Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 1/15 pp. 31-32
  • Ka Yi Bimbini a Kan Abin da Jehobah Ya Yi Maka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Bimbini a Kan Abin da Jehobah Ya Yi Maka
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ta Yaya Alkawarin da Ba a Cika ba Yake Shafan Mu?
  • Abin da Jehobah Ya Riga Ya Yi
  • Darussa Daga Kwanaki 40 na Ƙarshe da Yesu Ya Yi a Duniya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • An Ta da Yesu Daga Matattu!
    Littafi Mai Tsarki​—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?
  • Domin Kristi Aka Yi Annabce-annabce
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ku Koyar Da ’Yan’uwa Maza Su Yi Burin Aikin Kula
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 1/15 pp. 31-32

Ka Yi Bimbini a Kan Abin da Jehobah Ya Yi Maka

BA DA daɗewa ba bayan Yesu ya tashi daga matattu, almajiransa biyu suna tafiya daga Urushalima zuwa Imwasu. “Ananan suna cikin zance” in ji Linjilar Luka, “Yesu da kansa ya kusance su, ya tafi tare da su. Amma idanunsu a kame su ke da ba za su sansance shi ba.” Sai Yesu ya ce musu: “Wane irin zance ke nan ku ke yi da juna, kuna cikin tafiya, da fuskoki a ƙwantsare?” Me ya sa suke baƙin ciki? Almajiran suna sa rai cewa Yesu zai ceci Isra’ila a lokacin daga hannun ’Yan Al’ummai, amma bai yi hakan ba. Maimakon haka, aka kashe Yesu. Hakan ne ya sa suke baƙin ciki.—Luk 24:15-21; A. M. 1:6.

Yesu ya soma tattaunawa da almajiran. “Ya soma kuwa tun daga Musa da dukan annabawa, cikin dukan littattafai yana fasalta musu al’amura na bisa kansa.” Hakika, abubuwa da yawa na musamman da ke ƙarfafa bangaskiya sun faru a lokacin hidimar Yesu! Yayin da almajiran suka saurari bayanin Yesu, halinsu ya canja daga baƙin ciki zuwa farin ciki. Daga baya, da yamman nan, suka ce: “Zuciyarmu ba ta yi ƙuna daga cikinmu ba, sa’anda yake yi mamu zance a kan hanya, yana bayyana mamu littattafai?” (Luk 24:27, 32) Mene ne za mu iya koya daga yadda almajiran Yesu suka aikata?

Ta Yaya Alkawarin da Ba a Cika ba Yake Shafan Mu?

Almajiran biyu da suke kan hanyar Imwasu sun yi baƙin ciki saboda abin da suke sa rai cewa zai faru bai kasance hakan ba. Sun fuskanci abin da aka kwatanta a Misalai 13:12: “Muradin da ba a biya ba ya kan sa zuciya ta yi ciwo.” Hakazalika, wasu cikinmu, da suke bauta wa Jehobah da aminci cikin shekaru da yawa, sun yi zato cewa ya kamata a ce an riga an gama “ƙunci mai-girma.” (Mat. 24:21; R. Yoh. 7:14) Daidai ne mutum ya yi baƙin ciki na ɗan lokaci saboda abin da yake zato da bai faru ba.

Ku tuna cewa waɗannan almajirai biyu sun sake samun farin cikinsu bayan da Yesu ya taimaka musu su mai da hankali ga annabce-annabcen da sun riga sun auku, har na zamaninsu. Hakan nan ma, za mu iya kasancewa da farin ciki kuma mu jimre da fid da zuciya. Wani dattijo Kirista mai suna Michael da ya manyanta ya ce: “Kada ka mai da hankali ga abin da Jehobah bai riga ya yi ba tukun. Maimakon hakan, ka mai da hankali ga abin da ya riga ya yi.” Hakika, wannan shawara mai kyau ce!

Abin da Jehobah Ya Riga Ya Yi

Ka yi la’akari da wasu abubuwa na musamman da Jehobah ya riga ya cim ma. Yesu ya ce: “Wanda ya bada gaskiya gareni, ayyukan da na ke yi shi kuma zai yi; ayyuka kuma waɗanda sun ɗara waɗannan zai yi.” (Yoh. 14:12) A yau, bayin Allah sun cim ma ayyukan Kirista mafi girma. Fiye da mutane miliyan bakwai suna ɗokin tsira daga babban ƙunci. Ka yi tunani, fiye da dā amintattun bayin Jehobah sun kasance da ƙwazo a dukan duniya! Jehobah ya sa kalaman annabcin Yesu game da “ayyuka kuma waɗanda sun ɗara waɗannan” su kasance da gaske.

Mene ne kuma Jehobah ya yi mana? Ya yi wa mutane masu zuciyar kirki tanadin fita daga muguwar duniya, a alamance, zuwa aljanna ta ruhaniya da ya yi tanadinsa. (2 Kor. 12:1-4) Ka ɗauki lokaci ka yi tunani a kan wasu fasaloli na aljannar da muke morewa. Alal misali, ka kalli cikin laburari ɗin littattafanka ko kuma wanda ke cikin Majami’ar Mulki. Ka buɗe littafin nan Watch Tower Publications Index, ko kuma ka bincika Watchtower Library. Ka saurari wasan kwaikwayo na Littafi Mai Tsarki wanda aka ɗauka a faifai. Ka sake tunawa da yadda taron gunduma da ka halarta kwanakin baya ya kasance. Ƙari ga haka, ka yi tunani a kan cuɗanya mai kyau da muke morewa da ’yan’uwanmu Kiristoci maza da mata. Jehobah yana karimci sosai wajen yi mana tanadin abinci na ruhaniya mai yawa da ’yan’uwanci na ƙauna, hakika wannan aljanna ta ruhaniya ce!

Dauda marubucin wannan Zabura ya ce: “Ya Ubangiji Allahna, ayyuka masu-ban al’ajabi, waɗanda ka yi, suna dayawa, duk da tunaninka waɗanda sun nufo wajenmu.” (Zab. 40:5) Hakika, ta yin tunani a kan abubuwa masu ban al’ajabi da Jehobah ya riga ya yi mana kuma yin bimbini a kan ƙauna da yake mana, za mu samu ƙarfi don jimrewa cikin aminci a hidimar da muke yi da dukan zuciyarmu ga Ubanmu na samaniya, Jehobah.—Mat. 24:13.

[Hoton da ke shafi na 31]

Yesu ya taimaki almajiransa su yi tunani a kan abin da Jehobah ya riga ya yi musu

[Hotuna da ke shari na 32]

Ka sake tunawa da yadda taron gunduma da ka halarta kwanakin baya ya kasance

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba