Ka Sani?
Shin akwai kowane cikin almajiran Yesu sha biyu da ɗan’uwansa ne?
▪ Nassosi ba su ba da ainihin amsa ga wannan tambayar ba. Amma dai, wasu yanayi da al’ada sun nuna cewa wasu cikin almajiransa sha biyu ’yan’uwansa ne.
Marubutan Linjila sun faɗi sunayen matan da suke kallon Yesu yayin da yake mutuwa a kan gungumen azaba. Yohanna 19:25 ya yi magana game da su huɗu: “Uwatasa [Maryamu] da ’yar’uwar uwatasa, Maryamu matar Kilyobas, da kuma Maryamu Magdaliya.” Idan an gwada wannan ayar da kwatancin Matta da Markus game da wannan batun zai sa a kammala cewa ’yar’uwar mahaifiyar Yesu Salome ce. Kamar wannan Salome ce mahaifiyar ’ya’yan Zebedee. (Matta 27:55, 56; Markus 15:40) ’Ya’yanta waɗanda aka kira su Yaƙub da Yohanna, a wani wurin, ’ya’yan kawun Yesu ne. Yesu ya kira waɗannan ’yan’uwa biyu waɗanda suke sana’ar kamun kifi, su zama almajiransa.—Matta 4:21, 22.
Wasu littattafai sun yi da’awar cewa Kilyobas, ko Halfa, mijin wata mata da aka ambata a Yohanna 19:25, ɗan’uwan Yusufu ne, wato, mijin mahaifiyar Yesu. Idan wannan bayanin gaskiya ne, Yaƙub ɗan Halfa, wani cikin almajiran Yesu sha biyu ɗan kawunsa ne.—Matta 10:3.
Ta yaya ne Yesu da Yohanna Mai Baftisma suka danganci juna?
▪ Wasu sun yarda cewa waɗannan mutanen biyu sun danganci juna. An gaskata da hakan don fassarar Luka 1:36 wanda ba a bayyana dalla-dalla ba. Alal misali, fassarar King James Version, ta bayyana wannan ayar cewa mahaifiyar Yohanna, Alisabatu da mahaifiyar Yesu, Maryamu, dangin juna ne.
Ainihin kalmar Helenanci da aka yi amfani da ita a wannan ayar ba ta fito dalla dalla ba. Amma ta nuna cewa matan biyu dangin juna ne, amma lallai kawunsu ba ɗaya ba ne. Kamar yadda ƙamus ɗin nan The Interpreter’s Dictionary of the Bible ya ce, “ba za a iya yin amfani da kalmar ba wajen sanin ainihin dangantakarsu tun da kalmar tana da ma’ana da yawa.” To daga ina aka samo ra’ayin nan cewa Yesu ɗan kawun Yohanna ne? Kundin sanin nan The Catholic Encyclopedia ya ba da amsar: “Mun samo dukan bayanan da muke da su game da . . . iyayen Maryamu . . . ne daga littafin afokirifa.”
Saboda haka, Yesu da Yohanna dangin juna ne amma ba na kusa ba.