Ina Farin Cikin Bauta Wa Jehobah, Har A Lokatan Gwaje-gwaje
Maatje De Jonge-van Den Heuvel ce ta ba da labarin
NI ’YAR shekara 98 ce. Na yi farin cikin bauta wa Jehobah na shekara 70, kuma na fuskanci gwaje-gwaje ga bangaskiya ta. A lokacin Yaƙin Duniya na biyu, an saka ni cikin kurkuku, inda baƙin ciki ya sa na yanki wata shawara da ta sa na yi da na sani. ’Yan shekaru bayan hakan, na fuskanci wata gwaji mai wuya. Duk da haka, ina wa Jehobah godiya don na samu gatar bauta masa, har a lokatan gwaje-gwaje.
Rayuwata ta canja a watan Oktoba na shekara ta 1940. Ina da zama a garin Hilversum, wanda ke da nisan mil 15 daga kudu matso gabashin birnin Amsterdam a ƙasar Holan. Ƙasar tana ƙarƙashin sarautar Nazi. Ni da Jaap de Jonge, miji mai kula sosai mun yi aure na shekara biyar, kuma muna da ’ya mai shekara uku mai suna Willy. Muna zama kusa da wata iyali da ta talauce sosai wadda take famar ciyar da yara takwas. Duk da haka, sun yi wa wani baƙo matashi tanadin masauƙi da abinci. ‘Me ya sa suka ɗauki wannan ƙarin nauyin?’ Na yi mamaki. Sa’ad da na kai musu abinci, na samu labari cewa matashin majagaba ne. Ya tattauna da ni game da Mulkin Allah da kuma albarkar da zai kawo. Abin da ya tattauna da ni ya motsa ni sosai, kuma na karɓi gaskiya nan da nan. A wannan shekarar, na keɓe kaina ga Jehobah kuma aka yi mini baftisma. Miji na ma ya karɓi gaskiya, shekara ɗaya bayan da na yi baftisma.
Ko da yake ban da ilimin Littafi Mai Tsarki sosai, amma na fahimci cewa ta wurin zama Mashaidiya, ina cikin ƙungiyar da aka hana aikinta. Na kuma san cewa an riga an saka Shaidu da yawa cikin kurkuku don wa’azin saƙon Mulki da suke yi. Duk da haka, nan da nan na soma wa’azi gida zuwa gida, kuma ni da mijina mun ƙyale majagaba da masu kula masu ziyara su riƙa zama a gidanmu. Gidanmu ya kuma zama ma’adanar littattafai da suke bayyana Littafi Mai Tsarki, wanda ’yan’uwa maza da mata suke kawo mana daga birnin Amsterdam. Suna ɗaukan littattafan da babur kuma su rufe shi da tamfal. ’Yan’uwa da suke kawo littattafan suna da ƙauna da gaba gaɗi sosai! Suna sa rayuwarsu a kasada don ’yan’uwansu.—1 Yoh. 3:16.
“Inna, Za Ki Dawo da Wuri?”
Kusan watanni shida bayan da na yi baftisma, ’yan sanda uku sun zo gidanmu. Sai suka shiga ciki suna bincike. Ko da yake ba su ga kabad da ke cike da littattafai ba, amma sun ga wasu littattafai a ƙarƙashin gadonmu. Nan da nan suka ce na bi su zuwa ofishin ’yan sanda da ke birnin Hilversum. Sa’ad da na rungumi ’ya ta don na ce mata sai an jima, sai Willy ta tambaye ni, “Inna, za ki dawo da wuri?” Na ce, “E, Zan dawo gida da wuri.” Amma dai, zan yi watanni goma sha takwas masu wuya sosai kafin na sake riƙe ’ya ta.
Wani hafsan ɗan sanda ya kai ni Amsterdam don su yi mini tambayoyi. Sun nemi su sa na gaya musu inda ’yan’uwa uku Shaidun Jehobah da ke birnin Hilversum suke. Na ce: “Ban san su ba, sai dai ɗaya. Shi ne ke kawo mana madara.” Kuma hakan gaskiya ne, ɗan’uwan yana sayar da madara. Sai na daɗa, “Amma shi ne kawai zai iya amsa ko shi Mashaidin Jehobah ne.” Sa’ad da na ƙi na faɗa kome, suka mare ni kuma suka kulle ni, inda suka bar ni na tsawon watanni biyu. Sa’ad da mijina ya gano inda nike, ya kawo mini wasu tufafi da abinci. A watan Agusta na shekara ta 1941, aka kai ni wani mugun sansani da ake ajiye mata, wato, Ravensbrück, wanda ke da nisar mil 50 daga arewancin Berlin, a ƙasar Jamus.
“Ki Yi Fara’a, Ƙawa Ta”
Sa’ad da muka kai wurin, aka gaya mana cewa za a ƙyale mu mu koma gida inda mun sa hannu a takarda cewa ba za mu ci gaba da zama shaidu ba. Amma na ƙi sa hannu a takardar. Maimakon hakan, na ba su kayayyakin da na zo da su kuma na tuɓe tufafi na a gidan wanka, inda na haɗu da ’yan’uwa mata Kiristoci daga ƙasar Holan. Sai aka ba mu tufafin kurkuku mai ɗauke da bajo mai ruwan albasa da kwano da kofi da cokali. A dare na farko, ana saka mu a cikin wani sansani na ɗan lokaci. Na yi kuka na farko tun da aka tsare ni. Mene ne zai faru? “Har yaushe zan kasance a nan?” Na yi kuka da shassheƙa. Gaskiyar ita ce, dangantaka ta da Jehobah ba ta da ƙarfi sosai, tun da yake ban daɗe da karɓan gaskiya ba. Ina da abubuwa da yawa da zan koya. Washegari sa’ad da ake kiran sunaye, wata ’yar’uwa daga Dutch ta lura da baƙin ciki na. Ta ce: “Ki yi fara’a, ƙawa ta, ki yi fara’a! Mene ne zai same mu?”
Bayan an kira sunayen, aka kai mu wani bariki, inda ɗimbin ’yan’uwa mata Kiristoci daga ƙasar Jamus da Holan suka marabce mu. Wasu ’yan’uwa mata daga ƙasar Jamus sun riga sun zauna a bariki fiye da shekara ɗaya. Ganinsu da na yi ya ƙarfafa ni, kuma na yi fara’a. Na kuma yi farin cikin ganin cewa barikin da ’yan’uwanmu mata suke zama ya fi sauran barikin tsabta. Ban da tsabtarsa, an kuma san barikinmu kamar wurin da ba a sata, zage-zage, ko kuma faɗace-faɗace. Akasin mugun yanayin da muke fuskanta a sansanin, barikinmu yana kamar tsibiri mai tsabta wanda teku mai dauda ta kewaye ta.
Rayuwar Yau da Kullum a Sansani
Rayuwa a sansani ya haɗa da yin aiki sosai da kuma cin abinci kaɗan. Muna tashi da ƙarfe biyar na safe, kuma bayan hakan sai a soma kiran sunaye. Masu gadin suna sa mu tsaya a waje kusan sa’a ɗaya, ko ana rana ko kuma ruwan sama. Da ƙarfe biyar na yamma, bayan mun gama aiki mai wuya, sai a sake kiran sunayen. Sai mu ci burodi da miya kuma mu shiga barci cike da gajiya.
Kowanne rana ban da ranar Lahadi, ana sa na yi aiki a gonaki, inda nake yankan alkama da lauje, share ramuka da ake zuba ruwa a ciki, da kuma share gidajen aladu. Ko da yake aikin yana da wuya da kuma datti, amma ina yinsa kullum tun da ni matashiya ce kuma ina da sauran ƙarfi. Kuma ina ƙarfafa kaina ta rera waƙoƙin Mulki yayin da nake aiki. Amma dai, kullum ina kewar mijina da ’yata.
Ana ba mu abinci ɗan kaɗan, amma dukanmu ’yan’uwa mata muna ajiye yankin burodi guda kullum don mu samu abinci da yawa ranar Lahadi da muke samun zarafin kasancewa tare don tattauna jigon Littafi Mai Tsarki. Ba mu da littattafai da suke bayyana Littafi Mai Tsarki, amma ina sauraron ’yan’uwa mata daga ƙasar Jamus da suka manyanta yayin da suke tattauna Littafi Mai Tsarki. Mukan yi taro na Tuna da Mutuwar Kristi.
Wahala, Nadama, da Ƙarfafawa
A wasu lokatai, ana ce mu yi wasu ayyuka da ke tallafa wa yaƙin Nazi. Domin tsakatsakinmu a batutuwan siyasa, dukan ’yan’uwa mata sun ƙi yin wannan aikin, kuma ni ma na bi misalinsu na gaba gaɗi. A sakamako, an hana mu abinci kwanaki da yawa kuma muna kasancewa a tsaye na sa’o’i da yawa sa’ad da ake kiran sunaye. A lokacin wani ɗari, an rufe mu na kwanaki arba’in a cikin bariki ba tare da abin ɗumama ɗaki ba.
A matsayin Shaidun Jehobah, an gaya mana sau da yawa cewa za a ƙyale mu mu tafi gida idan mun ƙi imaninmu. Bayan na zauna a sansanin Ravensbrück fiye da shekara guda, na yi sanyin gwiwa sosai. Na yi sha’awar ganin mijina da ’ya ta sosai har na je wajen masu gadin, na ce su ba ni fam ɗin da ya ce na ƙi imani ta, kuma na sa hannu.
Sa’ad da ’yan’uwa matan suka ji abin da na yi, wasu suka soma guje mini. Amma dai, ’yan’uwa mata biyu tsofaffi ’yan ƙasar Jamus masu suna Hedwig da Gertrud sun neme ni kuma suka ƙarfafa ni cewa suna ƙauna ta sosai. Sa’ad da muke aiki tare a gidan aladun, sun bayyana mini muhimmancin kasancewa da aminci ga Jehobah da kuma yadda muke ƙaunarsa ta ƙin rabuwa da gaskiyarmu. Kulawarsu da kirkinsu ya taɓa zuciya ta sosai.a Na san cewa abin da na yi ba shi da kyau, kuma na so a soke sa hannu da na yi. Wata rana da yamma na gaya wa wata ’yar’uwa game da shawara da na yanke na soke sa hannun da na yi. Wataƙila wani hafsa ya ji tattaunawar da muka yi, domin a yammar, an sako ni daga sansani kuma aka komar da ni ƙasar Holan da jirgin ƙasa. Wata shugaba da ke wurin, da har yanzu ina tunawa da fuskarta ta ce mini, “Har yanzu ke ’yar Bibelforscher ce (Ɗaliban Littafi Mai Tsarki), kuma za ki ci gaba da kasancewa hakan.” Na amsa, “Hakika, zan ci gaba da kasancewa hakan da nufin Jehobah.” Duk da haka, na ci gaba da tunani, ‘Ta yaya zan soke wannan sa hannu da na yi?’
Wani furcin da ke cikin takardar shi ne: “Na tabbatar cewa ba zan taɓa yin tarayya da Ƙungiyar Ɗaliban Littafi Mai Tsarki na Dukan Duniya kuma ba.” Na san abin da zan yi! A watan Janairu na shekara ta 1943, ba da daɗewa ba bayan na kai gida, na kuma soma aikin wa’azi. Hakika, da a ce ’yan Nazi sun sake kama ni ina wa’azi game da Mulkin Allah, da sun tsananta mini sosai.
Don na nuna cewa ina so na kasance da aminci ga Jehobah, ni da mijina mun kuma buɗe gidanmu don masu kula masu ziyara da masu kawo littattafai su riƙa zama. Ina farin ciki matuƙa don wani zarafi da na samu na nuna cewa ina ƙaunar Jehobah da mutanensa!
Yanayi na Baƙin Ciki
’Yan shekaru kafin a daina yaƙin, maigidana da ni mun fuskanci yanayi na baƙin ciki. A watan Oktoba na shekara ta 1944, nan da na ’yarmu ta yi ciwo. Willy tana da ciwon maƙogwaro mai tsanani. Yanayinta ya taɓarɓare da sauri, kuma ta rasu bayan kwanaki uku. Tana da shekara bakwai kawai.
Rashin ’yarmu ya jawo mana baƙin ciki sosai. A gaske, gwaje-gwajen da na fuskanta a sansanin Ravensbrück bai kai baƙin cikin da na yi ba sa’ad da ’yarmu ta rasu ba. Amma dai, a lokatan wahala, muna samun ƙarfafa daga kalaman da ke Zabura 16:8 “Na sa Ubangiji a gabana kullum: Da shi ke yana ga hannun damana ba zan jijjigu ba.” Mijina da ni muna da bege ga alkawarin Jehobah na tashin matattu. Mun nace wa gaskiya kuma mun yi wa’azin bishara da ƙwazo. Har lokacin da mijina ya rasu a shekara ta 1969, ya taimaka mini na bauta wa Jehobah da farin ciki.
Albarka da Farin Ciki
A shekaru da yawa kafin lokacin, abin da yake kawo mana farin ciki shi ne kasancewa kusa da masu hidima ta cikakken lokaci. Kamar yadda yake a lokacin yaƙin, muna barin masu kula masu ziyara da matansu su zauna a gidanmu sa’ad da suke ziyarar ikilisiyarmu. Wasu ma’aurata masu kula masu ziyara, Maarten da Nel Kaptein, sun zauna a gidanmu na tsawon shekaru sha uku! Sa’ad da Nel ta yi ciwo mai tsanani, na samu zarafin kula da ita a gidanta na tsawon watanni uku kafin ta rasu. Yin tarayya da su da kuma ’yan’uwa maza da mata na ikilisiyar ta taimaka mini na more aljanna ta ruhaniya da muke ciki yanzu.
Wani abu mai muhimmanci a rayuwa ta ya faru a shekara ta 1995, sa’ad da aka gayyace ni zuwa wani taro da aka yi a sansanin Ravensbrück. A wajen na sadu da ’yan’uwa mata da muka zauna tare da su a sansanin, waɗanda mun yi shekara hamsin ba mu ga juna ba! Kasancewa tare da su lokaci ne da ba zan taɓa mantawa ba kuma zarafin ƙarfafa juna ne don yin begen lokacin da ƙaunatattu da suka mutu za su sake rayuwa kuma.
Manzo Bulus ya ambata a Romawa 15:4 cewa “ta wurin haƙuri da ta’aziyar littattafai mu zama da bege.” Ina godiya ga Jehobah don wannan begen da ya ba da, wanda ya taimaka mini na bauta masa da farin ciki, duk da gwaje-gwaje.
[Hasiya]
a A lokacin da ba ma samun saƙo daga hedkwata, ’yan’uwa suna bi da batu game da tsakatsaki iya ƙarfinsu. Hakan ya nuna dalilin da ya sa ’yar’uwa da ke sansanin ta aikata hakan da Maatje.
[Hoton da ke shafi na 10]
Tare da Jaap, a shekara ta 1930
[Hoton da ke shafi na 10]
’Yarmu Willy, sa’ad da take ’yar shekara bakwai
[Hoton da ke shafi na 12]
A shekara ta 1995, na halarci wani taro da muka sadu da ’yan’uwa da yawa. Ni ce a layin farko, mutum na biyu daga hannun hagu