Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 10/1 pp. 24-25
  • Darasi Game da Jin Ƙai na Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Darasi Game da Jin Ƙai na Allah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Mutum Mai Tawali’u da Gaba Gaɗi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Halakar Saduma Da Gwamarata
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Yesu ya Warkar da Mutane ta Hanyar Mu’ujiza
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Yesu Ya Sa Masu Sauraransa Sun Yi Mamaki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 10/1 pp. 24-25

Domin Matasa

Darasi Game da Jin Ƙai na Allah

YUNANA—SASHE NA 2

Umurni: Ka yi wannan aikin a inda babu surutu. Sa’ad da kake karanta nassosi, ka sa kanka cikin yanayin. Ka yi tunanin yanayin a zuciyarka. Ka ji muryoyin mutanen. Ka ji yadda ainihin mutanen da ke ciki suke ji. Ka sa labarin ya kasance kamar yanzu yake faruwa.

1 KA YI TUNANI A KAN YANAYIN NAN.—KARANTA YUNANA 3:1–4:11.

Yaya kake ganin Yunana ya ji sa’ad da ya shiga birnin Nineba?

․․․․․

Yaya kake ganin muryar Yunana take sa’ad da yake furta hukuncin Jehobah?

․․․․․

Wane irin rashin jin daɗi ne Yunana ya fuskanta yayin da yake zaune a wajen birnin? (Duba Yunana 4:5-8.)

․․․․․

2 KA BINCIKA SOSAI.

Mene ne wataƙila ya sa Yunana yake so Jehobah ya halaka Nineba kamar yadda ya annabta?

․․․․․

Ta wajen yin amfani da littattafan bincike da kake da su, ka nemi ƙarin bayani game da (1) yadda fasalin zurma take, da (2) ma’anar tsummokaran da sarkin Nineba ya saka ya kuma zauna a cikin toka.

․․․․․

Duk da jinkirin da ya fara yi na yin annabci a Nineba, me ya sa za a iya kiran Yunana annabi mai aminci da kuma gaba gaɗi? (Matta 21:28-31)

․․․․․

3 KA YI AMFANI DA ABIN DA KA KOYA. KA RUBUTA ABIN DA KA KOYA GAME DA . . .

Zarafin da ’yan Adam suke da shi na yin watsi da salon rayuwa marar kyau.

․․․․․

Jin ƙai na Jehobah.

․․․․․

Abin da ya sa ya kamata mu kasance masu jin ƙai.

․․․․․

4 WANE ƁANGAREN WANNAN LABARIN NE YA FI MA’ANA A GARE KA, KUMA ME YA SA?

․․․․․

KA ƘARA KOYO GAME DA LITTAFI MAI TSARKI, A DUNIYAR GIZON www.watchtower.org DA www.jw.org

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba