da mutane suka gaya mana cewa a Los Arenales, inda muka nufa, akwai wasu da suke kiran kansu Shaidun Jehobah kuma suna yin taron nazarin Littafi Mai Tsarki a wurin. Wannan labari ne mai ban mamaki da ƙarfin gwiwa.
Kafafuwanmu sun riga sun kumbure sa’ad da muka isa Los Arenales. Al’ummar tana da gidajen soro da aka yi jinkansu da yankakkun kwalaye masu ƙwari, babu makaranta ko wutar lantarki. Mutanen suna ware ne daga sauran al’ummai, cikin mugun talauci, kuma ainihin abincin da suke ci shi ne burodin da aka yi da garin masara da kuma wasu ƙananan abinci. Mun haɗu da Melesio, wani saurayi siriri wanda ya yi matuƙar farin ciki da ganinmu. Ya gayyace mu zuwa gidansa kuma ya gaya mana cewa yana addu’a a kowace rana cewa Jehobah ya aiko da Shaidunsa su zo su koyar da Littafi Mai Tsarki ga iyalinsa da ’yan’uwansa mutanen O’dam. Domin ya kasa amsa dukan tambayoyin da suka yi masa.
Mutanen O’dam suna bin wani addini mai suna shamanism. Suna amfani da ƙasusuwan gaggafa da gashinta a matsayin asiri, suna bauta wa ruwa da iska mai ƙarfi, da sauransu, kuma suna jin tsoron shama, waɗanda suke ci da guminsu. Melesio ya bayyana cewa sa’ad da ya koyi cewa Jehobah ne Allah na gaskiya a tafiye-tafiyensa zuwa birni, ya halaka dukan abubuwan da yake amfani da su wajen bauta wa gumaka. Al’ummar tana sa rai cewa allolinsu za su kashe shi. Sa’ad da hakan bai faru ba, sai mutanen suka gane cewa Jehobah ya fi ƙarfin allolinsu. A sakamakon haka, sai suka soma halartar nazarin Littafi Mai Tsarki da Melesio yake yi da iyalinsa, inda yake amfani da littattafanmu.
“Na gaya musu cewa suna bukatar su ƙone dukan layunsu da gumakansu,” in ji Melesio. Mutane da yawa sun ɗauki wannan matakin, kuma adadin waɗanda suke halartar taro ya fi mutane 80. Mun yi mamaki da muka ji haka, sai muka yanke shawarar yin taro da rana. Muka aika saƙo ta hanyar masinjoji a kan doki zuwa ga waɗanda suke zuwa taro a kai a kai a gidan Melesio. Ko da yake tsakiyar mako ne kuma an yi sanarwar a cikin ƙurarren lokaci, mutane 25 ne suka hallara, sun tako ne a ƙasa wasu kuma sun zo a kan jaki.
Yayin da Malesio yake fassara abin da muka ce, mun amsa tambayoyin da mutanen suka yi daga Littafi Mai Tsarki. Sun yi tambayoyi kamar: “Jehobah yana ƙaunarmu kuwa duk da cewa muna zaune ne a ƙauyukan da ke nesa?” “Yana jin addu’o’in da ake furtawa a harshen O’dam?” “Sa’ad da Armageddon ya zo, Jehobah zai san da zamanmu duk da cewa muna zaune ne nesa da birane?” Mun yi farin cikin tabbatar wa waɗannan mutane masu tawali’u daga Littafi Mai Tsarki cewa Jehobah yana kula da masu tawali’u, kome yarensu da kaɗaicinsu. Sun roƙe mu mu aiko wani don ya ƙara koyar da su.
Bayan taron, mun raba abincinmu da waɗannan sababbin abokan da muka yi. Dare ya riga ya yi, kuma ana sanyi sosai a wannan tsaunin, mun yi farin ciki sosai sa’ad da suka ba mu gidan da ake kan ginawa don mu kwana a ciki. Washegari da safe sun raka mu kuma suka bi da mu wani yanke zuwa inda a-kori-kurarmu take, kuma muka koma Durango, agajiye amma cike da gamsuwa.
Gata ne mai girma mu sadu da waɗannan mutane masu son gaskiya, waɗanda ba su da littattafan da suka bayyana Littafi Mai Tsarki a yaren da za su iya karantawa amma suna so su koyi gaskiya game da Allah kuma su bauta masa! Tun lokacin da muka ziyarce su, Shaidu guda shida sun je yankin, kuma sun yi makonni uku a wurin. Sun ba da taimako na ruhaniya ga mutane wajen 45 waɗanda suke so su bauta wa Jehobah da gaske. Dukansu suna halartar taro a kai a kai.
Kafin mu mance. An daina sayar da taba sigari a ƙaramin kanti guda ɗaya tak da ke Los Arenales. Dalilin shi ne, mutane da yawa suna nazarin Littafi Mai Tsarki kuma sun daina shan taba. Kuma mutanen sun je sun yi wa aurensu takarda don ya kasance bisa doka.
[Hoton da ke shafi na 28]
Melesio da matarsa, ’ya’ya huɗu mata, da surukarsa
[Hotuna da ke shari na 29]
Nazarin Littafi Mai Tsarki da taron Kirista a Los Arenales
[Inda Aka Ɗauko Hoto shafi na 29]
Servicio Postal Mexicano, Correos de Mexico