Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 7/1 p. 3
  • Ina Allah Yake?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ina Allah Yake?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Bala’i—Me Ya Sa Suka Yi Yawa Haka?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Allah Yana Yi Mana Horo Ne?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ina Duniya Ta Dosa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 7/1 p. 3

Ina Allah Yake?

A ranar 11 ga Satumba, shekara ta 2001: Da ƙarfe 8:46 na safe, jirgin sama mai ɗauke da fasinjoji ya faɗa wa dogon gini da ke arewa na Cibiyar Kasuwanci ta Duniya a Amirka, wannan shi ne hari na farko na ta’addanci cikin hare-haren da aka shirya. Cikin mintoci 102 bayan aukuwar, aƙalla mutane dubu uku ne suka mutu.

26 ga Disamba, 2004

Girgizar ƙasa mai tsanani a cikin Tekun Indiya ta tayar da mugun rakumin ruwa da ya shafi ƙasashe sha ɗaya, har da Afirka da ke da nisan kusan mil dubu uku daga wurin. A cikin rana guda, mutane dubu ɗari da hamsin suka rasa rayukansu ko kuma suka ɓace, kuma fiye da miliyan suka rasa gidajensu.

A ranar 1 ga Agusta, shekara ta 2009: Wani mutum mai shekara 42 yana wasa da jirgin ruwa mai gudu sosai tare da ɗansa ɗan shekara biyar, sa’ad da suka yi karo da matsayar jirgi da aka yi da katako. Baban ya mutu. Ɗansa bai mutu ba sai washegari. Wata ’yar’uwarsa da ke cike da baƙin ciki ta ce, “Na yi zaton cewa mu’ujiza za ta faru kuma ya warke.”

Idan ka karanta littafi ka ga hare-haren ta’addanci ko bala’o’i ko sa’ad da kai da kanka ka fuskanci bala’i, ka taɓa tunanin ko Allah yana ganin abin da ke faruwa kuwa? Ka yi mamakin ko ya yi watsi da mu ne? Littafi Mai Tsarki ya ba da amsa mai ƙarfafawa, kamar yadda za mu gani.

[Wuraren da Aka Ɗauko hoto da ke shafi na 3]

© Dieter Telemans/Panos Pictures

PRAKASH SINGH/AFP/Getty Images

© Dieter Telemans/Panos Pictures

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba