Mai Da Hankali Yana Kawo Sakamako Mai Kyau
KANA mai da hankali ga zarafin yin wa’azi da za su iya tasowa babu shiri a yankin ikilisiyarku? ’Yan’uwanmu Kiristoci da suke bakin teku inda jirage suke sauka a Turku, Finland, sun mai da hankali kuma hakan ya kai ga sakamako mai kyau.
Akwai lokacin da ’yan’uwan da ke Turku suka lura cewa wani rukunin mazan Asiya sun shigo gari domin su kammala aiki a kan wani babban jirgin ruwa da ake ginawa a inda ake gina jiragen ruwa. Daga baya, sai wani ɗan’uwa ya binciko hotal ɗin da ma’aikatan suka sauƙa. Ya sake gano cewa da sassafe, ana kwasan ma’aikatan da bas daga hotal ɗin zuwa tashar jiragen ruwa. Nan da nan, sai ya gaya wa ’yan’uwa da suke ikilisiyar da ake yaren Turanci a Turku.
Dattawan ikilisiyar sun fahimci cewa zuwan baƙi da yawa ya ba su zarafin gaya musu saƙon Mulki, kuma nan da nan suka shirya su yin kamfen na musamman. A ranar Lahadi na makon, masu shela guda goma suka taru a tashar safa da ƙarfe bakwai na safe. Da farko, babu ma’aikacin da ya zo. ‘Mun makara ne sosai?’ ’yan’uwan suna mamaki. ‘Sun bar Turku ne?’ Amma sai ɗaya daga cikin ma’aikatan ya zo yana sanye da kayan aiki. Sai kuma wani ma’aikacin ya ɓullo, sai suka soma fitowa ɗaɗɗaya. Ba da daɗewa ba, sai ma’aikata da yawa suka taru kusa da tashar bas ɗin. Masu shelan suka soma yin wa’azi, suna ba ma’aikatan littattafan Turanci. Abin farin ciki, ya ɗauki sa’a guda kafin dukan ma’aikatan su sami wurin zama a cikin motocin, kuma hakan ya ba ’yan’uwan isashen lokaci su yi magana da yawancinsu. Da motocin suka tashi, ma’aikatan sun tafi da ƙasidu 126 da kuma jaridu 329!
Sakamako mai kyau da suka samu ya ƙarfafa ’yan’uwan su sake yin irin wannan kamfen ɗin a mako na gaba, a lokacin ziyarar mai kula da ɗa’ira. Ana ruwa a ranar, a misalin shida da rabi na safe, mai kula da ɗa’ira ya gudanar da taron hidimar fage, sai masu shela ashirin da huɗu suka nufi tashar bas ɗin. A wannan lokaci sun tafi da littattafai na yaren Tagalog don sun gano cewa baƙin da yawa sun zo ne daga ƙasar Philippines. Da safiyar wannan rana, da motocin suka tashi zuwa inda jiragen suke tsayawa, ma’aikatan sun tafi da littattafai 7, ƙasidu 69, da kuma mujallu 479. Ka yi tunanin irin farin cikin da ’yan’uwanmu maza da mata suka yi domin sun saka hannu a wannan kamfen ɗin!
Kafin ma’aikatan su koma ƙasarsu, ’yan’uwan sun ziyarci yawancinsu a hotal ɗin da suka sauka kuma suka bayyana musu saƙon Mulkin dalla-dalla. Wasu ma’aikatan sun ce sun taɓa saduwa da Shaidu a wasu ɓangarorin duniya. Ma’aikatan sun furta godiyarsu ga ’yan’uwan don ƙoƙarin da suka yi don su tuntuɓe su a lokacin da suke ƙasar Finland.
Kana mai da hankali ga zarafin da za su iya tasowa a yankin ikilisiyarku? Kana ɗaukan mataki ka yi magana da mutanen da suka fito daga wurare dabam-dabam? Idan kana haka, kai ma za ka sami sakamako irin waɗanda ’yan’uwanmu da ke Turku suka more.
[Taswira/Hoton da ke shafi na 32]
(Don ganin cikakken rubutun, ka duba littafin)
FINLAND
HELSINKI
Turku