Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 12/15 p. 25
  • Ba a Makara a Bauta wa Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ba a Makara a Bauta wa Allah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Latvia ta Karɓi Bishara
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Muhimman Abubuwan da Na Shaida a Bautar Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Kana Bukatar Jimiri
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Yadda Za ka Iya More Yanayinka na Marar Aure
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 12/15 p. 25

Ba a Makara a Bauta wa Allah

A birnin Málaga, a kudancin ƙasar Sifen, wata mahaifiya da ’yarta masu suna iri ɗaya, wato Ana, sun yi baftisma a ranar 19 ga Disamba, 2009. Suna cikin mutane dubu biyu da ɗari uku da hamsin da biyu da suka ɗauki wannan matakin a ƙasar Sifen a shekara ta 2009. Amma wata kyakkyawar abu game da wannan mahaifiyar da ’yarta ita ce shekarunsu. Shekarar mahaifiyar ɗari da bakwai ne kuma na ’yarta tamanin da uku!

Mene ne ya motsa su su yi baftisma a matsayin alamar keɓe kansu ga Jehobah? A farkon shekara ta 1970, wata maƙwabciya takan gayyaci Ana ƙarama zuwa Rukunin Nazarin Littafi na Ikilisiya wanda ake yi a gidan Mashaidiyar. Ana takan halarta a kai a kai. Amma dai, saboda aikinta, Ana ba ta samu ci gaba ba.

Kusan shekara goma bayan hakan, wasu cikin ’ya’yan Ana suka soma nazarin Littafi Mai Tsarki kuma bayan ɗan lokaci suka zama bayin Jehobah. Ɗaya daga cikinsu, Mari Carmen, ta sa mahaifiyarta ta sake son gaskiyar Littafi Mai Tsarki kuma ta taimaka mata ta amince a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ita. Sai daga baya, kakar Mari Carmen, wato, Ana babba, ita ma ta soma nuna tana son saƙon Littafi Mai Tsarki. Daga baya, mutum goma cikin wannan iyalin suka yi baftisma.

A ranar baftismarsu, Ana biyun, mahaifiyar da ’yarta, sun yi farin ciki matuƙa. “Jehobah ya yi mini alheri sosai, da ya sa na san shi,” in ji Ana mai shekara ɗari da bakwai. “Kafin Aljanna ta zo,” in ji ’yarta, “Ina so na bauta wa Jehobah, ina yin nufinsa da kuma yin wa’azin bishara iya gwargwado ta.”

Abin da ya ba waɗannan gwauraye biyu farin ciki shi ne halartar tarurruka. “Ba sa fasa halartar kowanne taro,” in ji wani dattijo a ikilisiyarsu. “Suna a shirye kullum su ba da kalami a Nazarin Hasumiyar Tsaro.”

Misalinsu na aminci ya sa mu tuna da gwauruwa Hannatu, wadda “ba ta rabuwa da haikali, tana sujjada tare da azumi da addu’o’i dare da rana.” Hakan ya sa ta samu gatar ganin Yesu sa’ad da yake ɗan jariri. (Luk 2:36-38) Sa’ad da Hannatu take da shekara tamanin da huɗu, tsufa bai hana ta bauta wa Jehobah ba, hakan ma takwarunta a yau.

Shin kana da ’yan’uwa da suke a shirye su saurara wa saƙon Littafi Mai Tsarki? Ko kuma ka taɓa sami tsoho ko tsohuwa da ke a shirye ya ko ta saurara maka sa’ad da ka ziyarce su a gidansu? Irin waɗannan za su iya zama kamar su Ana a wannan labarin, domin ba a taɓa makara a bauta wa Allahn gaskiya, Jehobah.

[Bayanin da ke shafi na 25]

“Jehobah ya yi mini alheri sosai”

[Bayanin da ke shafi na 25]

“Kafin Aljanna ta zo, ina so na bauta wa Jehobah”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba