Ka Kusaci Allah
Yana Duba Hali Mai Kyau
1 SARAKUNA 14:13
“UBANGIJI yana binciken dukan zukata, ya kuma gāne dukan siffofin tunani.” (1 Labarbaru 28:9) Ya kamata waɗannan hurarrun Kalamai su cika zuciyarmu da godiya don yadda Jehobah yake kula da mu sosai. Ko da yake mu ajizai ne, Jehobah yana mai da hankali ga abubuwa masu kyau da ke zukatanmu. Mun samu wannan tabbacin a kalamansa game da Abijah, da ke cikin 1 Sarakuna 14:13.
Iyalin Abijah miyagu ne. Mahaifinsa, Jeroboam, shi ne shugaban daular ’yan ridda.a Jehobah ya yi niyyar share gidan Jeroboam gabaki ɗaya, “kamar yadda mutum ya kan share turoso.” (1 Sarakuna 14:10) Amma Allah ya ba da umurni cewa mutum ɗaya a cikin iyalin Jeroboam ne kaɗai za a yi wa jana’iza mai daraja, wato, Abijah, wanda ke rashin lafiya sosai a lokacin.b Me ya sa? Allah ya bayyana: “A cikinsa an iske nufin kirki zuwa ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, a cikin gidan Jeroboam.” (1 Sarakuna 14:1, 12, 13) Mene ne waɗannan kalamai suke nuna mana game da Abijah?
Littafi Mai Tsarki bai ce Abijah yana bauta wa Allah cikin aminci ba. Duk da haka, yana da wasu halaye masu kyau. Wannan halin kirki “zuwa ga Ubangiji” ne, wataƙila game da bautarsa. Marubutan tarihin Yahudawa sun ce wataƙila Abijah yana zuwa bauta a Urushalima ko kuma ya cire masu tsaro da mahaifinsa ya ajiye a kan hanya don su hana Isra’ilawa zuwa bauta a Urushalima.
Ko da yake ba mu san irin nufin kirki da Abijah ya yi ba, amma nufin kirkinsa na musamman ne. Na farko, ya fito ne daga zuciya. Wannan nufin kirkin yana “cikinsa” wato, a cikin zuciyarsa. Na biyu, babu irinsa. Abijah ya nuna wannan nufin kirki duk da cewa yana “cikin gidan Jeroboam.” Wani masani ya ce: “Abin yabawa ne sosai idan mutane suka ci gaba da kasancewa da halin kirki ko da suna zama a wurare da kuma cikin iyali marar kyau.” Wani kuma ya ce nufin kirkin Abijah “fitacce ne . . . , kamar yadda taurari suke haske sosai sa’ad da dare ya yi, da kuma yadda bishiyar al’ul take yin kyau sosai idan bishiyoyi da suka kewaye ta sun kaɗe ganyaye.”
Mafi muhimmanci, kalaman 1 Sarakuna 14:13 sun koya mana wani abu mai kyau game da Jehobah da kuma abin da yake dubawa a zuciyarmu. Ka tuna cewa an “iske” nufin kirki a cikin Abijah. Babu shakka, Jehobah ya bincike zuciyar Abijah har ya ga nufin kirki a cikinta. Akasin iyalinsa, Abijah lu’u lu’u guda ne da ke cikin “tarin duwatsu,” in ji wani masani. Jehobah ya daraja kirkinsa kuma ya albarkace shi, ta wajen nuna masa kaɗai tagomashi a cikin iyalin miyagu.
Shin ba abin ƙarfafa ba ne mu san cewa Jehobah yana duba kuma yana daraja nufin kirkin da ke cikin zuciyarmu duk da cewa mu ajizai ne? (Zabura 130:3) Ya kamata sanin hakan ya motsamu mu kasance kusa da Jehobah, Allahn da ke bincika zuciyarmu sosai don ya ga nufin kirkin da muke da shi ko da ɗan kaɗan ne.
[Hasiya]
a Jeroboam ya kafa bautar maraƙi a arewancin ƙabilu goma ta Isra’ila don kada mutanen su bauta wa Jehobah a haikalinsa da ke a Urushalima.
b Ana ɗaukan ƙin yi wa mutum jana’iza mai daraja a zamanin dā a matsayin alamar rashin amincewar Allah.—Irmiya 25:32, 33.