Menene Allah Yake Yi?
‘Ya [Jehobah], don me ka tsaya daga nesa? Don me ka ɓoye kanka a lokatan wahala?’a—ZABURA 10:1.
DA ZARAR ka duba kan maganar jarida, za ka san cewa muna cikin ‘lokatan wahala.’ Kuma sa’ad da bala’i ya faru a gida—sa’ad da wani laifin da aka aika ya shafe mu, haɗari mai tsanani, ko kuma sa’ad da wanda muke ƙauna ya mutu, za mu iya tambaya, Allah yana gani kuwa? Yana kula kuwa? Ya wanzu kuwa da gaske?
Amma dai, kana tunanin cewa za mu iya kasancewa da ra’ayin da bai dace ba game da Allah kuwa? Alal misali: Ka yi tunanin ƙaramin yaron da yake fushi domin mahaifinsa ya tafi wajen aiki. Yaron ya yi kewar babansa kuma yana son ya dawo gida. Yaron ya ji kamar babu mai kula da shi. Gabaki ɗayan ranar, ya ci gaba da tambaya, “Wai ina baba yake ne?”
Za mu iya gano matsalar da ke tunanin yaron. A wannan lokacin, mahaifinsa ya fita yin aiki ne don yi wa iyalin gabaki ɗaya tanadi. Shin tunaninmu zai iya kasancewa karkatacce kamar na yaron nan sa’ad da muka ce, “Ina Allah yake ne”?
Alal misali, wasu za su so Allah ya zama mahukuncin da zai hukunta masu laifi nan da nan. Wasu kuma suna ɗaukan Allah a matsayin Baban Kirsimati da ke sama, wanda matsayinsa shi ne ya ba da kyauta, wato, aiki, abokin aure, ko kuma katin cin caca.
Dukan waɗannan tunani biyu suna nufin cewa idan Allah bai yi adalci ba nan da nan ko kuma idan bai ba mu abin da muka roƙe shi ba, hakan na nufin cewa bai damu da wahalarmu ba kuma bai san bukatunmu ba. Amma babu abin da ya fi gaskiya! Gaskiyar ita ce, a yanzu, Jehobah Allah yana shirin yi wa dukan ’yan Adam tanadi, amma ba a hanyar da mutane da yawa suke roƙo ba.
Amma, menene Allah yake yi? Don amsa wannan tambayar, muna bukatan mu koma baya zuwa farkon tarihin ’yan Adam sa’ad da dangantakar mutane da Allah ta ɓace sosai, amma bai gagari gyara ba.
Mugun Sakamako na Zunubi
Ka yi tunanin gidan da ya yi shekaru da lalacewa. Rufin gidan ya faɗa ciki, kofofin sun kakkarye, kuma bangon waje ya lalace. Akwai lokacin da wannan gidan yake da kyau, amma yanzu ya lalace. Saboda tsananin lalacewar da gidan ya yi, gyara shi ba zai yi sauƙi ba, ba za a iya yin hakan cikin dare ɗaya ba.
Yanzu ka yi la’akari da ɓarnar da aka yi wa ’yan Adam shekaru dubu shida da suka wuce sa’ad da wani ruhun da ba a gani, Shaiɗan, ya ruɗi Adamu da Hauwa’u su yi tawaye ga Allah. Kafin wannan aukuwar, waɗannan ma’aurata na farko sun more koshin lafiya da begen yin rayuwa na har abada tare da zuriyoyin yaransu. (Farawa 1:28) Sa’ad da suka yi zunubi, kamar dai Adamu da Hauwa’u sun ɓata iyalin ’yan Adam da ba su haifa ba tukun.
Kada ka raina sakamako marar kyau da yin tawaye yake jawowa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kamar yadda zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum ɗaya [Adamu], mutuwa kuwa ta wurin zunubi.” (Romawa 5:12) Bayan mutuwa, zunubi ya raunana dangantakarmu da Mahaliccinmu kuma ya shafe mu a zahiri, a tunani da kuma a motsin rai. A sakamakon haka, yanayinmu ya yi kama ne da gidan da ya lalace. Ayuba mutum mai aminci ya kammala yanayinmu sa’ad da ya kwatanta cewa mutum ‘kwanakinsa kaɗan ne, cike da wahala kuma.’—Ayuba 14:1.
Amma Allah ya yi watsi ne da ’yan Adam bayan Adamu da Hauwa’u sun yi zunubi? A’a! Hakika, tun daga lokacin har yanzu, Ubanmu na samaniya yana ta yin aiki a madadin ’yan Adam. Don mu daɗa yin godiya ga abubuwan da yake yi mana, ka yi la’akari da matakai uku masu muhimmanci da ake bukata don sake gyara gida da kuma yadda kowanne cikin waɗannan ya shafi abin da Allah ya yi don ya ceto ’yan Adam.
1 Bayan an bincika gidan da ya lalace, mai shi zai yanke shawarar ko ya gyara shi ko kuma ya rushe shi.
Nan da nan bayan tawayen da aka yi a Adnin, Jehobah Allah ya sanar da nufinsa na ’yantar da ’yan Adam. Ya ce wa ruhun da ba a gani da ya rinjaye su: “Tsakaninka da macen kuma zan kafa magabtaka, da tsakanin zuriyarka da zuriyarta kuma: shi za ya ƙuje kanka, kai kuma za ka ƙuje duddugensa.”—Farawa 3:15.
Da waɗannan kalamai, Jehobah ya yi alkawarin halaka wanda ya jawo tawayen a Adnin. (Romawa 16:20; Ru’ya ta Yohanna 12:9) Ƙari ga hakan, Jehobah ya annabta cewa wani “zuriya” da zai bayyana a nan gaba zai ceto ’yan Adam daga zunubi.b (1 Yohanna 3:8) Waɗannan alkawuran sun bayyana wata muhimmiyar gaskiya: Allah zai gyara, ba halaka, halittarsa ba. Amma mai da ’yan Adam irin yanayin da suke a farko zai ɗauki lokaci.
2 Mai zane ya zana fasalin ginin da za a yi gabaki ɗaya.
Jehobah Allah ya ba Isra’ilawa tsarin dokoki kuma ya zana musu haikalin da za su riƙa bauta masa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Inuwar al’amuran da ke zuwa ne.” (Kolosiyawa 2:17) Kamar zanen gida, suna wakiltan wani abu mafi girma.
Alal misali, Isra’ilawa suna yin hadayun dabba don a gafarta zunubansu. (Levitikus 17:11) Hakan yana nuni ne ga hadaya mafi girma da za a yi ƙarnuka da yawa a gaba, wato, hadayar da za ta ba ’yan Adam ceto na ainihi.c Ainihin fasalin mazauni da haikalin da Isra’ilawa suke bauta suna wakiltan matakan da Almasihun da aka yi alkawarinsa zai ɗauka, daga mutuwarsa na hadaya zuwa komawarsa cikin sama.—Duba taswiran da ke shafi na 7.
3 An zaɓi maginin da zai bi zanen kuma ya gyara ginin.
Yesu ne Almasihun da aka yi alkawarinsa wanda zai bi fasalin da aka kafa ta hanyar hadayun Isra’ilawa kuma zai ba da ransa don ya ceto ’yan Adam. Hakika, Yohanna Mai Yin Baftisma ya kira Yesu “Ɗan rago na Allah wanda yana ɗauke da zunubin duniya.” (Yohanna 1:29) Yesu ya karɓi aikin da aka ba shi da dukan zuciya. Ya ce: “Gama na sauko daga sama, ba domin in yi nufin kaina ba, amma nufin wanda ya aiko ni.”—Yohanna 6:38.
Nufin Allah ga Yesu ya haɗa da “bada ransa kuma abin fansar mutane dayawa” da kuma yi wa mabiyinsa alkawarin Mulki. (Matta 20:28; Luka 22:29, 30) Mulkin nan hanya ce da Allah zai cim ma nufinsa ga ’yan Adam. Ana kiran saƙon Mulkin Allah “bishara” domin ya bayyana cewa Allah ya kafa gwamnati a sama da zai gudanar da ayyuka a duniya!—Matta 24:14; Daniyel 2:44.d
Aikin Maidowa Yana Ci Gaba
Kafin ya koma sama, Yesu ya umurci mabiyinsa: “Ku almajirtarda dukan al’ummai, kuna yi masu baftisma zuwa cikin sunan Uba da na Ɗa da na Ruhu Mai-tsarki . . . Ga shi kuwa ina tare da ku kullayaumi har matuƙar zamani.”—Matta 28:19, 20.
Saboda haka, mutuwar Yesu ba zai dakatar da maida ’yan Adam cikin yanayin da suke a dā ba. Zai ci gaba har “matuƙar zamani,” lokacin da Mulkin Allah zai soma yin sarauta a duniya. Lokacin ya zo. Mun san da hakan domin alamun da Yesu ya ba da game da “matuƙar zamani” suna cika yanzu.e—Matta 24:3-14; Luka 21:7-11; 2 Timotawus 3:1-5.
A yau, Shaidun Jehobah a ƙasashe 236 suna yin biyayya ga umurnin Yesu na yin wa’azin bishara ta Mulkin Allah. Hakika, an tsara mujallar da kake karantawa yanzu don ta taimaka maka ka koyi ƙarin abubuwa game da wannan Mulkin da abubuwan da zai cim ma. A cikin shafi na 2 na dukan talifin Hasumiyar Tsaro, za ka ga wannan kalami: “Wannan mujallar . . . tana yi wa mutane ta’aziyya cewa Mulkin Allah, wanda gwamnati ce ta gaske a samaniya, ba da daɗewa ba za ta kawo ƙarshen dukan mugunta kuma ta mai da duniya ta zama aljanna. Tana sa a ba da gaskiya ga Yesu Kristi, wanda ya mutu domin mu sami rai madawwami kuma wanda a yanzu shi ne Sarkin Mulkin Allah.”
Babu shakka, a yanzu wataƙila kana jin labarai game da hare-haren ta’addanci ko bala’o’i, ko kuma kana fuskantar matsaloli na kai. Amma yin nazarin Littafi Mai Tsarki zai tabbatar da kai cewa Allah bai yi watsi da ’yan Adam ba. Akasin haka, “ba shi da nisa da kowane ɗayanmu.” (Ayyukan Manzanni 17:27) Kuma alkawarinsa na maido da abin da iyayenmu na fari suka ɓatar zai yi nasara.—Ishaya 55:11.
[Hasiya]
a Jehobah ne sunan Allah kamar yadda aka bayyana cikin Littafi Mai Tsarki.
b Don samun bayani dalla-dalla game da Farawa 3:15, ka duba babi na 19 na littafin nan Ka Kusaci Jehovah, shaidun Jehobah ne suka wallafa.
c Don ƙarin bayani, ka duba babi na 5 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
d Don ƙarin bayani game da Mulkin Allah, ka duba babi na 8 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
e Don ƙarin bayani, ka duba babi na 9 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
[Taswira/Hotuna da ke shafi na 7]
(Don ganin cikakken rubutun, ka duba littafin)
“Mai-kama da na Gaskiya ga Zancen Fasali”—Abin da Mazaunin Yake Wakilta
BAGADI
Amincewa da Allah ya yi ya karɓi hadayar Yesu.—IBRANIYAWA 13:10-12.
BABBAN FIRIST
Yesu.—IBRANIYAWA 9:11.
1 A Ranar Kafara, babban firist yakan yi hadaya domin zunubin mutane.—LEVITIKUS 16:15, 29-31.
1 A ranar 14 ga Nisan, 33 A.Z., Yesu ya yi hadaya da ransa a madadinmu.—IBRANIYAWA 10:5-10; 1 YOHANNA 2:1, 2.
MAI TSARKI
Sake haihuwar Yesu a matsayin ɗa na ruhaniya na Allah yayin da yake duniya.—MATTA 3:16, 17; ROMAWA 8:14-17; IBRANIYAWA 5:4-6.
LABULEN
Jikin Yesu, abin da ya raba rayuwar duniya da ta sama.—1 KORINTIYAWA 15:44, 50; IBRANIYAWA 6:19, 20; 10:19, 20.
2 Babban firist yakan shiga bayan labulen da ya raba Mai Tsarki daga Mafi Tsarki.
2 Bayan tashinsa daga matattu, Yesu ya wuce “bayan labule na biyu,” ta wajen tashi zuwa sama domin “shi bayyana a gaban fuskar Allah sabili da mu.”—IBRANIYAWA 9:24-28.
MAFI TSARKI
Sama.—IBRANIYAWA 9:24.
3 Da zarar yana cikin Mafi Tsarkin, babban firist zai yayyafa jinin hadayar a gaban akwatin alkawari.—LEVITIKUS 16:12-14.
3 Ta wajen miƙa darajar jininsa, Yesu ya yi tanadin tabbatacciyar kafara domin zunubanmu.—IBRANIYAWA 9:12, 24; 1 BITRUS 3:21, 22.