Ga Sunan a Cikin Kwari
ST. MORITZ. Ka taɓa jin sunan nan kuwa? Wataƙila, domin wurin shaƙatawa ne da aka fi sani a Kwarin Engadine a ƙasar Switzerland. Amma St. Moritz wuri ne da yake jawo hankalin mutane sosai don kwarinta mai kyau sosai da ke cikin Tudun Alps a kudu maso gabas na ƙasar Switzerland kusa da iyakar ƙasar Italiya. Akwai wuri mai suna Swiss National Park, inda furanni da dabbobi dabam dabam masu kyau suke yaba wa Mahaliccinmu Mai Girma, Jehobah. (Zab. 148:7-10) Hakan ma yake da al’adun da ake yi tun tsakiyar ƙarni na goma sha bakwai.
Abubuwa da ke gidaje da yawa a kwarin nan za su jawo hankalinka sosai. Har yanzu akwai sunan Allah a gaban gidaje, kamar a ainihin ƙofar gidan. A ƙarnuka da suka wuce, a kan yi zane-zane a wajen gidaje, ko da fanti, ko a yi zane ta wurin kankare filasta ɗin, ko a yi zane a dutse. Za ka iya ganin hoton wani gida a ƙauyen Bever. Fassarar abin da aka rubuta ita ce: “An gina gidan a shekara ta 1715. Jehobah ne farko da kuma ƙarshe. Da ikon Allah za a iya cim ma kome, ban da shi ba za a iya cim ma kome ba.” Hakika, wannan alama ta zamanin dā tana ɗauke da sunan Allah.
Za ma ka iya ganin zane da ya fi daɗewa a ƙauyen Madulain. Zanen ya ce: “Zabura 127. Idan ba [Jehobah] ya gina gidan ba, Banza magina su ke aiki. Lucius Rumedius. A shekara ta 1654.”
Me ya sa aka rubuta sunan Allah a wurare da yawa a wannan kwarin? A zamanin da ake yin gyare-gyare, an buga Littafi Mai Tsarki na Romansh, wato, yaren Latin da ake yi a Engadine. Hakika, littafi na farko da aka taɓa fassarawa a yaren kenan. Abin da mutanen ƙauyen suka karanta daga Kalmar Allah ya motsa su su rubuta sunansu da kuma ƙauli na Littafi Mai Tsarki wanda ya haɗa da sunan Allah.
Hakika, har a yau, waɗannan zane-zanen, suna shelar sunan Jehobah da kuma yaba masa, ƙarnuka da yawa bayan an rubuta su a gidaje. Ana marabtar baƙi da mazauna wannan kwarin su daɗa saninsu game da Allah mai girma, Jehobah, ta ziyarar wani ginin da ke ɗauke da sunansa, wato, Majami’ar Mulki ta Shaidun Jehobah a garin Bever.
[Inda Aka Ɗauko Hoto shafi na 7]
© Stähli Rolf A/age fotostock