Ka Kasance Da Ƙarfi A Ruhaniya Yayin Da Kake Kula Da Dangi Marar Lafiya
BAYAN da aka gano wani kumburi da ke kusa da ƙashin bayanta, an gano cewa Kim, wata, Mashaidiya, tana da ciwon kansa.a “Sa’ad da aka cire kumburin ta hanyar tiyata,” in ji maigidanta, Steve, “Kim ta shiga yin jinyar kansa. A sakamakon jinyar, ta rarrauna sosai. Ba ta iya yin tafiya sosai.”
Ka yi tunanin irin baƙin cikin da Steve ya yi sa’ad da ya ga matarsa da yake ƙauna take fama da wannan ciwo da ke raunana ta. Wataƙila kana da wani a cikin iyali da yake fama da mugun ciwo ko kuma sakamakon tsufa. (M. Wa. 12:1-7) Idan haka ne, domin ka kula da wanda kake ƙauna da kyau, kana bukatan ka kula da kanka. Idan ka raunana a ruhaniya, hakan zai iya shafan motsin ranka da kuma lafiyarka kuma ba za ka iya ba da taimakon da iyalinka ke bukata ba. Ta yaya za ka iya daidaita ayyuka na ruhaniya yayin da kake kula da ɗan’uwanka da bai da lafiya ko wanda ya tsufa? Akwai wasu abubuwa da waɗanda suke cikin ikilisiyar Kirista za su iya yi don su nuna kula ga irin waɗannan masu ciwo?
Ka Kasance da Daidaituwa—Ta Yaya?
Domin ka kula da ruhaniyarka da kuma lafiyarka a lokacin da kake kula da dangi marar lafiya, kana bukatar daidaitawa da kuma yin kasafin lokacinka da kuma kuzari. “Wurin masu-tawali’u akwai hikima,” in ji Misalai 11:2. A wannan mahalli, kalmar nan “tawali’u” tana nufin mutum ya san kasawarsa. Domin ka tabbata cewa ba ka yi fiye da abin da ya fi ƙarfin ka ba, kana bukatan ka bincika tsarin aikinka da kuma hakkokinka.
Steve ya nuna hikima da kuma tawali’u ta wajen bincika ayyukansa. Ƙari ga aikinsa, yana hidima a matsayin mai tsara ayyukan rukunin dattawa da kuma mai kula da hidima a ikilisiyar Shaidun Jehobah a ƙasar Ireland. Har ila, yana cikin Kwamitin Hulɗa da Asibitoci a yankinsu. “Kim ba ta taɓa cewa ina ƙyale ta ta wurin mai da hankali sosai ga waɗannan hakkokin ba,” in ji Steve. “Amma na sani cewa ina yin abin da ya fi ƙarfina.” Ta yaya Steve ya daidaita yanayin? “Bayan da na yi addu’a,” in ji shi, “na tsai da shawara na daina yin hidima na mai tsara ayyukan rukunin dattawa. Na ci gaba da yin hidima a matsayin dattijo, amma ta wajen ba da wasu cikin hakkokin ikilisiya da nake da su ga ’yan’uwa, na samu damar ba Kim lokaci da kulawa da take bukata.”
Da shigewar lokaci, Kim ta samu sauƙi. Steve da Kim sun sake bincika yanayinsu, kuma da taimakon matarsa, Steve ya sake ɗaukan hakkokinsa na dā a cikin ikilisiya. “Mun koyi yin aiki daidai da yanayin da ciwon ya ƙyale,” in ji Steve. “Na yi godiya ga Jehobah don taimakonsa da kuma matata don goyon bayanta duk da rashin lafiyarta.”
Ka yi la’akari da labarin Jerry, mai kula mai ziyara, da matarsa, Maria. Suna bukatan su daidaita makasudansu domin su kula da iyayensu da suka tsufa. “Da ni da maigidana muna da makasudin yin hidima a matsayin masu wa’azi a ƙasashen waje,” in ji Maria. “Jerry ne kaɗai ɗansu tilo, kuma iyayensa suna bukatan kulawa. Saboda haka, muka tsai da shawarar mu zauna a Ireland don mu kula da su. Ta wurin yin hakan, mun samu damar kula da mahaifin Jerry sa’ad da aka kwantar da shi a asibiti kafin ya rasu. A yanzu muna yin magana da mahaifiyar Jerry a kowace rana, kuma inda muke bai da nisa saboda taimaka mata. Ikilisiyar da mahaifiyar Jerry take ta taimaka sosai, hakan ya sa mun ci gaba da hidimar kula da da’ira da muke yi.”
Yadda Wasu Za Su Iya Taimakawa
Sa’ad da yake faɗin irin tanadodin da za a yi wa gwauraye tsofaffi a cikin ikilisiya, manzo Bulus ya rubuta: “Amma idan wani bai yi tattalin nasa ba, balle na iyalinsa, ya musunci imani, gwamma marar-bangaskiya da shi.” Bulus ya tunasar da ’yan’uwa Kiristoci cewa idan suna son tafarkin rayuwarsu ta zama “abin karɓa ne a wurin Allah,” dole ne su kula da iyayensu tsofaffi da kuma kakanninsu ta wajen biyan bukatunsu. (1 Tim. 5:4, 8) Amma, waɗanda suke cikin ikilisiya ma suna bukatan su ba da taimako mai amfani.
Ka yi la’akari da labarin Hakan da kuma Inger, ma’aurata tsofaffi da suke da zama a ƙasar Sweden. “Yayin da aka gano cewa matata tana da ciwon kansa,” in ji Hakan, “hakan ya girgiza mu ƙwarai. A dā Inger tana cike da lafiya da ƙarfi. A yanzu kuwa muna bukatan mu riƙa zuwa asibiti a kullum don jinya, kuma maganin yana raunanata. Inger ta zauna a gida a wannan lokaci, kuma ina bukatan in zauna da ita in kula da ita.” Ta yaya ikilisiyarsu ta taimaka wa Hakan da kuma Inger?
Dattawan ikilisiyar sun yi shiri domin ma’auratan su saurari taron ikilisiya ta hanyar tarho. Ƙari ga hakan, ’yan’uwa maza da mata sun ci gaba da ziyartarsu kuma suna kiransu ta hanyar tarho. Sun kuma aika wasiƙu da katuna. “Mun ji a jikinmu irin tallafawar da dukan ’yan’uwa suka yi mana da kuma yadda Jehobah ya taimaka mana,” in ji Hakan. “Wannan kulawa yana da muhimmanci don mu kasance da ƙarfi a ruhaniya. Muna farin ciki, Inger ta warke, kuma muna iya halartar taron Kirista a Majami’ar Mulki.” Sa’ad da waɗanda suke cikin ikilisiya suka yi iya ƙoƙarinsu don su taimaka wa marasa lafiya da kuma tsofaffin da ke tsakaninsu, suna nuna cewa su ‘abokai ne na kullayaumi da ke nuna ƙauna, da kuma ’yan’uwa da an haife domin kwanakin shan wuya.’—Mis. 17:17.
Jehobah Yana Ɗaukan Taimakon da Kuke Ba da Wa da Tamani
Kula da dangi marar lafiya ba ƙaramin aiki ba ne. Duk da haka, Sarki Dauda ya rubuta: “Mai-albarka ne shi wanda ya kula da matalauta,” kamar mutumin da yake bukatan taimako domin rashin lafiya.—Zab. 41:1.
Me ya sa waɗanda suke kula da marasa lafiya ko masu shan wahala suke farin ciki? “Mai-jin tausayin fakirai yana bada rance ga Ubangiji,” in ji Misalai 19:17, “kuma za ya sāka masa da alherinsa.” Allah na gaskiya yana mai da hankali musamman ga bayinsa masu aminci waɗanda suke fama da ciwo, kuma yana yi wa waɗanda suka kula da su albarka. Mai Zabura ya raira: “Ubangiji za ya toƙara [irin wannan mutumin] a bisa shimfiɗarsa ta rashin lafiya: kana gyarta masa shimfiɗa cikin cutarsa.” (Zab. 41:3) Muna da tabbaci cewa idan wanda yake nuna kula cikin ƙauna ya fuskanci wahala ko bala’i, Jehobah zai taimake shi.
Abin farin ciki ne mu san cewa Jehobah Allah yana lura da kuma amince da abin da muke yi don mu kula da dangi marar lafiya! Ko da yake ba da irin wannan taimako zai bukaci ƙoƙartawa a gefenmu, Nassosi sun ba mu tabbaci cewa “da irin waɗannan hadayu Allah yana jin daɗi.”—Ibran. 13:16.
[Hasiya]
a An canza sunayen.
[Hotuna da ke shafi na 18]
Ka kasance da ƙarfi a ruhaniya kuma ka karɓi taimako daga wasu