Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 4/1 pp. 12-14
  • Ƙage Da Gaskiya Gaskiya Game Da Yesu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ƙage Da Gaskiya Gaskiya Game Da Yesu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Amsoshin Tambayoyinmu Game da Yesu Kristi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Fahimtar “Nufin Kristi”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Yesu Ya Yi Aure Ne? Yana da ’Yan’uwa Kuwa?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Wane ne Yesu Kristi?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 4/1 pp. 12-14

Ƙage Da Gaskiya Gaskiya Game Da Yesu

MENENE KAKE TSAMMANI? BAYANAN DA KE GABA GASKIYA NE KO KUWA ƘAGE NE?

An haifi Yesu a ranar 25 ga Disamba.

Mazaje masu hikima uku sun ziyarci Yesu a lokacin da aka haife shi.

Yesu ne kaɗai iyayensa suka haifa.

Yesu Allah ne amma ya shiga sifar mutum.

Yesu ya fi mutumin kirki kawai.

MUTANE da yawa za su amsa cewa dukan waɗannan kalaman gaskiya ne. Wasu za su iya cewa yana da wuya kuma ba zai yiwu ba a san gaskiyar. Wataƙila suna ji cewa da zarar ka amince da Yesu, amsar ba ta da amfani.

Amma Littafi Mai Tsarki bai faɗa hakan ba. Ya ƙarfafamu mu samu “cikakken sanin Ubangijinmu Yesu Kristi.” (2 Bitrus 1:8, New World) Muna samun wannan sanin ta yin nazarin Linjiloli. Suna bayyana gaskiya game da Yesu, wanda hakan ke taimaka mana mu bambanta ƙage da gaskiya. Saboda haka bari mu duba abin da Linjiloli suka ce game da waɗannan imanin da aka faɗa a sama.

IMANI: An haifi Yesu a ranar 25 ga Disamba.

MATSAYI: ƘAGE.

Babu wani wuri a cikin Littafi Mai Tsarki da ya yi magana game da wata ko ranar da aka haifi Yesu. To, daga ina ne aka samo kwanan watan 25 ga Disamba? In ji littafin nan The Encyclopædia Britannica, wasu da suke kiran kansu Kiristoci “suka sa ranar ta yi daidai da ranar bikin kafirai na Roma wanda ya yi daidai da . . . lokacin ɗari, sa’ad da rana yake daɗa daɗewa kuma rana yake daɗa yin sama sosai.” Wannan littafin bincike ya nuna cewa al’adun Kirsimati da yawa sun samo asali ne daga “bikin da arna ke yi na noma da kallon rana a tsakiyar lokacin ɗari.”

Shin Yesu zai amince a yi bikin haihuwarsa a ranar 25 ga Disamba kuwa? Ka yi la’akari da wannan: Ba a san ranar da aka haifi Yesu ba. Babu inda Nassosi ya ce mu yi bikin haihuwarsa, kuma babu shaidar da ta nuna cewa Kiristoci na dā sun yi hakan. Akasin haka, Littafi Mai Tsarki ya faɗi ainihin ranar da Yesu ya mutu, kuma ya umurci mabiyinsa su tuna ranar.a (Luka 22:19) Babu shakka, Yesu yana so a mai da hankali ne a kan tamanin mutuwar fansa da ya yi ba ga haihuwarsa ba.—Matta 20:28.

IMANI: Mazaje uku masu hikima (ko kuwa sarakuna a wasu al’adu) sun ziyarci Yesu a lokacin haihuwarsa.

MATSAYI: ƘAGE.

Wataƙila ka taɓa ganin hotuna ko zane da suke nuna Yesu jariri yana kwace cikin sakarkari, kuma mazaje uku masu hikima sun kewaye shi riƙe da kyaututtuka. Amma wannan hoton ƙarya ne ba gaskiya ne ba.

Shin gaskiya ne cewa wakilai da aka aiko daga Gabas sun ziyarci Yesu jariri. Waɗannan baƙin ainihi masanin yanayin taurari ne. (Matta 2:1,The New English Bible; The Bible—An American Translation) Kuma sun gan Yesu kwance cikin sakarkarin ne? A’a, sun ziyarce shi ne a gida. Babu shakka, sun isa wurin ne watanni da yawa bayan haihuwar Yesu.—Matta 2:9-11.

Game da adadin baƙin, shin su 2 ne? 3? ko 30? Littafi Mai Tsarki bai faɗa ba. Wataƙila wannan adadin nan uku ya samo asali ne daga kyauta kala uku da suka kawo.b (Matta 2:11) Wasu ma sun ce wai kowanne cikin waɗannan mutane da ake da’awar cewa masu hikima ne suna wakiltan jinsi dabam na ’yan Adam. Amma wannan ra’ayin ba ya cikin Nassosi. Maimakon hakan, kamar yadda wani littafi da ya bayyana Linjila ya ce, wannan ƙagen ya samu ne daga “wani ɗan tarihi na ƙarni na takwas wanda kawai ya zauna ya ƙirƙiro irin wannan tunanin.”

IMANI: Yesu ne kaɗai iyayensa suka haifa.

MATSAYI: ƘAGE.

An bayyana dalla-dalla a cikin Linjila cewa Yesu yana da ’yan’uwa. Linjilar Luka ta kira Yesu ‘ɗan farin’ Maryamu, kuma hakan ya nuna cewa daga baya ta haifi wasu yara.c (Luka 2:7) Linjilar Markus ta ba da rahoto cewa wasu a cikin birnin Nazarat sun misalta Yesu da ’yan’uwansa, kuma ba su ɗauke shi kamar wani mutum na musamman ba. Sun yi tambaya: “Wannan ba shi ne . . . ɗan’uwan Yaƙub, da Yosi, da Yahuda, da Siman? ’Yan’uwansa mata fa ba nan su ke tare da mu ba?”—Markus 6:3; Matta 12:46; Yohanna 7:5.

Duk da abin da Linjila ta ce, ’yan tauhidi da yawa sun nace cewa Yesu kaɗai aka haifa. Wasu sun ce ’yan’uwansa maza da mata da aka ambata ’ya’yan dangi ne.d Wasu kuma sun ce wai waɗannan ’yan’uwan Yesu yaran Yusufu ne kafin ya auri Maryamu. Amma ka yi la’akari da wannan: Da a ce Yesu kaɗai ne Maryamu ta haifa, da waɗannan ’Yan Nazarat za su furta abin da suka ce? Akasin haka, wataƙila wasu cikinsu sun ga sa’ad da Maryamu take ɗauke da cikin waɗannan yaran. Sun sani ƙwarai cewa Yesu yana ɗaya daga cikin yaran da Maryamu ta haifa.

IMANI: Yesu Allah ne amma ya shiga sifar mutum.

MATSAYI: ƘAGE.

Koyarwar nan da ta ce Allah ya zo cikin duniya a matsayin Yesu, wadda ita ce cibiyar koyarwar Allah-Uku-Cikin-Ɗaya, ta daɗe da wanzuwa amma ba ta soma ba a zamanin Yesu. Maimakon haka, The Encyclopædia Britannica ya lura da wannan: “Kalmar nan Allah-Uku-Cikin-Ɗaya da sauransu ba su cikin Sabon Alkawari . . . Koyarwar ta taso da sannu-sannu a ƙarnuka da yawa kuma cikin jayayya da yawa.”

Addinai suna rage darajar Yesu sa’ad da suka koyar cewa shi Allah ne da ya zo cikin sifar mutum.e Ta yaya? Ka yi la’akari da wannan kwatanci. Wasu ma’aikata sun bukaci wani abu daga mai kula da aikinsu, amma ya ce ba shi da ikon yin hakan. Idan kalamansa gaskiya ne, mai kula da aikin ya nuna cewa ba shi da cikakken iko. Idan ba gaskiya ba ne, wato, idan zai iya biyan bukatansu amma ya ƙi yin hakan, ya ruɗe su ke nan.

A yanzu, yaya Yesu ya amsa sa’ad da almajiransa biyu suka nemi matsayi na ɗaukaka? Ya gaya musu: “Zama ga hannun dama na, da hannun hagu na, ba nawa ba ne da zan bayas, amma za ya zama na waɗanda Ubana ya shirya masa shi.” (Matta 20:23) Da gaskiya ne cewa Yesu Allah ne, da hakan bai zama ƙarya ba? Maimakon haka, ta wajen mai da hankali ga Wanda yake da iko mafi girma, Yesu ya kafa kyakkyawar misali na filako, kuma ya nuna cewa Allah ya fi shi girma.

IMANI: Yesu ya fi mutumin kirki kawai.

MATSAYI: GASKIYA.

Yesu ya bayyana dalla-dalla cewa shi ba mutumin kirki kawai ba ne. Ya ce: ‘Ni Ɗan Allah ne.’ (Yohanna 10:36) Ko da yake, kowanne mutum zai iya da’awar cewa shi Ɗan Allah ne. Amma da a ce Yesu ƙarya yake yi, menene hakan zai nuna game da shi? Hakika, hakan zai nuna cewa shi ba mutumin kirki ba ne, amma mugun ɗan zamba!

Shaida mafi tabbaci ta fito ne daga Allah da kansa. Sau biyu ya ce game da Yesu “Wannan Ɗana ne.” (Matta 3:17; 17:5) Ka yi tunani: Nassosi ya ambata lokatai kaɗan kawai da aka taɓa jin muryar Allah a duniya, duk da haka, a lokatai biyu a cikin su Allah ya tabbatar da cewa Yesu Ɗansa ne! Wannan tabbaci ne mafi girma da ya nuna cewa Yesu ainihin mutumin da ya kira kansa ne.

Wannan talifin ya tona wani gaskiya game da Yesu da ba ka sani ba a dā? Idan haka ne, me zai sa ba za ka daɗa yin nazarin hurarren Linjila ba? Irin wannan nazarin zai iya kasance mai daɗi kuma mai amfani. Ballantana ma, Yesu da kansa ya ce koyon gaskiya game da shi da Ubansa yana kai ga “rai na har abada.”—Yohanna 17:3.

[Hasiya]

a Yesu ya mutu a ranar Idin Ƙetarewa, ko 14 ga Nisan, kamar yadda kalandar Yahudawa ta nuna.—Matta 26:2.

b Matta ya bayyana cewa baƙin “sun buɗe dukiyarsu” sai suka ba Yesu zinari, lubba, da jawul. Abin sha’awa, wataƙila waɗannan tsaraba masu tsada sun zo ne a daidai lokaci, tun da ba da daɗewa ba bayan hakan iyalin Yesu waɗanda talakawa ne sun yi gudun hijira.—Matta 2:11-15.

c Ko da yake ɗaukan cikin Yesu mu’ujiza ce, amma Maryamu ta haifi sauran yaranta ne ta wajen saduwa da mijinta, Yusufu.—Matta 1:25.

d Wannan ra’ayin, da Jerome ya faɗa kusan shekara ta 383 A.Z., sananne ne a tsakanin waɗanda suka gaskata cewa Maryamu ta kasance budurwa a dukan rayuwarta. Daga baya, Jerome ya yi shakkar wannan ra’ayin nasa da ya furta, amma a zukatan mutane da yawa, da kuma a Cocin Katolika, koyarwar ta ci gaba.

e Don cikakken tattaunawar koyarwar Allah-Uku-Cikin-Ɗaya, ka duba mujallar nan Ya Kamata Ka Dogara Da Dunƙulin-Alloli-Uku? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

[Akwati/Hoton da ke shafi na 14]

Ƙarin Gaskiya da Zai Iya Ba Ka Mamaki

Yaya halin Yesu yake? Shin shi mai taurin zuciya ne, mai kumburi, da ba zai iya sha’ani da talakawa ba? Wasu za su amsa e. Wataƙila shi ya sa suke mamakin sanin cewa Yesu . . .

• ya halarci liyafa mai faranta zuciya.—Yohanna 2:1-11.

• ya yaba wa mutane.—Markus 14:6-9.

• ya ji daɗin kasancewa tare da yara.—Markus 10:13, 14.

• ya yi kuka a gaban mutane.—Yohanna 11:35.

• ya ji juyayi.—Markus 1:40, 41.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba