Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 4/1 pp. 30-31
  • Yesu Ya Koyi Yin Biyayya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yesu Ya Koyi Yin Biyayya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Yesu Ya Yi Biyayya a Kowane Lokaci
    Ku Koyar da Yaranku
  • Abin da Misalin Maryamu Ya Koya Mana
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • “Ga ni, Baiwar Ubangiji”
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Ta Yi ‘Bimbini a Cikin Zuciyarta’
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 4/1 pp. 30-31

Ku Koyar Da Yaranku

Yesu Ya Koyi Yin Biyayya

YANA kasance ma da wuya wasu lokatai ka yi biyayya kuwa?—a Idan kana hakan ba abun mamaki ba ne. Kowa a wasu lokatai suna ganin wuyar yin biyayya. Ka san kuwa cewa har Yesu ma ya koyi yin biyayya?—

Ka san wanda ya kamata dukan matasa su yi wa biyayya kuwa?— E, mamarmu da babanmu. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku yi biyayya da waɗanda suka haife ku cikin Ubangiji.” (Afisawa 6:1) Wanene uban Yesu?— Jehobah Allah, kuma shi ma Ubanmu ne ma. (Matta 6:9, 10) Amma idan ka ce Yusufu ne uban Yesu, Maryamu kuma mamarsa ce ka yi daidai. Ka san yadda suka zama iyayensa kuwa?—

Mala’ika Jibra’ilu ya gaya wa Maryamu cewa za ta zama mahaifiya ko da ba ta sadu da na miji ba. Jehobah ya sa hakan ya yiwu ta yin babbar mu’ujiza. Jibra’ilu ya bayyana wa Maryamu: “Ikon Maɗaukaki kuma za ya inuwantadda ke: domin wannan kuwa abin nan da za a haifa, za a ce da shi mai-tsarki, Ɗan Allah.”—Luka 1:30-35.

Allah ya ɗauki rayuwar Ɗansa daga sama kuma ya saka shi cikin Maryamu. Sai wannan rai ya yi girma cikinta yadda sauran jarirai suke yi cikin mahaifiyarsu. Kusan watanni tara bayan hakan, aka haifi Yesu. Amma a yanzu, Yusufu ya auri Maryamu, kuma mutane da yawa suna tsammani cewa Yusufu ne ainihin mahaifin Yesu. Hakika, Yusufu ubansa na riƙo ne. Saboda hakan, za a iya cewa Yesu yana da ubanni biyu!

Sa’ad da Yesu yake ɗan shekara sha biyu, ya yi wani abu da ya nuna cewa yana ƙaunar Ubansa na samaniya, Jehobah. A lokacin, iyalin Yesu, kamar yadda suka tsaba yi sun yi tafiya mai nisa zuwa Urushalima don Idin Ƙetarewa. Bayan hakan, sa’ad da suke kan hanyar dawowa, Yusufu da Maryamu ba su lura cewa Yesu ba ya tare da su. Kana mamaki yadda suka manta da shi?—

A lokacin, Yusufu da Maryamu suna da wasu yara. (Matta 13:55, 56) Wataƙila suna da dangi da suke tafiya tare da su, kamar su Yaƙub, Yohanna tare da mahaifinsu, Zebedee, da mahaifiyarsu, Salome, wacce wataƙila ’yar’uwar Maryamu ce. Saboda haka wataƙila Maryamu tana tunani cewa Yesu yana tare da sauran ’yan’uwansu da suke rukunin.—Matta 27:56; Markus 15:40; Yohanna 19:25.

Sa’ad da Yusufu da Maryamu suka ankara cewa, Yesu ya ɓace, suka koma Urushalima da gaggawa. Suka nemi ɗansu da garaje. A rana ta uku suka gan shi a cikin haikali. Maryamu ta ce masa: “Don menene ka yi mana haka? ga ubanka da ni da baƙinciki muka neme ka.” Amma Yesu ya amsa: “Me ya sa kuka neme ni? ba ku sani ba wajib ne a gareni ina cikin sha’anin Ubana ba?”—Luka 2:45-50.

Kana tsammani cewa bai dace yadda Yesu ya amsa mahaifiyarsa ba?— Iyayensa sun san cewa yana ƙaunar yin bauta a gidan Allah. (Zabura 122:1) Saboda haka, ya dace da Yesu ya ce ya kamata su fara neman shi a haikali. Daga baya, Maryamu ta ci gaba da yin tunani a kan abin da Yesu ya ce.

Menene ra’ayin Yesu game da Yusufu da Maryamu?— Littafi Mai Tsarki ya ce: “[Yesu] ya tafi tare da su, ya zo Nazarat; yana biyayya da su.” (Luka 2:51, 52) Menene za mu iya koya daga misalin Yesu?— E, muna bukatar mu yi biyayya ga iyayenmu ma.

Duk da haka, bai kasance da sauƙi Yesu ya yi biyayya ko yaushe ba, har ga Ubansa na samaniya.

A rana ta ƙarshe kafin mutuwarsa, Yesu ya tambayi ko Jehobah zai canja ra’ayi game da abin da ya nufa ya yi. (Luka 22:42) Amma duk da haka Yesu ya yi biyayya ga Allah ko da bai kasance da sauƙi ba. Littafi Mai Tsarki ya faɗi cewa “ya koya biyayya ta wurin wahalar da ya sha.” (Ibraniyawa 5:8) Kana tsammani cewa mu ma za mu iya koyi darasin kuwa?—

[Hasiya]

a Idan kana karanta wa yaro, wannan alamar fid da ma’ana tana nufin ka dakata, ka ƙarfafa shi ya faɗi ra’ayinsa.

TAMBAYOYI:

▪ Ta yaya Maryamu ta zama mahaifiyar Yesu, kuma yaya aka yi Yesu ya samu uba biyu a wani azancin?

▪ Me ya sa iyayen Yesu ba su san cewa sun bar shi a baya ba?

▪ A wane wuri ne Yesu ya yi zato cewa iyayensa za su neme shi?

▪ Menene za mu iya koya daga misalan Yesu?

[Hoton da ke shafi na 31]

Me ya sa ka yi tsammanin cewa da ya dace Yusufu da Maryamu su fara neman Yesu a cikin haikali?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba