Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 5/15 pp. 28-32
  • Kada Ka Ɓata Zuciyar Ruhu Mai Tsarki Na Jehobah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kada Ka Ɓata Zuciyar Ruhu Mai Tsarki Na Jehobah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Abin da Bulus Yake Nufi
  • Ta Yaya Kirista Zai Iya Ɓata Zuciyar Ruhu?
  • Yadda Za Mu Guji Ɓata Zuciyar Ruhu
  • Wasu Hanyoyi da Za Mu Guji Ɓata Zuciyar Ruhu
  • Muna Bukatan Mu Kasance a Faɗake
  • Ka Yi Tafiya Bisa Ga Ruhu Kuma Ka Yi Rayuwar Da Ta Jitu Da Keɓe Kanka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Yadda Ruhun Allah Ya Yi Ja-gora A Ƙarni Na Farko Da Kuma A yau
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Me Zai Taimaka Idan Wani Naka Ya Rasu?
    Karin Batutuwa
  • Me Ya Sa Ruhun Allah Zai Yi Mana Ja-gora?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 5/15 pp. 28-32

Kada Ka Ɓata Zuciyar Ruhu Mai Tsarki Na Jehobah

“Kada kuwa ku ɓata zuciyar ruhu mai-tsarki na Allah, wanda aka hatimce ku a cikinsa.”—AFIS. 4:30.

1. Menene Jehobah ya yi ga miliyoyin mutane, kuma wane hakki ne suke da shi?

AKWAI wani abu na musamman da Jehobah ya yi wa miliyoyin mutane da suke zama a wannan duniya mai cike da matsaloli. Ya sa ya yiwu su kusace shi ta hanyar Ɗansa makaɗaici, Yesu Kristi. (Yoh. 6:44) Kana ɗaya daga cikin waɗannan mutanen idan ka riga ka keɓe kanka ga Allah kuma kana rayuwar da ta jitu da keɓe kanka. A matsayin wanda ya yi baftisma cikin sunan ruhu mai tsarki, kana da hakkin yin rayuwar da ta jitu da ruhun.—Mat. 28:19.

2. Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?

2 Mu da muke “shuka ga ruhu” muna yafa sabon mutum. (Gal. 6:8; Afis. 4:17-24) Amma manzo Bulus ya ba mu shawara kuma ya gargaɗe mu kada mu ɓata zuciyar ruhu mai tsarki na Allah. (Karanta Afisawa 4:25-32.) Yanzu za mu mai da hankali sosai ga wannan shawarar da manzon ya ba da. Menene Bulus yake nufi sa’ad da ya yi magana game da ɓata zuciyar ruhun Allah? A waɗanne hanyoyi ne wanda ya keɓe kansa ga Jehobah zai iya ɓata zuciyar ruhunsa? Kuma yaya za mu guji ɓata zuciyar ruhun Jehobah?

Abin da Bulus Yake Nufi

3. Ta yaya za ka bayyana ma’anar kalaman da ke Afisawa 4:30?

3 Da farko, ka lura da kalaman Bulus da suke rubuce a Afisawa 4:30. Ya rubuta: “Kada kuwa ku ɓata zuciyar ruhu mai-tsarki na Allah, wanda aka hatimce ku a cikinsa zuwa ranar fansa.” Bulus ba ya son ’yan’uwansa ƙaunatattu masu bi su saka ruhaniyarsu cikin haɗari. Da ruhun Jehobah ne aka ‘hatimce su zuwa ranar fansa.’ Ruhu mai tsarki na Allah hatimi ne a lokacin da kuma a yanzu don “abin da zai yi nan gaba” ga shafaffu masu aminci. (2 Kor. 1:22, Littafi Mai Tsarki) Hatimin yana nuna cewa su bayin Allah ne kuma za su yi rayuwa a sama. Adadin waɗanda aka hatimce su ne mutane 144,000.—R. Yoh. 7:2-4.

4. Me ya sa yake da muhimmanci mu guji ɓata zuciyar ruhun Allah?

4 Ɓata zuciyar ruhun zai iya zama mataki na farko na rasa ja-gorancin ruhun Allah a rayuwar Kirista. Abin da Dauda ya ce bayan ya yi zunubi da Bath-sheba ya nuna cewa hakan zai yiwu. Dauda ya tuba ya roƙi Jehobah: “Kada ka yashe ni daga gabanka; kada kuma ka ɗauke mini ruhunka mai-tsarki.” (Zab. 51:11) Shafaffun da suka kasance da “aminci har mutuwa” ne kawai za su karɓi “rawanin” rai na marar mutuwa a sama. (R. Yoh. 2:10; 1 Kor. 15:53) Kiristoci masu begen yin rayuwa a duniya su ma suna bukatan ruhu mai tsarki idan suna son su kasance da aminci ga Allah kuma su samu kyautarsa na rai bisa imani da hadayar fansa na Kristi. (Yoh. 3:36; Rom. 5:8; 6:23) Saboda haka, dole ne dukanmu mu guji ɓata zuciyar ruhu mai tsarki na Jehobah.

Ta Yaya Kirista Zai Iya Ɓata Zuciyar Ruhu?

5, 6. Ta yaya Kirista zai iya ɓata zuciyar ruhun Jehobah?

5 A matsayin Kiristoci da suka keɓe kai, za mu iya guje wa ɓata zuciyar ruhun. Hakan zai yiwu idan mun ‘ci gaba da tafiya bisa ga ruhu,’ ta yin hakan ba za mu ƙyale sha’awar jiki ta sha kanmu ba kuma ba za mu aikata halaye marar kyau ba. (Gal. 5:16, 25, 26) Amma hakan zai iya canjawa. Za mu iya ɓata zuciyar ruhun Allah sosai idan muka soma bijirewa a hankali, wataƙila ba tare da mun lura ba, ta wajen aikata halayen da Allah ya haramta a cikin hurarriyar Kalmarsa.

6 Idan mun ci gaba da yin abin da ya saɓa da ja-gorancin ruhu mai tsarki, za mu riƙa ɓata zuciyarsa da kuma Jehobah, Tushen wannan ruhun. Bincika Afisawa 4:25-32 zai nuna mana yadda za mu bi da kanmu, kuma zai iya taimaka mana mu guji ɓata zuciyar ruhun Allah.

Yadda Za Mu Guji Ɓata Zuciyar Ruhu

7, 8. Ka bayyana dalilin da ya sa za mu riƙa faɗin gaskiya.

7 Dole ne mu kasance masu faɗin gaskiya. A Afisawa 4:25, Bulus ya rubuta “Ku riƙa faɗi wa junanku da maƙwabtanku gaskiya, kuna kawarda ƙarya: gama mu gaɓaɓuwa ne na junanmu.” Tun da yake mu “gaɓaɓuwa ne na junanmu,” bai kamata mu zama masu cuku-cuku ba ko kuma mu yi ƙoƙarin yaudarar ’yan’uwa masu bi, gama hakan daidai ne da yi musu ƙarya. Duk mutumin da ya ci gaba da bin irin wannan tafarkin ba zai kasance da dangantaka da Allah ba.—Karanta Misalai 6:16-19.

8 Kalamai da ayyuka na cuku-cuku za su iya ɓata haɗin kai na ikilisiya. Saboda haka, ya kamata mu zama kamar amintaccen annabin nan Daniel, wanda mutane ba su samu illa ba a gare shi. (Dan. 6:4) Kuma ya kamata mu riƙa tuna shawarar da Bulus ya ba Kiristocin da suke da begen zuwa sama cewa kowacce gaɓa na “jikin Kristi” na da alaƙa da sauran gaɓoɓi kuma tana bukatan ta kasance da haɗin kai da shafaffu mabiya na gaskiya na Yesu. (Afis. 4:11, 12) Idan muna da begen yin rayuwa har abada cikin Aljanna a duniya, dole ne mu ma mu riƙa faɗin gaskiya, hakan zai daɗa kawo haɗin kai ga ’yan’uwancinmu na dukan duniya.

9. Me ya sa yake da muhimmanci mu bi gargaɗin da ke Afisawa 4:26, 27?

9 Dole ne mu yi tsayayya da Iblis, kada mu ba shi zarafin yi mana lahani a ruhaniya. (Yaƙ. 4:7) Ruhu mai tsarki yana taimaka mana mu yi tsayayya da Shaiɗan. Alal misali, za mu yi hakan ta wajen guje wa yin fushi ainun. Bulus ya rubuta: “Ku yi fushi, amma kada ku yi zunubi: kada rana ta faɗi kuna kan fushinku: kada kuwa ku ba Shaiɗan dama.” (Afis. 4:26, 27) Idan wani ya ba mu haushi, yin addu’a nan da nan a cikin zuciyarmu zai taimaka mana mu kasance da “sanyin ruhu,” kuma mu nuna kamewa maimakon mu yi abin da zai ɓata zuciyar ruhun Allah. (Mis. 17:27) Saboda haka, kada mu ci gaba da yin fushi kuma mu ba Shaiɗan zarafin sa mu yin mugunta. (Zab. 37:8, 9) Hanya ɗaya da za mu yi tsayayya da shi ita ce ta wajen sasanta jayayya da wuri cikin jituwa da shawarar da Yesu ya ba da.—Mat. 5:23, 24; 18:15-17.

10, 11. Me ya sa bai kamata mu yi sata ba ko kuma mu yi rashin gaskiya?

10 Bai kamata mu faɗa cikin gwajin yin sata ko kuma rashin gaskiya ba. Game da sata, Bulus ya rubuta: “Mai-yin sata kada ya ƙara yin sata: amma gwamma ya yi aiki, da hannuwansa yana aika abin da yake da kyau, domin shi kasance da abin da za shi ɗiba shi bayar ga wanda ya rasa.” (Afis. 4:28) Idan Kirista da ya keɓe kansa ya yi sata, zai ‘kama sunan Allah a banza’ ta wajen sa a kushe sunan. (Mis. 30:7-9) Ko talauci ba zai sa yin sata ya kasance abu mai kyau ba. Waɗanda suke ƙaunar Allah da maƙwabtansu sun fahimci cewa yin sata bai da kyau.—Mar. 12:28-31.

11 Bulus bai faɗi abin da bai kamata mu yi ba kawai, ya nuna abin da ya kamata mu yi. Idan muna rayuwa da kuma yin tafiya bisa ga ruhu mai tsarki, za mu yi aiki tuƙuru don mu kula da iyalinmu kuma mu samu ‘abin da za mu bayar ga wanda ya rasa.’ (1 Tim. 5:8) Yesu da manzaninsa sun ajiye kuɗi don su taimaka wa talakawa, amma Yahuda Iskariyoti maci amana ya sace wasu daga cikin kuɗin. (Yoh. 12:4-6) Hakika ba ruhu mai tsarki ba ne yake masa ja-gora. Ya kamata mu da ruhun Allah yake yi wa ja-gora “mu yi tasarrufin kirki cikin dukan abu,” kamar yadda Bulus ya yi. (Ibran. 13:18) Ta haka za mu guje wa ɓata zuciyar ruhu mai tsarki na Jehobah.

Wasu Hanyoyi da Za Mu Guji Ɓata Zuciyar Ruhu

12, 13. (a) Kamar yadda aka nuna a Afisawa 4:29, wane irin furci ne ya kamata mu guje wa? (b) Yaya ya kamata furcinmu ya kasance?

12 Dole ne mu kula da furcinmu. Bulus ya ce: “Kada kowane ruɓaɓen zance shi fita daga cikin bakinku, sai irin abin da ke mai-kyau garin ginawa yayinda ake bukata, domin shi ba da alheri ga waɗanda suke ji.” (Afis. 4:29) A nan ma, manzon ya gaya mana abin da ba za mu yi ba; kuma ya gaya mana abin da za mu riƙa yi. A ƙarƙashin ja-gorancin ruhu mai tsarki na Allah, za mu faɗi ‘abin da ke mai kyau garin ginawa, domin shi ba da alheri ga waɗanda suke ji.’ Bugu da ƙari, kada mu ƙyale “ruɓaɓen zance” ya fito daga bakinmu ba. An yi amfani da kalmar Helenanci da aka fassara “ruɓaɓe” don a kwatanta ruɓaɓɓen ’ya’yan itace, kifi, ko nama. Kamar yadda muke ƙyamar irin waɗannan abincin, ya kamata mu ƙi jinin furcin da Jehobah ba ya so.

13 Ya kamata furcinmu ya zama nagari, na alheri, “gyartace da gishiri.” (Kol. 3:8-10; 4:6) Ya kamata mutane su ga cewa mun bambanta sa’ad da suka saurari furcinmu. Saboda haka, bari mu taimaka wa mutane ta wurin yin furci da ke “mai-kyau garin ginawa.” Bari mu ji kamar mai zabura wanda ya raira waƙa: “Bari batutuwan bakina, da tunanin zuciyata, su zama abin karɓa a gareka, Ya Ubangiji, dutsena da mai-fansana.”—Zab. 19:14.

14. In ji Afisawa 4:30, 31, menene ya kamata mu kawar daga jikinmu?

14 Dole ne mu guji dukan ɗacin zuciya, fushi, zage-zage da dukan ƙeta. Bayan da ya yi gargaɗi game da ɓata zuciyar ruhu mai tsarki na Allah, Bulus ya rubuta: “Bari dukan ɗacin zuciya, da hasala, da fushi, da hargowa, da zage-zage, su kawu daga gare ku, tare da dukan ƙeta.” (Afis. 4:30, 31) A matsayin ’yan Adam ajizai, mu duka muna bukatan mu yi aiki tuƙuru don mu bi da tunaninmu da kuma ayyukanmu yadda ya kamata. Idan muka yi sakaci da “ɗacin zuciya, da hasala, da fushi,” za mu ɓata zuciyar ruhu na Allah. Hakan yake kuma idan muka ci gaba da tattara dukan laifofin da aka yi mana, muka nuna halin ƙiyayya, kuma muka ƙi sulhuntawa da wanda ya yi mana laifi. Idan muka soma ƙin gargaɗin da ke cikin Littafi Mai Tsarki, muna iya koyon halin da zai sa mu yi zunubi ga ruhu kuma hakan zai iya kai ga mugun sakamako.

15. Idan aka yi mana laifi, me ya kamata mu yi?

15 Muna bukatan mu kasance masu kirki, tausayi, da kuma gafartawa. Bulus ya rubuta: “Ku yi wa juna kirki, kuna tausayi, kuna yafe wa juna kamar yadda Allah ya yafe muku ta wurin Almasihu.” (Afis. 4:32, Littafi Mai Tsarki) Ko idan an ɓata mana rai sosai don abin da aka yi mana, muna bukatan mu gafarta, kamar yadda Allah yake gafarta mana. (Luk. 11:4) A ce wani ɗan’uwa ya faɗi wani mummunan abu game da mu. Don mu sulhunta al’amura, sai muka je muka same shi. Ya nuna baƙin ciki a kan abin da ya faru kuma ya nemi gafara. Za mu gafarta masa, amma muna bukatan mu yi fiye da haka. “Ba za ka ɗauka wa kanka fansa, ba kuwa za ka yi nukuran ’ya’yan jama’arka,” in ji Leviticus 19:18, “amma sai ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka: ni ne Ubangiji.”

Muna Bukatan Mu Kasance a Faɗake

16. Ka ba da misalin da ya nuna cewa za mu iya yin gyara don kada mu ɓata zuciyar ruhun Jehobah.

16 Ko a lokacin da muke mu kaɗai, za a iya jarraba mu mu yi wani abin da zai ɓata wa Allah rai. Alal misali, wataƙila ɗan’uwa ya daɗe yana sauraron kiɗa da bai dace da Kiristoci ba. Daga baya, lamirinsa ya damu ƙwarai don ƙin gargaɗin Littafi Mai Tsarki da ke cikin littattafan “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.” (Mat. 24:45) Yana iya yin addu’a game da wannan matsala kuma ya tuna da kalmomin Bulus da ke rubuce a Afisawa 4:30. Da yake ya ƙudurta cewa ba zai yi kome da zai ɓata zuciyar ruhun Allah ba, ya tsai da shawara ya guji kaɗe-kaɗe da ba su dace ba ga Kirista daga yanzu. Jehobah zai albarkaci halin da ɗan’uwan ya nuna. Saboda haka, bari a kowane lokaci mu guji ɓata zuciyar ruhun Allah.

17. Menene zai iya faruwa idan ba mu kasance a faɗake ba kuma ba ma yin addu’a?

17 Idan ba mu kasance a faɗake da yin addu’a ba, muna iya faɗa wa ƙazami ko mugun hali da zai sa mu ɓata zuciyar ruhu. Domin Ubanmu na samaniya yana yin amfani da ruhunsa mai tsarki don ya nuna halaye da suka jitu da halinsa, za a iya ɓata masa rai, ko kuma sa shi baƙin ciki, abin da ba za mu so mu taɓa yi ba. (Afis. 4:30) Marubuta Yahudawa na ƙarni na farko sun yi zunubi ta wajen faɗin cewa mu’ujizan Yesu daga wajen Shaiɗan ne. (Karanta Markus 3:22-30.) Waɗannan maƙiya na Kristi sun ‘saɓi ruhu mai tsarki’ kuma ta hakan sun yi zunubin da ba za a iya gafarta musu ba. Kada mu bari hakan ya same mu!

18. Ta yaya za mu iya sanin cewa ba mu yi zunubin da ba za a iya gafarta ba?

18 Tun da yake ba ma son mu yi kusa da yin zunubi da ba za a gafarta mana ba, muna bukatan mu tuna abin da Bulus ya ce game da ɓata wa ruhun zuciya. Amma idan muka yi zunubi mai tsanani kuma fa? Idan muka tuba, kuma dattawa suka taimaka mana, za mu iya kammala cewa Allah ya gafarta mana, kuma ba mu yi zunubi ba ga ruhu mai tsarki. Da taimakon Allah, za mu iya guje wa ɓata zuciyar ruhun a kowace hanya.

19, 20. (a) Waɗanne abubuwa ne muke bukatan mu guje wa? (b) Ya kamata mu ƙuduri aniyar yin menene?

19 Ta hanyar ruhunsa mai tsarki, Allah ya ɗaukaka ƙauna, farin ciki, da haɗin kai na mutanensa. (Zab. 133:1-3) Saboda haka, ya kamata mu guji ɓata zuciyar ruhun ta wajen yin mugun gulma ko kuma ta wajen faɗin abubuwa da zai sa a raina makiyayan da ruhu ya naɗa. (A. M. 20:28; Yahu. 8) Maimakon haka, ya kamata mu ɗaukaka haɗin kai da kuma daraja juna a cikin ikilisiya. Hakika, bai kamata mu kafa rukuni tsakanin mutanen Allah ba. Bulus ya rubuta: “’Yan’uwa, ina roƙonku, ta wurin sunan Ubangijinmu Yesu Kristi, dukanku ku yi magana ɗaya, kada tsatsaguwa su kasance a tsakaninku; amma ku zama cikakku cikin hankali ɗaya da shasara ɗaya.”—1 Kor. 1:10.

20 Jehobah yana shirye kuma zai iya taimaka mana mu guji ɓata zuciyar ruhunsa. Bari mu ci gaba da yin addu’a don samun ruhu mai tsarki kuma mu ƙuduri aniya kada mu ɓata zuciyarsa. Bari mu ci gaba da “shuka ga ruhu,” mu riƙa biɗar ja-gorarsa a yanzu da kuma har abada.

Yaya Za Ka Amsa?

• Menene ɓata zuciyar ruhun Allah yake nufi?

• Ta yaya mutumin da ya keɓe kansa ga Jehobah zai iya ɓata zuciyar ruhun Allah?

• A waɗanne hanyoyi ne za mu guji ɓata zuciyar ruhu mai tsarki?

[Hoton da ke shafi na 30]

Ku sulhunta jayayya da wuri

[Hoton da ke shafi na 31]

Wannene cikin wannan ’ya’yan itacen ya fi dacewa da furcinka?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba