Na Ga Ikon Gaskiyar Littafi Mai Tsarki
Vito Fraese ne ya ba da labarin
WATAƘILA, ba ka taɓa jin sunan nan Trentinara ba. Wani ƙaramin gari ne a kudancin Naples, a ƙasar Italiya. A can aka haifi iyayena da wana Angelo. Bayan da aka haifi Angelo, sai iyayena suka ƙaura zuwa ƙasar Amirka kuma suka yi zama a birnin Rochester, a New York, kuma a wurin ne aka haife ni a shekara ta 1926. A shekara ta 1922 ne mahaifi na ya fara saduwa da Ɗaliban Littafi Mai Tsarki da aka san da su da Shaidun Jehobah a yau. Ba da daɗewa ba, shi da Mahaifiyata suka zama Ɗaliban Littafi Mai Tsarki.
Mahaifina natsattse ne, mai tunani, kuma ba ya son rashin adalci. Bai iya jimre wa yadda limamai suke sa mutane su kasance cikin jahilci ba, kuma ba ya barin zarafin yaɗa koyarwar Littafi Mai Tsarki ya wuce shi. Da ya yi murabus, ya soma hidima ta cikakken lokaci kuma ya nace a yin hidimar har sa’ad da rashin lafiya da kuma ɗari suka tilasta masa ya daina hidima a lokacin da yake shekara 74. Duk da haka, ya ci gaba da yin wa’azi yana samun sa’o’i 40 ko 60 a wata har ya kai shekarunsa na 90. Misalin mahaifina ya shafe ni sosai. Ko da yake yana da ban dariya, amma bai da wasa. Yakan ce, “Dole ne a ɗauki gaskiya da muhimmanci.”
Baba da Mama sun yi ƙoƙari su koya wa dukanmu yara biyar Kalmar Allah. Na yi baftisma a ranar 23 ga Agusta a shekara ta 1943, kuma a watan Yuni na shekara ta 1944 na zama majagaba. Yata Carmela majagaba ce a birnin Geneva, New York, da Fern abokiyar hidimarta mai fara’a. Bai daɗe ba na gane cewa Fern yarinya ce da zan yi duk rayuwata da ita. Saboda haka, a watan Agusta a shekara ta 1946 muka yi aure.
Hidima a Wata Ƙasa
Mun yi hidimarmu ta farko da ta biyu a matsayin majagaba na musamman a birnin Geneva da Norwich, New York. A watan Agusta na shekara ta 1948, mun samu gatar halartar aji na 12 na makarantar Giliyad. Sai aika tura mu hidima a birnin Naples da ke Italiya da wasu ma’aurata Carl da Joanne Ridgeway masu hidima a wata ƙasa. A lokacin, birnin Naples yana fama ya farfaɗo daga ɓarna da yaƙi ya yi a wajen. Yana da wuya a samu gida, saboda haka mun zauna a ƙananan ɗakuna biyu na wasu watanni.
Na yi girma ina jin iyayena suna yaren Naples, amma mutane sun fahimci yaren Italiya da nake yi duk da cewa ina magana ne kamar Ba’amirke. Ya yi wa Fern wuya ta koyi yaren. Amma daga baya ta koyi yaren har ta zo ta fi ni yinsa.
Da farko, wata iyali mai mutane huɗu kaɗai ne da suke son saƙon muka samu a birnin Naples. Suna sayar da tabar sigari da gwamnati ta hana shiga ƙasa. A kowace rana, wata a cikin wannan iyalin, mai suna Teresa, tana canjawa. Da safe sai ta cika sigari a cikin aljihu na siket ɗin ta, sai hakan ya sa ta kiɓa. Da yamma kuma, sai ta zama siririya kamar kara. Gaskiya ta canja wannan iyalin gabaki ɗaya. Daga baya, mutane 16 cikin wannan iyalin sun zama Shaidu. Yanzu a birnin Naples, akwai Shaidu kusan 3,700.
Hamayya ga Aikinmu
Bayan da muka yi wata tara kaɗai a birnin Naples, sai hukuma ta tilasta wa mu huɗun mu bar birnin. Sai muka tafi ƙasar Switzerland na wata guda, muka dawo Italiya da takardar biza na masu yawon shaƙatawa. Aka tura ni da Fern zuwa birin Turin. Da farko, wata budurwa ta ba mu hayar ɗaki guda, kuma muna amfani da gidan wanka da kuma kicin ɗin ta. Sa’ad da ma’aurata Carl da Joanne Ridgeway suka isa Turin, muka yi hayar babban gida tare. Da shigewar lokaci, mu ma’aurata biyar da muke hidima a wata ƙasa muka zauna a wannan gidan tare.
A shekara ta 1955, sa’ad da hukuma ta sa muka bar birnin Turin, an riga an kafa tushen sababbin ikilisiyoyi guda huɗu. Yanzu akwai ’yan’uwa a yankin da suka ƙware da za su iya kula da waɗannan ikilisiyoyin. Hukumar ta ce mana, “Muna da tabbaci cewa muddin ku ’yan Amirka kun tafi, za a mance da dukan abubuwa da kuka cim ma.” Amma, ƙaruwa da aka samu ya nuna cewa nasara ga aikin ya dangana ga Allah. A yau, akwai fiye da Shaidu 4,600 da ikilisiyoyi 56 a birnin Turin.
Florence, Birni Ne Mai Ban Al’ajabi
Wani birni da aka tura mu shi ne Florence. Sau da yawa muna ji game da wannan birnin, yayata Carmela da mijinta Merlin Hartzler sun yi hidima a wannan birnin. Duk da haka, ka yi tunanin zama a wurare masu ban al’ajabi kamar su Piazza della Signoria da Ponte Vecchio da Piazzale Michelangelo, da kuma Palazzo Pitti da suke birnin Florence. Abin farin ciki ne a ga yadda mutanen Florence suka aikata ga bishara.
Mun yi nazari da wata iyali, kuma iyayen suka yi baftisma. Amma, magidancin mai shan taba ne. A shekara ta 1973, Hasumiyar Tsaro ta nuna cewa shan taba mummunan hali ne kuma ta aririce masu karatu su daina yin hakan. Yaransa da suka yi girma suka roƙe shi ya daina. Ya yi alkawari zai yi hakan, amma bai daina ba. Wata rana da yamma matarsa ta gaya wa tagwayensu masu shekara tara su je su kwanta su kaɗai kafin ta yi addu’a da suke yi kafin su yi barci. Daga baya sai ta ji wani iri kuma ta tafi ɗakinsu. Sun riga sun yi nasu addu’ar. Ta tambaye su, ‘Mene ne kuka yi addu’a a kai?’ “Jehobah, don Allah ka taimaki Baba ya daina shan tabar sigari.” Matar ta kira mijinta, “Ka zo ka ji addu’ar yaranka.” Sa’ad da ya yi hakan, sai ya soma kuka kuma ya faɗa, “Ba zan sake shan tabar sigari kuma ba!” Ya cika alkawarinsa, kuma yanzu fiye da mutane 15 a cikin wannan iyalin Shaidu ne.
Hidima a Afirka
A shekara ta 1959 aka tura mu zuwa birnin Mogadishu, da ke ƙasar Somaliya, tare da mutane biyu masu hidima a ƙasar waje, Arturo Leveris da wana Angelo. Ana hargitsin siyasa mai tsanani sa’ad da muka isa. Ya kamata gwamnatin Italiya su ja-goranci ƙasar Somaliya su samu ’yanci bisa umurni da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ba da, amma yanayin kamar yana taɓarɓarewa. Wasu mutanen Italiya da muka yi nazari da su suka bar ƙasar, kuma bai yiwu ba a ƙafa ikilisiya a wurin.
A wannan lokacin, mai ziyara mai kula da reshe ya ce na zama mataimakinsa. Saboda haka muka soma ziyarar ƙasashe da ke kusa da wurin. Wasu da muka yi nazari da su sun samu ci gaba amma sun bar ƙasarsu domin hamayya. Wasu sun tsaya ko da yake sun jimre wa wahala da yawa.a Yin tunani a kan ƙaunarsu ga Jehobah da abin da suka jimre don su kasance da aminci har ila yana sa mu farin ciki.
Zafi da laima da suke ƙasar Somaliya da Eritrea sau da yawa suna da tsanani ainun. Wasu abincin wurin suna sa mu daɗa jin zafi. A lokaci na farko da muka ci ɗaya daga cikin waɗannan abincin a gidan wata ɗalibanmu na Littafi Mai Tsarki, cikin wasa matata ta ce kunnuwanta sun yi ja kamar danja!
Sa’ad da aka tura Angelo da Arturo zuwa wani birni, aka bar mu mu kaɗai. Ba shi da sauƙi mu kasance mu kaɗai, ba mai ƙarfafa mu. Duk da haka, wannan yanayi ya taimaka mana mu kusaci Jehobah kuma mu dogara gare shi sosai. Ziyara da muka kai zuwa ƙasashe da aka hana aikinmu tushen ƙarfafa ne a gare mu.
A ƙasar Somaliya, da akwai wahaloli dabam dabam. Ba mu da firiji, saboda haka muna sayan yawan abinci da za mu ci kowace rana, ko idan hakan yana nufin sayan ’yan kifin shark mai baban kai ko kuma ’ya’yan itatuwa, kamar su mangwaro da gwanda, da garehul (manyan lemu) da kwakwa, ko kuma ayaba. Sau da yawa muna jimre da ƙwari. Wani lokaci suna tsayawa a kan wuyanmu sa’ad da muke gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki. Muna da basfa, saboda haka ba ma tafiya na sa’o’i a cikin zafin rana.
Mun Koma Ƙasar Italiya
Da taimakon abokai, mun iya samun kwalekwale mai ɗaukan ayaba don mu tafi Italiya mu halarci taron ƙasashe da aka yi a birnin Turin a shekara ta 1961. Mun ji cewa za a tura mu wani wuri. A watan Satumba na shekara ta 1962 muka koma Italiya, inda na soma hidimar mai kula da da’ira. Don muna ziyarar da’irori biyu, mun sayi ƙaramar mota da muka yi amfani da ita na tsawon shekara biyar.
Bayan mun zauna a zafin Afirka, yanzu za mu jimre da sanyi. A lokacin ɗari na farko, sa’ad da muke ziyarar wata ikilisiya da ke kusa da tudun Alps, mun kwana a cikin wani ɗaki da ba a sa abin ɗumama ɗaki ba, a kan ma’adanan ciyayi. Sanyin ya yi yawa har muka sa kwat kafin mu yi barci. Daddaren nan, kaji guda huɗu da karnuka biyu suka mutu don sanyi!
Daga baya, na yi hidimar mai kula da gunduma. A waɗannan shekaru, mun ziyarci dukan ƙasar Italiya. Mun ziyarci wasu wurare, kamar su Calabria da Sicily sau da yawa. Muna ƙarfafa matasa su samu ci gaba a ruhaniya kuma su yi aikin cim ma burin yin hidima a matsayin masu kula a ikilisiya da masu kula masu ziyara ko kuma masu hidima a Bethel.
Mun koyi abubuwa da yawa daga abokai masu aminci da suka bauta wa Jehobah da dukan zuciyarsu. Muna daraja halayensu, kamar kasancewa da cikakken aminci ga Jehobah, yin karimci, kuma suna ƙaunar ’yan’uwansu, suna kuma da halin daidaitawa da kuma sadaukarwa. Mun halarci ɗaurin aure a Majami’ar Mulki. Shaidu da aka amince da su a matsayin masu hidima na addini ne suka yi waɗannan ɗaurin aure, wanda ba zai yiwu ba a cikin ƙasar shekaru da yawa da suka shige. Ikilisiyoyi ba sa yin taro kuma a cikin kicin na ’yan’uwa ko kuma su zauna a kan katako, kamar yadda suke yi dā a birnin Turin. Maimakon haka, yawancin ikilisiyoyi suna da Majami’un Mulki masu kyau da ke ɗaukaka Jehobah. Ba ma yin manyan taro a filin wasa da ba su dace ba, maimakon haka muna yi a Majami’un Babban Taro. Kuma abin farin ciki ne mu ga adadin masu shela sun wuce 243,000. Sa’ad da muka isa ƙasar Italiya, da akwai masu shela 490 kaɗai.
Mun Yi Zaɓi Mai Kyau
Mun fuskanci wasu matsaloli da suka ƙunshi kewar gida da rashin lafiya. Fern tana kewar gida duk lokacin da ta ga teku. Kuma an yi mata tiyata masu tsanani sau uku. Akwai lokacin da za ta je yin nazarin Littafi Mai Tsarki da wani, sai wani mai hamayya ya kai mata hari da shebur mai yatsu. Wannan harin da aka kai mata ya sa a kwantar da ita a asibiti.
Ko da yake wani lokaci muna fuskantar sanyin gwiwa, amma mun ‘sa begenmu ga Jehobah,’ bisa ga abin da ke Makoki 3:24. Shi Allah ne mai ta’aziyya. A wani lokaci da muke sanyin gwiwa, Fern ta samu wata wasiƙa mai ban ƙarfafa daga Ɗan’uwa Nathan Knorr. Ya rubuta cewa tun da yake an haife shi kusa da Bethlehem, Pennsylvania, ya san inda Fern ta soma hidimar majagaba, ya sani sarai cewa matan Pennsylvania Dutch kamar ita suna da ƙarfi da kuma naciya. Gaskiyarsa. Cikin shekaru da yawa, mun samu ƙarfafa a hanyoyi da yawa kuma daga mutane da yawa.
Duk da matsaloli, mun yi ƙoƙari mu ci gaba da kasancewa da himma a hidimar. Ta wurin kwatanta wannan ruhu na himma da Lambrusco, wata giya mai tartsatsi a ƙasar Italiya, Fern da wasa ta ce, “Ba za mu bar ruhunmu ya daina tartsatsi ba.” Bayan shekara 40 na aikin mai kula da da’ira da gunduma, mun samu sabon gata na ziyara da kafa rukuni da ikilisiyoyi a wasu harsuna da ba na Italiya ba. Irin waɗannan rukunin suna wa’azi ga mutane daga ƙasar Bangladesh da Sin da Eritrea da Habasha da Gana da Indiya da Nijeriya da Philippines da Sri Lanka da kuma wasu ƙasashe. Littafi ba zai isa ba don mu rubuta hanyoyi masu ban al’ajabi da muka ga ikon Kalmar Allah na canja rayuwar waɗanda suka ɗanɗana jin ƙan Jehobah.—Mi. 7:18, 19.
Muna addu’a kowace rana ga Jehobah cewa ya ci gaba da ba mu ƙarfi na hankali da na zahiri da muke bukata don mu cika hidimarmu. Farin cikin Ubangiji shi ne ƙarfinmu. Yana sa idanunmu su haskaka kuma ya tabbatar mana cewa mun yi zaɓi da suka dace a rayuwa yayin da muke yaɗa koyarwar Littafi Mai Tsarki.—Afis. 3:7; Kol. 1:29.
[Hasiya]
a Ka duba 1992 Yearbook of Jehovah’s Witnesses, shafuffuka na 95-184.
[Taswira/Hotuna da ke shafi na 27-29]
(Don ganin cikakken rubutun, ka duba littafin)
Iyayena a birnin Rochester, New York
1948
A birnin South Lansing don aji na 12 na makarantar Giliyad
1949
Ni da Fern kafin mu tafi ƙasar Italiya
A tsibirin Capri da ke ƙasar Italiya
1952
A birnin Turin da Naples tare da wasu masu wa’azi a ƙasashen waje
1963
Fern tare da wasu ɗalibanta na Littafi Mai Tsarki
“Ba za mu bar ruhunmu ya daina tartsatsi ba”