Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 4/1 pp. 26-29
  • Shin Littafi Mai Tsarki Ya Ba da Dukan Bayani Game da Yesu Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Shin Littafi Mai Tsarki Ya Ba da Dukan Bayani Game da Yesu Kuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • A Wanne Lokaci Ne Aka Rubuta Nassosin Helenanci na Kirista, Kuma Wanene Ya Rubuta Shi?
  • Wanene Ya Zaɓi Littattafan?
  • Me Ya Sa Littattafan Afokirifa Ya Fita Dabam?
  • Marubutan Littafi Mai Tsarki Sun Yi Gargaɗi Cewa Masu Ridda Za Su Taso
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 4/1 pp. 26-29

Shin Littafi Mai Tsarki Ya Ba da Dukan Bayani Game da Yesu Kuwa?

Yesu bai mutu a Golgota ba, kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya ce ya yi ne, amma ya tsira? Shin ya auri Maryamu Magadaliya kuma ya samu yara daga wurinta? Ko kuwa shi marar fara’a ne wanda ya ƙi kowace irin annashuwar rayuwa na duniya? Zai yiwu a ce ya koyar da abubuwan da suka bambanta da abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki da muke karantawa?

IRIN waɗannan jita–jitar sun zama ruwan dare a kwanakin nan, domin ana nuna su a wasanni da kuma littattafai. Bayan wannan ƙagaggen labarin da ba gaskiya ba ne, akwai littattafai da yawa da suka mai da hankali ga rubutun Afokirifa daga ƙarni na biyu da na uku A.Z., wanda aka ce wai ya bayyana gaskiya cewa an cire Yesu a Linjila. Shin waɗannan da’awar gaskiya ne kuwa? Za mu iya tabbata cewa Littafi Mai Tsarki ya faɗi dukan gaskiya game da Yesu?

Don Amsa waɗannan tambayoyin, yana da amfani mu yi la’akari da abubuwa uku masu muhimmanci. Na farko ya dace mu san gaskiya game da mazajen da suka rubuta Linjila da kuma lokacin da suka rubuta ta, na biyu, ya dace mu san wanda ya tsara littattafan Nassosi da yadda aka yi hakan, na uku kuma, muna bukatar wasu bayanai game da littafin Afokirifa da kuma yadda suka bambanta da karɓaɓɓun littattafai.a

A Wanne Lokaci Ne Aka Rubuta Nassosin Helenanci na Kirista, Kuma Wanene Ya Rubuta Shi?

Wasu sun faɗa cewa an rubuta Linjilar Matta shekaru takwas bayan mutuwar Kristi, wato, kusan 41 A.Z. Masana da yawa sun faɗa cewa an rubuta ta shekaru da yawa bayan mutuwarsa, amma an amince cewa an rubuta dukan littattafai na Nassosin Helenanci na Kirista a ƙarni na farko A.Z.

Waɗanda suka shaida rayuwa, mutuwa, da tashin Yesu daga matattu suna raye a lokacin, kuma za su iya tabbatar da Linjila. Kuma za su iya tono kowacce kuskuren da aka yi. Farfesa F. F. Bruce ya lura: “Abu ɗaya mafi ƙarfi game da wa’azin da manzanni suka yi shi ne gaba gaɗi da suke da shi, ba sa ce ‘Mun shaida waɗannan abubuwan ba,’ amma ‘yadda ku kuma kun sani.’ (Ayyukan Manzanni 2:22).”

Waɗanne mutane ne suka rubuta Nassosin Helenanci na Kirista? Sun haɗa da wasu cikin manzannin Yesu sha biyu. Waɗannan da sauran marubutan Littafi Mai Tsarki, kamar su Yaƙub, Yahuda, da wataƙila, Markus sun halarci Fentakos na 33 A.Z. sa’ad da aka kafa ikilisiya na Kirista. Dukan marubutan, haɗe da Bulus, suna da dangantaka sosai da hukumar mulki na ikilisiyar Kirista na farko, wanda ya haɗa da manzanni da kuma dattawa a Urushalima.—Ayyukan Manzanni 15:2, 6, 12-14, 22; Galatiyawa 2:7-10.

Yesu ya umurce almajiransa su yi aikin wa’azi da koyarwar da ya soma. (Matta 28:19, 20) Har ma ya ce: “Wanda ya ji ku ya ji ni.” (Luka 10:16) Ƙari ga hakan, ya yi musu alkawari cewa ruhu mai tsarki na Allah, zai ba su ƙarfin da suke nema don yin wannan aikin. Saboda haka idan manzanni ko abokan aikinsu suka yi rubutu, wato, mazajen da a bayyane yake sosai cewa Allah ya albarkace su da ruhu mai tsarki, Kiristocin zamanin dā suna amincewa da irin waɗannan littattafai.

Wasu marubutan Littafi Mai Tsarki sun shaida cewa abokansu da suka rubuta Littafi Mai Tsarki ma an hure su. Alal misali, manzo Bitrus ya yi magana game da wasiƙar Bulus kuma ya bayyana su cikin “sauran Littattafai.” (2 Bitrus 3:15, 16) Bulus kuma da kansa ya san cewa Allah ya hure manzanni da sauran annabawa Kirista.—Afisawa 3:5.

Saboda haka, Linjila tana da babban tabbaci cewa ingantacciya ce. Ba tatsuniya da almara ba ne. Tarihi da aka rubuta sosai ne, wanda waɗanda suka gani kuma aka hure su ta ruhu mai tsarki suka rubuta.

Wanene Ya Zaɓi Littattafan?

Wasu mawallafa suna da’awa cewa wani coci mai iko sosai ne ya zaɓi littattafai da suka ƙunshi Nassosin Helenanci na Kirista a ƙarƙashin ja-gorancin Sarki Constantine. Amma, ba haka yake ba.

Alal misali, ka lura da bin da Farfesa na Tarihin Coci Oskar Skarsaune ya ce: “Limaman coci ko kowa bai taɓa faɗa littattafai da ya kamata a zaɓa cikin Sabon Alkawari, ko wannene bai kamata a zaɓa ba . . . An zaɓi littattafan a hanya da ya dace: Littattafai da aka san cewa manzanni ko abokan aikinsu ne suka rubuta a ƙarni na farko A.Z. ne aka zaɓa. An saka sauran rubutu, wasiƙu, ko ‘linjila’ da aka rubuta daga baya . . . An kammala wannan abun shekaru da yawa kafin zamanin Constantine da kuma kafawar cocinsa. Kiristocin da aka tsananta wa ne suka zaɓa Sabon Alkawari ba cocin da suke amfani da iko ba.”

Ken Berding, farfesan da ke nazarin Nassosin Helenanci na Kirista, ya ba da wannan bayani game da yadda aka samo littattafai na Littafi Mai Tsarki: “Cocin ba su zaɓa littattafai ba, amma ya fi dacewa a ce cocin sun amince da littattafai da Kiristoci sun riga sun amince kamar ainihi Kalmar Allah.”

Amma dai, Kiristocin ƙarni na farko ne kaɗai suka zaɓi littattafan nan? Littafi Mai Tsarki ya faɗar mana cewa wani abu mafi muhimmanci da kuma iko ne ya jawo hakan.

Kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya nuna, wata baiwar ruhu da aka ba ikilisiyar Kiristoci na dā shi ne “rarrabawar ruhohi.” (1 Korintiyawa 12:4, 10) An ba wasu cikin waɗannan Kiristoci iko sosai don su fahimci bambancin da ke tsakanin kalamai da Allah ya hure da wanda bai hure ba. Kiristoci a yau za su iya samun tabbaci cewa Nassosin da ke Littafi Mai Tsarki karɓaɓɓu ne da hurarru.

Hakika, an zaɓa littattafan a zamanin dā a ƙarƙashin ja-gorancin ruhu mai tsarki. Daga kusan ƙarshen ƙarni na biyu A.Z., wasu marubuta sun yi magana game da tabbaci cewa littattafan Littafi Mai Tsarki karɓaɓɓu ne. Waɗannan marubutan, ba su zaɓa littattafan ba, amma dai sun tabbatar da abin da Allah ya riga ya amince da ta wakilansa, waɗanda suke cikin ja-gorancin ruhunsa.

Tarin littattafai na dā ma sun ba da tabbaci game da littattafai waɗanda karɓaɓɓu ne a yau. Akwai fiye da tarin littattafai dubu biyar na Nassosin Helenanci a yare na ainihi, haɗe da wasu na ƙarni na biyu da uku. Littattafan nan ne, ba na Afokirifa ba ne, aka ɗauka a matsayin karɓaɓɓu a ƙarni na farko A.Z. don haka aka kofa da kuma rarraba shi.

Amma dai, tabbacin da ke cikin Littafi Mai Tsarki ne tabbaci mafi muhimmanci cewa hurarre ne. Karɓaɓɓun littattafan sun jitu da “sahihiyan kalmomi.” (2 Timotawus 1:13) Suna motsa masu karatu su ƙaunaci, su bauta, kuma su yi wa Jehobah hidima, kuma sun ba da gargaɗi game da camfi, sihiri da bautar halitta. Sun jitu da tarihi kuma suna ɗauke da annabci. Kuma suna ƙarfafa masu karantawa su ƙaunaci ’yan’uwansu. Littattafan Nassosin Helenanci na Kirista suna ɗauke da waɗannan abubuwan na musamman. Za a iya ce hakan ma game da littattafan afokirifa kuwa?

Me Ya Sa Littattafan Afokirifa Ya Fita Dabam?

Littattafan afokirifa sun bambanta ƙwarai da karɓaɓɓun littattafai. An rubuta waɗannan littattafan afokirifa tsakanin 150 zuwa 300 A.Z., shekaru da yawa bayan an rubuta karɓaɓɓun littattafan. Suna magana game da Yesu da Kiristanci da basu jitu da hurarrun Nassosi ba.

Alal misali, Linjilar Toma a littafin afokirifa ta yi magana marar gaskiya da yawa game da Yesu, kamar cewa Yesu zai mai da Maryamu na miji don ya yiwu ta shiga Mulkin sama. Littafin labarin jariri na Toma ya bayyana sa’ad da Yesu yake jariri yana yin fushi sosai har ma ya kashe wani yaro da ganga. Littafin afokirifa na Ayyukan Bulus da Ayyukan Bitrus sun nanata cewa a ƙi kowanne irin jima’i gabaki ɗaya kuma ya ce manzanni sun umurci mata su saki mazajensu. Linjilar Yahuda ya nuna Yesu yana wa almajiransa dariya saboda addu’a da suka yi wa Allah kafin su ci abinci. Irin waɗannan bayanan sun saɓa da abin da ke cikin karɓaɓɓun littattafai.—Markus 14:22; 1 Korintiyawa 7:3-5; Galatiyawa 3:28; Ibraniyawa 7:26.

Littattafan afokirifa da yawa suna koyar da imanin Gnostic, wanda ya ce Mahalicci, Jehobah ba Allah mai kyau ba ne. Sun kuma amince cewa tashin matattu ba gaskiya ba ne, kuma dukan abin duniya mugunta ce, kuma ya ce Shaiɗan ne ya sa a yi aure da kuma haifi yara.

Littattafan afokirifa da yawa sun yi ƙaulin Littafi Mai Tsarki amma ba gaskiya ba ne. Shin an haɗa baki ne an cire waɗannan littattafai daga cikin Littafi Mai Tsarki? Wani masani na littafin afokirifa M. R. James, ya ce: “Zancen cewa an cire su daga cikin littattafan Sabon Alkawari bai taso ba, amma sun saɓa da karɓaɓɓun littattafai sosai.”

Marubutan Littafi Mai Tsarki Sun Yi Gargaɗi Cewa Masu Ridda Za Su Taso

A cikin karɓaɓɓun littattafan, za mu ga gargaɗi da yawa game da masu ridda da za su taso kuma su ɓata ikilisiyar Kirista. Hakika, wannan ridda ta riga ta soma a ƙarni na farko, amma manzanni ba su ƙyale ta yaɗu ba sosai. (Ayyukan Manzanni 20:30; 2 Tasalonikawa 2:3, 6, 7; 1 Timotawus 4:1-3; 2 Bitrus 2:1; 1 Yohanna 2:18, 19; 4:1-3) Irin waɗannan gargaɗin sun yi magana game da littattafai da za su taso bayan mutuwar manzanni, rubutun da sun saɓa da koyarwar Yesu.

Hakika, irin waɗannan littattafan za su iya kasance tsofaffi da masu amfani ga wasu masana da ’yan tarihi. Amma ka yi la’akari da wannan: A ce masana sun tara littattafan ƙarya da aka rubuta a yau, wataƙila sun samo su ne daga jaridun gulma da na addinan tawaye da sihiri, sai suka ajiye ta a cikin ma’adana? Shin idan ta daɗe sosai, hakan za ta sa ta kasance littafin gaskiya da tabbatacce kuwa? Bayan shekaru dubu ɗaya da ɗari bakwai, ƙaryace-ƙaryace da wofin da ke cikin littattafan za su zama gaskiya ne don dai sun daɗe sosai?

Hakika a’a! Hakan ya yi daidai da da’awar cewa Yesu ya auri Maryamu Magadaliya da kuma wasu baƙin kalamai da ke littattafan afokirifa. Ina amfanin dogara ga waɗannan littattafai da ba gaskiya ba, musamman ma da yake akwai tabbatattu? Dukan abubuwan da Allah yake son mu sani game da Ɗansa suna cikin Littafi Mai Tsarki, littafin da za mu iya dogara da shi.

[Hasiya]

a Akwai littattafai sittin da shida waɗanda an san da su kamar littattafan Littafi Mai Tsarki kuma sun tabbatar da mu cewa hurarru ne daga wurin Allah kuma ainihi sashe ne na Kalmar Allah.

[Zane/Hoton da ke shafi na 26]

[Don ganin cikakken rubutun, ka duba littafin]

RAYUWAR YESU RUBUTUN SASHEN HELENANCI RUBUTUN AIKIN

NA LITTAFI MAI TSARKI AFOKIRIFA

2 K.Z. 33 A.Z. 41 98 130 300

[Inda Aka Ɗauko]

Kenneth Garrett/National Geographic Image Collection

[Hoton da ke shafi na 28]

Manzo Bulus ya yi mu’ujizai, har da tayar da matattu, kuma hakan ya ba da tabbaci cewa ruhu mai tsarki na Allah yana yi wa shi da rubutunsa ja–gora

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba