Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 2/15 pp. 30-32
  • Abin da Zai Taimaka wa Matasa Su Tuna da Mahaliccinsu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Abin da Zai Taimaka wa Matasa Su Tuna da Mahaliccinsu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Abin Taimako a Nazarin Littafi Mai Tsarki na Iyali
  • Littafi don Sadarwa
  • Ka Motsa Zuciya
  • Bauta Ta Iyali Tana Da Muhimmanci Don Tsira!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Iyaye Ku Kāre Kyautarku Mai Tamani
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Iyaye, Ku Kula da Yaranku
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 2/15 pp. 30-32

Abin da Zai Taimaka wa Matasa Su Tuna da Mahaliccinsu

SHEKARU dubu uku da suka shige, Sulemanu mutum mai hikima ya rubuta cewa: “Ka tuna da Mahaliccinka kuma a cikin kwanakin ƙuruciyarka.” (M. Wa. 12:1) Matasa Kiristoci yanzu sun sake samun wani abin da zai taimaka musu su yi hakan. An fito da littafin nan Questions Young People Ask—Answers That Work, Littafi na 2 a Taron Gunduma na Shaidun Jehobah mai jigo, “Ruhun Allah Yana Yi Mana Ja-gora” da aka yi a dukan duniya daga watan Mayu 2008 zuwa Janairu 2009.

Hukumar Mulki ta rubuta wasiƙa da ke shafi na farko na littafin ga matasa. Ta ce: “Muna addu’a cewa bayanin da ke cikin wannan littafin zai taimaka muku ku jimre da matsi da gwaji da ke fuskantar matasa a yau kuma zai nuna muku yadda za ku tsai da shawarwari da suka jitu da nufin Allah.”

Iyaye suna son su yi renon yaransu “cikin foron Ubangiji da gargaɗinsa.” (Afis. 6:4) Amma sa’ad da suka kai ƙuruciya, matasa da yawa suna rashin tabbaci game da kansu kuma suna son a yi musu ja-gora. Idan kai mahaifi ko mahaifiyar matashi ne, yaya za ka taimaka wa yaronka ya amfana sosai daga wannan littafin? Ga wasu shawarwari a gaba.

▪ Ka karɓi naka littafin kuma ka san abin da ke ciki sosai. Hakan ya wuce karanta littafin kawai. Ka yi ƙoƙari ka lura da yadda aka furta ra’ayoyi a cikin littafin. Maimakon kawai ya gaya wa matasa abin da ke daidai da abin da ba daidai ba, littafin ya yi ƙoƙari ya koyar da “hankulansu.” (Ibran. 5:14) Ya kuma ba su shawarwari masu kyau a kan yadda za su dage ga yin abin da ke daidai. Alal misali, Babi na 15 “How Can I Resist Peer Pressure?”(“Yaya Zan Ƙi da Matsi na Tsara?”) bai gaya wa matasa su ce a’a kawai ba. Ya tsara yadda za a yi amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki cikin dabara da kuma yadda za a ba da amsa a yanayi na gaske a rayuwa domin matasa su san yadda za su “amsa tambayar kowa.”—Kol. 4:6.

▪ Ka yi amfani da wuraren da mai karatu yake tattaunawa da littafin. Ko da yake an shirya waɗannan wuraren ne don matasa, zai dace idan ka cika waɗannan wurare sa’ad da za ka iya yin hakan a naka kofin.a Alal misali, sa’ad da kake yin la’akari da tambayoyi biyu game da fita zance a shafi na 16, ka yi ƙoƙari ka tuna yadda ka ji sa’ad da kake shekarun ɗanka. Wataƙila a filin rubutu da aka ba da, za ka so ka cika amsoshin yadda za ka amsa a lokacin. Sa’an nan za ka iya tambayar kanka: ‘Yaya yadda nake ji game da wannan batun ya canja cikin shekarun da suka shige? Wane fahimi na samu tun daga lokacin da nake ƙuruciya, kuma yaya zan koya wa yaro na wannan fahimin?’

▪ Ka daraja sirrin ɗanka da ya rubuta. An shirya wurin rubuta ra’ayi na littafin don a san ra’ayin yaronka kuma a sa ya rubuta game da batun ko kuma ya yi tunani a kansa. Makasudinka shi ne ka san abin da ke cikin zuciyarsa, ba abin da ya rubuta ba. A shafi na 3 a sashe mai jigo “A Note to Parents,” (“Abin Lura ga Iyaye”) littafin ya ce: “Don ka ƙarfafa yaranka su rubuta abin da ke zuciyarsu a cikin littafinsu, kada ka saka musu ido. Daga baya suna iya gaya maka batutuwan da suka rubuta.”

Abin Taimako a Nazarin Littafi Mai Tsarki na Iyali

Littafin Young People Ask, Littafi na 2, abin taimako ne mafi kyau da za ku yi amfani da shi a lokacin Bauta ta Iyali. Tun da yake littafin ba shi da tambayoyin nazari a sakin layi, yaya za ka iya yin amfani da shi? Me ya sa ba za ka canja tsarin nazarin littafin ta wajen yin amfani da abin da ya fi dacewa da yaranka ba?

Alal misali, wasu iyalai suna iya jin daɗin yin gwaji sa’ad da suke bincika sashen nan “Peer-Pressure Planner” (“Shiri don Matsi na Tsara”) da ke shafuffuka na 132 da 133. Tambaya na farko a wajen yana iya taimaka wa yaronka ko ’yarka ya fahimci batun da shi ko ita ya ga ya fi yi masa wuya. Tambaya na biyu ta nuna yanayi da matsi zai taso. Bayan an tattauna sakamakon faɗa wa matsi na tsara ko kuma ƙinsa, an gaya wa ɗanka ya shirya wasu amsoshi na amincewa da matsin, ƙinsa, ko kuma mayar da matsin. Ka taimaka wa ɗanka ko ’yarka ya ko ta shirya amsoshi dabam-dabam da suke so kuma waɗanda za su iya yin amfani da su da gaba gaɗi da kuma tabbaci.—Zab. 119:46.

Littafi don Sadarwa

Littafin nan, Young People Ask, Littafi na 2, ya ƙarfafa matasa su riƙa tattaunawa da iyayensu. Alal misali, akwatunan nan “How Can I Talk to Dad or Mom About Sex?” (“Yaya Zan Yi wa Baba ko Mama Magana Game da Jima’i?”) (shafuffuka na 63-64) da kuma “Talk to Your Parents!” (“Ka Yi Magana da Iyayenka!”) (shafi na 189) sun ba da shawarwari masu kyau a kan yadda za su soma tattaunawa game da batutuwa masu wuya. Wata yarinya ’yar shekara 13 ta rubuta, “Wannan littafin ya ƙarfafa ni na tattauna da iyayena game da abubuwan da suke zuciyata, har da abubuwan da na yi.”

Wannan littafin ya ƙarfafa tattaunawa a wasu hanyoyi kuma. A ƙarshen kowane babi akwai akwati mai jigo “What Do You Think?” (“Menene Ra’ayinka?”) Wannan ba yin bita kawai ba ne, za a iya yin amfani da shi a matsayin awutlayi don tattaunawa na iyali. A kusa da ƙarshen kowane babi akwai akwati mai jigo “Action Plan!” (“Shirin Mataki”) Wannan akwatin ya ba matasa zarafin rubuta takamammun hanyoyin da za su yi amfani da abin da suka koya a wannan babin. Sashe na ƙarshe na kowane akwatin “Action Plan!” ya ce: “Abin da zan so na tambayi iyayena game da wannan batun shi ne . . . ” Wannan zai taimaka wa matasa su dogara ga iyayensu don shawara mai kyau.

Ka Motsa Zuciya

A matsayin iyaye, makasudinka shi ne ka motsa zuciyar ɗanka. Littafin nan Young People Ask, Littafi na 2, zai taimake ka ka yi hakan. Ka yi la’akari da yadda wani uba ya yi amfani da wannan littafin don ya riƙa tattaunawa da kyau da ’yarsa.

“Da ni da Rebekah muna da wurare masu kyau da muke takawa mu je, mu hau babur ko keke, ko kuma mu tafi da mota. Waɗannan yanayi yana ba ta zarafi da ke sa ta faɗi zuciyarta.

“Sashe na farko da muka tattauna a wannan littafin shi ne wasiƙa daga Hukumar Mulki da kuma ‘Abin Lura ga Iyaye.’ Ina son ’yata ta san cewa kamar yadda aka faɗa a shafi na 3, tana da ’yancin yin rubutu a cikin littafinta yadda take so. Ba na dubawa na ga abin da ta rubuta.

“Na bar Rebekah ta zaɓi babobi da za ta so ta tattauna da kuma tsarin da za ta so ta bi ta tattauna su. Ɗaya daga cikin babobi na farko da ta zaɓa shi ne ‘Should I Play Electronic Games?’ (‘Ya Kamata Na Yi Wasanni na Kwamfuta?’) Ban taɓa tunanin cewa za ta zaɓi wannan ba! Amma, tana da dalilin yin hakan. Abokanta da yawa suna yin mugun wasannin kwamfuta. Ban san irin hotunan nuna ƙarfi da magana ta ban ƙyama da ke ciki ba! Amma mun tattauna dukan waɗannan a cikin akwatin nan “Action Plan!” da ke shafi na 251. Wannan akwatin ya kuma taimaka wa Rebekah ta shirya amsar da za ta ba da idan wani yana ƙoƙarin ya matsa mata ta yi wasan.

“A wannan lokacin, Rebekah ta gaya mini abin da ta rubuta a littafinta. A lokacin nazarinmu ba ma daina tattaunawa. Kowannenmu yana karantawa ɗaya bayan ɗaya, kuma tana son ta yi magana game da kome, har da hotuna da akwatunan. Wannan ya ba ni zarafin gaya mata yadda abubuwa suke sa’ad da nake shekarunta, sa’annan sai ta gaya mini abubuwan da suke faruwa a yau. Tana son ta gaya mini kome!”

Idan kai mahaifi ne ko kuma mahaifiya, babu shakka ka yi farin ciki sa’ad da aka fito da wannan littafin. Yanzu kuna da zarafin yin amfani da shi da kyau. Hukumar Mulki tana begen cewa wannan littafin Questions Young People Ask—Answers That Work, Littafi na 2, zai zama albarka ga iyalinku. Bari ya taimaki kowa, musamman matasanmu ƙaunatattu su ci gaba da ‘yin tafiya bisa ga ruhu mai tsarki.’—Gal. 5:16.

[Hasiya]

a Wasu falle na wuraren rubuta ra’ayinka da ke littafin ya shafi kowa. Alal misali, akwatin nan “Control Your Anger” (Ka Riƙe Fushinka) (shafi na 221) zai taimaka maka yadda zai taimaka wa ɗanka ko ’yarka. Zai kasance hakan ga “Peer-Pressure Planner” (Shiri Don Matsi na Tsara”) (shafuffuka na 132-133), “My Monthly Budget” (Kuɗin da Zan Riƙa Kashewa Kowane Wata”) (shafi na 163), da kuma “My Goals” (Makasudina) shafi na 314.

[Akwati da ke shafi na 30]

Abin da Wasu Matasa Suke Faɗa

“Wannan littafi ne da za ka zauna da fensil kuma ka karanta shi kana yin bimbini. An shirya shi don a yi amfani da shi a matsayin inda za ka iya yin rubutu don ka yi bimbini da muradin samun hanyar rayuwa mafi kyau.”—Nicola.

“An matsa mini sosai na riƙa fita zance, har da mutanen da suke da nufin kirki. Sashe na farko na wannan littafin ya tabbatar mini cewa ko da menene wani ya faɗa, ban yi shirin fita zance ba.”—Katrina.

“Akwatin nan ‘Kana Yin Tunanin Yin Baftisma?’ ya taimaka mini na ɗauki baftismata da muhimmanci sosai. Ya motsa ni na sake bincika yadda nake nazari da addu’a.”—Ashley.

“Ko da yake iyayena Kiristoci sun koya mini tun ina ƙarama, wannan littafin ya sa ni tunani da kaina game da matakai da ya kamata na ɗauka a rayuwata. Ya kuma taimaka mini na gaya wa iyayena zuciya ta.”—Zamira.

[Hoton da ke shafi na 31]

Iyaye, ku san wannan littafin sosai

[Hoton da ke shafi na 32]

Ka kafa makasudin motsa zuciyar yaranka

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba