Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 10/1 p. 22
  • Shin kowa yana da zarafi ya san Allah kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Shin kowa yana da zarafi ya san Allah kuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Game da Allah na Gaskiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ka Ƙaunaci Allah Da Yake Ƙaunarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ka Kasance Kusa da Jehobah
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • “Wajibi Ne Ka Ƙaunaci Jehobah Allahnka”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 10/1 p. 22

Masu Karatu Sun Yi Tambaya . . .

Shin kowa yana da zarafi ya san Allah kuwa?

▪ Sa’ad da aka tambaye shi ko wace doka ce mafi girma, Yesu ya ce: “Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka.” (Matta 22:37) Amma, kafin mutane su ƙaunaci Allah, suna bukatan su samu cikakken sani game da shi. (Yohanna 17:3) Shin kowa ne ke da zarafin samun wannan sanin kuwa?

Ainihin inda ake samun sani game da Allah shi ne a cikin Littafi Mai Tsarki. (2 Timotawus 3:16) Mutane da yawa suna zama a yankin da akwai Littafi Mai Tsarki a ko’ina. Wataƙila an ziyarci waɗannan mutanen a kai a kai don su samu cikakken sani game da Allah ta hanyar yin nazarin Littafi Mai Tsarki. (Matta 28:19) Wasu iyayensu Kiristoci masu ƙauna ne suka yi renonsu, suna ba su zarafin koyo game da Allah a ko yaushe.—Kubawar Shari’a 6:6, 7; Afisawa 6:4.

Wasu kuwa ba su samu irin wannan zarafi mai kyau ba. Wasu sun fito ne daga iyalai marasa kula inda iyaye ba sa nuna wa yaransu ƙauna. (2 Timotawus 3:1-5) Zai yi wa mutane da suka taso a irin wannan yanayin wuya su ɗauki Allah a matsayin Ubanmu na samaniya mai ƙauna. Mutane da yawa ba su samu zarafin yin makaranta sosai ba, kuma hakan ya sa ba su iya karanta Littafi Mai Tsarki ba. Koyarwar addinan ƙarya ta makantar da zukatan wasu, ko kuma suna zama a iyali, yanki, ko ƙasa inda ba a amince da koyarwar gaskiya ta Littafi Mai Tsarki ba. (2 Korintiyawa 4:4) Yanayin waɗannan mutanen zai iya hana su samun zarafin koya game da Allah kuma su ƙaunace shi kuwa?

Yesu ya faɗi cewa matsalolin da wasu suke fuskanta za su sa ya kasance da wuya su ƙaunaci Allah kuma su yi masa biyayya. (Matta 19:23, 24) Amma, Yesu ya tuna wa almajiransa cewa ko da wasu matsalolin sun fi ƙarfin mutum, “ga Allah dukan abu ya yiwu.”—Matta 19:25, 26.

Ka yi la’akari da waɗannan gaskiya da ke gaba: Jehobah Allah ya tabbatar da cewa Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki, ne littafin da aka fi rarrabawa. Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa za a yi wa’azin bishara game da Allah da kuma nufinsa ga duniya a cikin “iyakar duniya.” (Matta 24:14) A yau, Shaidun Jehobah suna wa’azin bishara a ƙasashe fiye da 230 kuma suna buga littattafai da suke bayyana Littafi Mai Tsarki a harsuna 500. Waɗanda ba su da Littafi Mai Tsarki har ila za su iya koyan abubuwa masu yawa game da Allah ta wajen lura da abubuwan da ya halitta.—Romawa 1:20.

Ƙari ga hakan, Kalmar Allah ta ce: “Ubangiji yana binciken dukan zukata, ya kuma gane dukan sifofin tunani: idan ka biɗe shi, yā samu gareka.” (1 Labarbaru 28:9) Ko da yake Jehobah bai yi alkawari cewa kowa zai samu zarafi iri ɗaya ba, amma ya tabbata cewa za a ba dukan masu zukatan kirki zarafi. Zai tabbata cewa waɗanda ba su taɓa samun zarafin koyo game da shi ba za su yi hakan ta wajen tashin matattu zuwa rai a sabuwar duniya ta adalci.—Ayyukan Manzanni 24:15.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba