Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 5/15 pp. 12-17
  • Mata, Me Ya Sa Za Ku Miƙa Kai Ga Shugabanci?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mata, Me Ya Sa Za Ku Miƙa Kai Ga Shugabanci?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Sai In Yi Masa Mataimaki”
  • Sa’ad da Abokin Aure Ba Mai Bi Ba Ne
  • Za Su Riƙa Faɗin Ra’ayinsu Kuwa?
  • Mata Biyu da Ba Su Yi Shiru Ba
  • ‘Macen da Ake Yabonta’
  • Ka Nuna Godiya don Kyautar Allah
  • Mata Ku Yi Wa Mazanku Ladabi Sosai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • “Miji Kuma Shi Ne Shugaban Matarsa”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Shawara Mai Kyau Ga Ma’aurata
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 5/15 pp. 12-17

Mata, Me Ya Sa Za Ku Miƙa Kai Ga Shugabanci?

“Kan mace kuma namiji ne.”—1 KOR. 11:3.

1, 2. (a) Menene manzo Bulus ya rubuta game da tsarin shugabanci na Jehobah da kuma miƙa kai? (b) Waɗanne tambayoyi za a tattauna a wannan talifin?

JEHOBAH ya kafa tsarin shugabanci da manzo Bulus ya ambata yayin da ya rubuta cewa “kan kowane namiji Kristi ne” da kuma “kan Kristi kuma Allah ne.” (1 Kor. 11:3) Talifin da ya gabata ya nuna cewa Yesu ya ɗauke shi gata da kuma abin farin ciki ya yi biyayya da Shugabansa, Jehobah Allah, kuma Kristi ne shugaban Kiristoci maza. Kristi mai alheri ne, mai hankali, mai tausayi, da kuma marar son kai yayin da yake sha’ani da mutane. Ya kamata maza a cikin ikilisiya su yi hakan ga wasu, musamman matansu.

2 Mata kuma fa? Wanene shugabansu? “Kan mace kuma namiji ne,” in ji Bulus. Yaya mata za su ɗauki wannan hurarren furci? Za a yi amfani da wannan ƙa’idar idan mai gidan marar bi ne? Miƙa kai ga shugabancin namiji na bukatan mata ta yi shiru a cikin auren ne, ba za ta faɗa ra’ayinta ba sa’ad da ake tsai da shawara? A wace hanya ce mace za ta sa a yabe ta?

“Sai In Yi Masa Mataimaki”

3, 4. Me ya sa tsarin shugabanci a aure yake da amfani?

3 Allah ne ya shirya wanda zai zama shugaba a iyali. Bayan ya halicci Adamu, Jehobah ya ci gaba da cewa: “Ba ya yi kyau ba mutum shi kasance shi ɗaya; sai in yi masa mataimaki mai-dacewa.” Bayan halittar Hauwa’u, Adamu ya yi farin cikin samun abokiya da kuma mataimakiya da ya ce: “Wannan yanzu ƙashi ne daga ƙasusuwana, nama ne daga namana.” (Far. 2:18-24) Adamu da Hauwa’u suna da gata mai girma na zama uba da kuma uwa na dukan ’yan Adam kamiltattu, waɗanda za su yi rayuwa har abada a cikin farin ciki a aljanna a dukan duniya.

4 Domin tawayen iyayenmu na farko, an yi hasarar kamiltaccen yanayin gonar Adnin. (Karanta Romawa 5:12.) Amma tsarin shugabanci ta tsaya daram. Yayin da dukansu suka yi amfani da shi yadda ya dace, yana kawo amfani mai girma da kuma farin ciki a cikin aure. Sakamakon zai yi daidai da yadda Yesu ya ji game da miƙa kai ga Shugabansa, Jehobah. A rayuwarsa kafin ya zo duniya, Yesu kullum yana “farinciki a gaban [Jehobah].” (Mis. 8:30) Domin ajizanci, maza ba sa iya zama kamiltattun shugabanni, kuma mata ba sa iya miƙa kai gabaki ɗaya. Yayin da magidanta da kuma mata suka ci gaba da yin iyakar ƙoƙarinsu, ko ta yaya, za su sami sakamako mai kyau na farin ciki a cikin aure a wannan lokaci.

5. Me ya sa ma’aurata za su bi gargaɗin da ke Romawa 12:10?

5 Idan aure zai yi nasara yana da muhimmanci sosai ma’aurata su yi amfani da gargaɗin Littafi Mai Tsarki ga dukan Kiristoci: ‘Ku yi zaman daɗin soyayya da junanku cikin ƙaunar ’yan’uwa; kuna gabatar da juna cikin bangirma.’ (Rom. 12:10) Kuma, ya kamata mai gida da uwargida su yi aiki tuƙuru don su ‘kasance da nasiha zuwa ga junan[su], masu-tabshin zuciya, suna yi wa junansu gafara.’—Afis. 4:32.

Sa’ad da Abokin Aure Ba Mai Bi Ba Ne

6, 7. Menene zai iya zama sakamakon idan mace Kirista tana da halin biyayya ga mijinta marar bi?

6 Idan abokin aurenki ba bawan Jehobah ba kuma fa? Sau da yawa, maigida ne yake zama marar bi. A wannan yanayi, yaya mace za ta bi da shi? Littafi Mai Tsarki ya ba da amsa: “Ku mataye kuma, ku yi zaman biyayya ga mazaje naku; domin ko da akwai waɗansu da ba su yin biyayya da magana, su rinjayu ban da magana saboda halayen matansu; suna lura da halayenku masu-tsabta tare da tsoro.”—1 Bit. 3:1, 2.

7 Kalmar Allah ta gaya wa mata ta yi zaman biyayya ga mijinta marar bi. Halinta mai kyau zai rinjaye shi ya yi la’akari da abin da ya motsa ta ta yi hakan. A sakamakon hakan, maigidan zai bincika imanin matarsa Kirista sai kuma a hankali ya karɓi gaskiyar da kansa.

8, 9. Menene mata Kirista za ta iya yi idan maigidanta marar bi ba ya karɓi saƙon ba ko da yake tana da hali mai kyau?

8 Idan maigidan marar bi bai canja kuma ba fa? Ko da yake zai kasance da wuya, Nassosi sun ƙarfafa mata su nuna halaye masu kyau a dukan lokaci. Alal misali, 1 Korintiyawa 13:4 ta faɗa: “Ƙauna tana da yawan haƙuri.” Saboda haka, yana da kyau mata Kirista da “dukan tawali’u da ladabi, da jimrewa,” tana haƙuri da yanayin cikin ƙauna. (Afis. 4:2) Da taimakon ikon Allah, wato ruhunsa mai tsarki, za mu iya nuna halaye na Kirista ko a yanayi mai wuya ma.

9 “Zan iya yin abu duka ta wurin Kristi da yake ƙarfafani,” in ji Bulus. (Filib. 4:13) Ruhun Allah zai iya taimakon abokiyar aure Kirista ta yi abubuwa da yawa da ba zai yiwu ba. Alal misali, mugun hali daga abokin auren zai iya jarabtar mata ta yi ramako. Amma dai, Littafi Mai tsarki ya gaya wa dukan Kiristoci: “Kada ku sāka wa kowane mutum mugunta da mugunta . . . . Gama an rubuta: ‘Ɗaukar fansa tawa ce; ni zan yi sakamako, in ji Ubangiji.’” (Rom. 12:17-19) Hakazalika, Tassalunikawa 5:15 ya shawarce mu: “Ku yi hankali kada kowa ya saka wa wani mugunta da mugunta; amma kullum a biɗi abin da ke nagari zuwa ga juna ga dukan mutane kuma.” Da taimakon ruhu mai tsarki na Jehobah, abin da ba za mu iya yi da ƙarfinmu ba zai yiwu. Zai dace mu yi addu’a ga ruhu mai tsarki na Allah ya yi mana tanadin abin da ba mu da shi!

10. Yaya Yesu ya bi da baƙar magana da kuma munanan halaye na wasu?

10 Yesu ya kafa misali mai kyau wajen yin sha’ani da waɗanda suka faɗa ko yi abubuwa da ba su da kyau a gare shi. “Sa’anda aka zage shi,” in ji 1 Bitrus 2:23, “ba ya mayar da zagi ba; sa’anda ya sha azaba, ba ya yi kashedi ba; amma ya danƙa maganatasa ga wanda ke yin shari’a mai-adalci.” An gargaɗe mu mu bi misalinsa mai kyau. Kada ka yi fushi don munanan halaye na wasu. Kamar yadda aka gargaɗi dukan Kiristoci, ku zama “masu-tabshin zuciya, masu-tawali’u, ba masu rama mugunta da mugunta ba.”—1 Bit. 3:8, 9.

Za Su Riƙa Faɗin Ra’ayinsu Kuwa?

11. Wane gata mai girma wasu mata suke da shi?

11 Yin biyayya ga shugabancin maigida yana nufin cewa mata ba za su riƙa saka baki a al’amura na iyali ko wasu batutuwa ne? A’a. Jehobah ya ba mata da kuma maza gata masu yawa. Ka yi tunanin gata mai girma da aka ba mutane 144,000 da za su zama sarakuna da firistoci a sama a ƙarƙashin Kristi yayin da zai yi sarauta a bisa wannan duniya! Wannan adadin ya haɗa da mata. (Gal. 3:26-29) Babu shakka, Jehobah ya ba mata aiki mai muhimmanci a cikin tsarinsa na abubuwa.

12, 13. Ka ba da misali da ya nuna cewa mata sun yi annabci.

12 Alal misali, a lokacin da aka rubuta littafi mai tsarki, mata sun yi annabci. Joel 2:28, 29 ya annabta: “Zan zuba ruhuna a bisa dukan masu-rai; ’ya’yanku maza da mata za su yi annabci. . . . Kuma a bisa bayina maza da mata zan zuba ruhuna cikin waɗancan kwanaki.”

13 Wasu almajiran Yesu 120 da suka taru a gidan sama a Urushalima a ranar Fentikos na shekara ta 33 A.Z., sun haɗa da mata da maza. An zubo da ruhun Allah a kan wannan rukunin duka. Saboda haka, Bitrus ya yi ƙaulin abin da annabi Joel ya annabta da kuma yi amfani da shi ga maza da mata duka. Bitrus ya ce: “Abin da aka faɗi ta bakin annabi Yowel; Zai zama a cikin kwanakin ƙarshe, in ji Allah, Zan zuba Ruhuna bisa mai-rai duka: ’Ya’yanku, maza da mata, za su yi annabci, . . . bisa bayina, maza da mata, Zan zuba Ruhuna cikin waɗannan kwanaki, za su yi annabci kuma.”—A. M. 2:16-18.

14. Wane hakki ne mata suke da shi wajen yaɗa Kiristanci na farko?

14 A ƙarni na farko, mata sun ɗauki hakki na musamman wajen yaɗa Kiristanci. Sun yi wa’azi ga mutane game da Mulkin Allah kuma sun yi abubuwa da suka shafi aikin wa’azi. (Luk 8:1-3) Alal misali, manzo Bulus ya kira Fibi “yar’uwanmu, wadda ta ke mai-hidimar ikilisiya da ke a Kankriya.” Da yake aika gaisuwa ga abokan aikinsa, Bulus ya ambata adadin mata da yawa masu aminci, haɗe da “Tarifaina da Tarifusa, waɗanda su ke aiki cikin Ubangiji.” Ya kuma gai da “Barsisa ƙaunatace, wanda ya yi aiki da yawa cikin Ubangiji.”—Rom. 16:1, 12.

15. Wane hakki ne mata suke da shi wajen yaɗa Kiristanci a zamaninmu?

15 A zamaninmu, yawancin mutane fiye da miliyan bakwai da suke wa’azin bisharar Mulkin Allah a dukan duniya mata ne. (Mat. 24:14) Da yawa a cikinsu suna hidima na cikakken lokaci, suna wa’azi a ƙasashen waje, da kuma hidima a Bethel. Mai Zabura Dauda ya raira waƙa: “Ubangiji ya bada sako: Mata masu-shelar bisharan kuwa babbar runduna ne.” (Zab. 68:11) Waɗannan kalmomi sun zama gaskiya! Jehobah yana mutunta matsayin mata wajen sanar da bisharar da kuma cim ma ƙudurinsa. Bukatarsa cewa mata su miƙa kai ba ya nufin yin shiru.

Mata Biyu da Ba Su Yi Shiru Ba

16, 17. Yaya misalin Saratu ya nuna cewa mata za su iya faɗin ra’ayinsu a cikin aure?

16 Idan Jehobah ya ba mata gata masu yawa, ya kamata magidanta su tuntuɓi matansu kafin su yanke shawara mai muhimmanci. Za su zama masu hikima idan suka yi hakan. Nassosi sun ambata yanayi da yawa da mata suka yi magana ko kuma aikata ba ma tare da izinin magidantansu ba. Yi la’akari da yanayi biyu.

17 Saratu, matar uban iyali Ibrahim, ta ci gaba da gaya masa ya saki matarsa ta biyu da kuma ɗanta domin rashin biyayyarsu. “Abin nan fa ya yi wa Ibrahim ciwo ƙwarai,” amma ban da Allah. Jehobah ya gaya wa Ibrahim: “Kada wannan ya zama abu mai-zafi a gare ka saboda saurayin, da baiwarka kuma; cikin dukan abin da Saratu ta faɗa maka, sai ka ji maganarta.” (Far. 21:8-12) Ibrahim ya yi biyayya ga Jehobah, ya saurari muryar Saratu, kuma ya yi abin da ta ce.

18. Wane mataki ne Abigail ta ɗauka?

18 Ka yi la’akari kuma da Abigail, matar Nabal. Sa’ad da Dauda yake gudu domin kishin Sarki Saul, yana zama kusa da garken Nabal. Maimakon su ɗauki wani abu a cikin kayan mawadacin nan, Dauda da mutanensa sun tsare kayansa. Amma dai, Nabal “mutumin mai-tankiya ne mai-munanan ayyuka” ya kuwa yi “furji” ga mutanen Dauda. Mutumi ne “shaƙiyi” da kuma “wauta kuma gareshi.” Sa’ad da mutanen Dauda da ladabi suka roƙa abinci, Nabal ya ƙi. Yaya Abigail ta aikata sa’ad da ta ji abin da ya faru? Ba tare da gaya wa Nabal ba, ta “ta yi hanzari, ta ɗauki dunƙulen gurasa guda metin, da salkar ruwan anab biyu, da raguna biyar shiryayyu, da mudu biyar na tumammen hatsi, da nonnai na zabibi guda ɗari, da waina ta ɓaure guda metin” ta kuma ba wa Dauda da mutanensa. Abigail ta yi abin da yake da kyau ne? “Sai Ubangiji ya buga Nabal” in ji Littafi Mai Tsarki, “har ya mutu.” Daga baya Dauda ya auri Abigail.—1 Sam. 25:3, 14-19, 23-25, 38-42.

‘Macen da Ake Yabonta’

19, 20. Me yake sa mace ta zama abin yabo?

19 Nassosi ya yaba wa macen da take yin abubuwa a yadda Jehobah yake so. Littafin Misalai ya yaba wa “mace mai-tsarkin rai,” da cewa: “Tamaninta ya fi gaban lu’u lu’ai. Zuciyar mijinta tana dogara gareta, ba kuwa za shi rasa riba ba. Ta kan yi masa alheri ba mugunta ba dukan muddar ranta.” Ƙari ga haka, “ta kan buɗe bakinta da hikima: Kaidar nasiha kuma tana kan harshenta. Ta kan tsare al’amuran iyalinta da kyau, ba ta cin abincin ragonci. ’Ya’yanta su kan tashi, su ce da ita mai-albarka: Har mijinta kuma yana yabonta.”—Mis. 31:10-12, 26-28.

20 Me yake sa mace ta zama abin yabo? “Tagomashi yana da rikici, jamali kuma abin banza ne,” in ji Misalai 31:30, “amma mace mai-tsoron Ubangiji za a yabe ta.” Jin tsoron Jehobah ya haɗa da yin biyayya da zuciya ɗaya ga waɗanda Jehobah ya ba su shugabanci. “Kan mace kuma namiji ne,” kamar yadda “kan kowane namiji Kristi ne” kuma “kan Kristi kuma Allah ne.”—1 Kor. 11:3.

Ka Nuna Godiya don Kyautar Allah

21, 22. (a) Waɗanne dalilai ne ma’aurata Kiristoci suke da shi na nuna godiya ga kyautar Jehobah na aure? (b) Me ya sa za mu nuna biyayya ga tsarin Jehobah na iko da kuma shugabanci? (Duba akwati a shafi na 17.)

21 Kiristoci da suka yi aure suna da dalilai masu yawa na nuna godiya ga Allah! Za su yi aiki tare kamar ma’aurata masu farin ciki. Musamman za su iya yin godiya ga kyautar Allah na aure don zai ba su zarafin haɗa kansu da kuma yin tafiya tare da Jehobah. (Ruth 1:9; Mi. 6:8) Shi da ya kafa aure, ya san ainihin abin da ake bukata don a yi farin ciki a aure. Kullum kuna yin abubuwa a hanyarsa, kuma ‘farinciki na Ubangiji shi ne ƙarfinku,’ ko a cikin duniyar nan da take cike da damuwa.—Neh. 8:10.

22 Maigida Kirista da yake ƙaunar matarsa kamar kansa zai nuna shugabanci na ƙauna da kuma kulawa. Matarsa mai ibada za ta zama abar ƙauna, gama za ta tallafa masa kuma ta nuna masa ladabi sosai. Mafi muhimmanci, aurensu mai kyau zai girmama Allahnmu, Jehobah da ya cancanci mu yaba masa.

Ka Tuna?

• Menene tsarin Jehobah na shugabanci da kuma miƙa kai?

• Me ya sa ma’aurata za su girmama juna?

• Ta yaya mata Kirista mai bi za ta bi da maigidanta marar bi?

• Me ya sa magidanta za su tuntuɓi matansu kafin su yanke shawara mai muhimmanci?

[Akwati da ke shafi na 17]

Me Ya Sa Za Ka Daraja Masu Iko?

Jehobah ya kafa tsarin iko da kuma shugabanci a cikin halittunsa masu basira. An yi hakan ne domin amfanin halittun ruhu da kuma ’yan Adam. Wannan ya ba su zarafin nuna ’yancin zaɓinsu da kuma girmama Allah ta wurin yi masa bauta cikin jituwa da haɗin kai.—Zab. 133:1.

Ikilisiyoyin Kiristoci shafaffu sun fahimci iko da kuma shugabancin Yesu Kristi. (Afis. 1:22, 23) Wajen amincewa da ikon Jehobah, daga bisani “shi Ɗan da kansa kuma za ya sarayu ga wannan wanda ya sarayar da dukan kome a ƙarƙashin mulkinsa, domin Allah ya zama duka cikin duka.” (1 Kor. 15:27, 28) Saboda haka, ya dace mutane da suka keɓe kansu ga Allah suna haɗa kai ga tsarin shugabanci a cikin ikilisiya da kuma a iyali! (1 Kor. 11:3; Ibran. 13:17) Ta yin hakan, za mu amfani kanmu a matsayin waɗanda za su samu amincewar Jehobah da kuma albarkarsa.—Isha. 48:17.

[Hoton da ke shafi na 13]

Addu’a za ta taimaka wa mata Kirista ta nuna halaye na ibada

[Hotuna da ke shafi na 15]

Jehobah yana mutunta hakkin da mata suke da shi wajen yaɗa sakon Mulkin

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba