Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 2/15 pp. 3-5
  • Kana Ɗaukan Jehobah a Matsayin Ubanka?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kana Ɗaukan Jehobah a Matsayin Ubanka?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Jehobah—Mai Tanadi Cikin Ƙauna
  • Ubanmu “Mai Kāriya”
  • Yadda Muka Amfana Sosai!
  • Ubanmu Yana ‘Riƙe Hannun Damanmu’
  • Jehobah Ubanmu Yana Kaunar Mu Sosai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • ‘Ɗan Yana A Shirye ya Bayyana Uban’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ka Kusaci Jehobah da Kuma ’Yan’uwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Uba da Babu Kamarsa Matta 3:16, 17
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 2/15 pp. 3-5

Kana Ɗaukan Jehobah a Matsayin Ubanka?

“UBANGIJI, ka koya mana yin addu’a.” Sa’ad da wani daga cikin almajiransa ya yi wannan roƙo, Yesu ya amsa: “Sa’anda kuna yin addu’a, ku ce, Ya Uba, a tsarkake sunanka.” (Luk 11:1, 2) Yesu zai iya kiran Jehobah da manyan laƙabai kamar “Alƙadiru” ‘Mai-Koyarwa’ “Mahalicci” “Mai-Zamanin Dā,” da “Sarki na zamanu.” (Far. 49:25; Isha. 30:20; 40:28; Dan. 7:9; 1 Tim. 1:17) Maimakon haka, Yesu ya zaɓi kalmar nan “Uba.” Me ya sa? Wataƙila domin yana son mu kusaci Mutumi mafi girma a sararin samaniya yadda yaro mai tawali’u yake kusantar uba mai ƙauna.

Amma, yana yi wa wasu mutane wuya su ɗauki Allah a matsayin Ubansu. Wata Kirista mai suna Atsukoa ta ce, “Shekaru da yawa bayan na yi baftisma, ya yi mini wuya na kusaci Jehobah kuma na yi addu’a a gare shi a matsayin Uba.” Da take faɗan dalilin wannan fama, ta ce, “Ban tuna lokacin da babana ya nuna mini ƙauna ba.”

A waɗannan miyagun kwanaki na ƙarshe, ba a samun “ƙauna irin na tabi’a” da mutum yake bukatar ya samu daga wurin ubansa. (2 Tim. 3:1, 3) Saboda haka, ba sabon abu ba ne mutane su ji yadda Atsuko take ji ba. Amma, abin ban ƙarfafa ne mu san cewa muna da dalilai masu kyau na ɗaukan Jehobah a matsayin Ubanmu mai ƙauna.

Jehobah—Mai Tanadi Cikin Ƙauna

Idan za mu ɗauki Jehobah a matsayin Ubanmu, muna bukatan mu san shi sosai. Yesu ya ce: “Ba mai-sanin Ɗan, sai Uban kaɗai, ba kuwa mai-sanin Uban, sai Ɗan, da dukan wanda Ɗan ya nufa shi bayyana masa.” (Mat. 11:27) Hanya mafi kyau ta sanin Jehobah a matsayin Uba ita ce yin tunani a kan abin da Yesu ya bayyana game da Allah na gaskiya. Saboda haka, menene Yesu ya koyar game da Uban?

Da yake nuna cewa Jehobah ne Tushen rayuwarsa, Yesu ya ce: “Ina rayuwa saboda Uban.” (Yoh. 6:57) Mu ma muna rayuwa ne saboda Uban. (Zab. 36:9; A. M. 17:28) Menene ya motsa Jehobah ya ba mutane rai? Ƙauna ce ta motsa shi. Babu shakka ya kamata mu ƙaunaci Ubanmu na samaniya saboda irin wannan kyauta da ya ba mu.

Ƙauna mafi girma da Allah ya nuna wa ’yan Adam ita ce yin tanadin hadayar fansa ta Yesu. Fansa ta sa ya yiwu ’yan Adam masu zunubi su kasance da dangantaka na kud da kud da Jehobah ta hanyar Ɗansa ƙaunatacce. (Rom. 5:12; 1 Yoh. 4:9, 10) Kuma domin Ubanmu na samaniya Mai Cika alkawuransa ne, muna da tabbaci cewa dukan waɗanda suke ƙaunarsa da kuma yi masa biyayya za su more “yancin darajar ’ya’yan Allah” a nan gaba.—Rom. 8:21.

Ubanmu na samaniya kuma “ya kan sa ranatasa ta fito” kullum. (Mat. 5:45) Da kyar mu yi tunanin cewa yana da muhimmanci mu yi addu’a don rana ta fito. Duk da haka, muna bukata da kuma more ɗuminta! Bugu da ƙari, Ubanmu Mai Tanadi ne da babu kamarsa, wanda ya san bukatunmu kafin mu tambaye shi. Saboda haka, ya kamata mu ɗauki lokaci mu lura kuma mu yi bimbini cikin godiya a kan yadda Ubanmu na samaniya yake kula da halittunsa, ko ba haka ba?—Mat. 6:8, 26.

Ubanmu “Mai Kāriya”

Annabcin Ishaya ya tabbatar wa mutanen Allah na dā: “Duwatsu za su tashi a wurinsu, tuddai kuma za su kawu; amma alherina ba za ya tashi daga wurinki ba, alkawarina kuma na salama ba za ya kawu ba, in ji Jehobah mai kāriya zuwa gareki.” (Isha. 54:10, The Bible in Living English) Don ya nanata wannan darasin, addu’ar Yesu a darensa na ƙarshe a duniya ta nuna cewa da gaske Jehobah “mai kāriya” ne. Yesu ya yi addu’a game da almajiransa cewa: “Suna cikin duniya, ni kuwa ina zuwa gare ka. Ya Uba mai-tsarki, ka kiyaye su a cikin sunanka.” (Yoh. 17:11, 14) Jehobah ya lura da mabiyan Yesu kuma ya kāre su.

Hanya ɗaya da Allah yake kāre mu daga dabarun Shaiɗan a yau ita ce ta wajen yin tanadin abinci na ruhaniya a kan lokaci ta hanyar “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.” (Mat. 24:45) Cin wannan abinci mai ƙarfafawa yana da muhimmanci idan muna son mu “yafa dukan makamai na Allah.” Alal misali, ka yi la’akari da “garkuwa ta bangaskiya,” wadda muke “ɓice dukan jefejefe masu-wuta na Mugun” da ita. (Afis. 6:11, 16) Bangaskiyarmu tana kāre mu daga haɗari na ruhaniya kuma hakan ya nuna cewa muna amincewa da ikon kāriya na Ubanmu.

Muna iya ƙara samun fahimi game da kulawar Ubanmu na samaniya ta wajen yin la’akari da yadda Ɗan Allah ya aikata sa’ad da yake duniya. Ka lura da labarin da ke rubuce a Markus 10:13-16. A wajen an yi ƙaulin Yesu yana gaya wa almajiransa: “Ku bar yara ƙanƙanana su zo gareni.” Sa’ad da waɗannan yara ƙanƙanana suka taru a wajensa, Yesu ya rungume su kuma ya yi musu albarka. Babu shakka hakan ya sa su farin ciki sosai! Kuma tun da yake Yesu ya ce: “Wanda ya gan ni ya ga Uban,” mun san cewa Allah na gaskiya yana son mu zo wajensa.—Yoh. 14:9.

Jehobah Allah Tushe ne na ƙauna da babu iyakarta. Shi mai yin Tanadi ne kuma Mai kāriya da babu kamarsa wanda yake son mu kusace shi. (Yaƙ. 4:8) Babu shakka, Jehobah ne Uba mafi kyau!

Yadda Muka Amfana Sosai!

Muna samun amfani sosai ta wajen dogara ga Jehobah Ubanmu na samaniya mai ƙauna da kula. (Mis. 3:5, 6) Yesu ya amfana ta wajen dogara ga Ubansa sosai. Kristi ya gaya wa almajiransa: “Ba ni kaɗai ba ne, amma da ni da Uba wanda ya aiko ni.” (Yoh. 8:16) Yesu yana da tabbaci a koyaushe cewa Jehobah zai taimake shi. Alal misali, a lokacin baftismarsa, ya samu tabbaci daga Uban, wanda ya sanar: “Wannan Ɗana ne, ƙaunatacena, wanda raina na jin daɗinsa ƙwarai.” (Mat. 3:15-17) Kuma gab da mutuwarsa, Yesu ya ce: “Uba, a cikin hannuwanka ni ke bada ruhuna.” (Luk 23:46) Har ila Yesu ya dogara sosai ga Ubansa kamar dā.

Mu ma za mu iya shaida hakan. Tun da yake Jehobah yana tare da mu, ba ma bukatan mu ji tsoro. (Zab. 118:6) Atsuko, da aka ambata ɗazu, ta saba dogara ga ƙarfinta sa’ad da take fuskantar matsaloli. Amma sai ta yi nazarin rayuwar Yesu da hidimarsa, ta mai da hankali musamman ga dangantakarsa na kud da kud da Ubansa na samaniya. Menene sakamakon? “Na koyi ma’anar samun Uba da kuma dogara a gare shi,” in ji Atsuko. Ta daɗa: “Na samu salama ta gaske da farin ciki. Hakika, babu dalilin damuwa game da kome.”

Ta yaya muke ƙara samun amfani ta wajen ɗaukan Jehobah a matsayin Ubanmu? Yara suna ƙaunar iyayensu kuma suna son su faranta musu rai. Domin yana ƙaunar Ubansa, Ɗan Allah ‘kullum yana aikata abin da ya gamshe shi.’ (Yoh. 8:29) Hakazalika, ƙaunar Ubanmu na samaniya za ta motsa mu mu aikata da hikima kuma mu ‘yabe shi’ a fili.—Mat. 11:25; Yoh. 5:19.

Ubanmu Yana ‘Riƙe Hannun Damanmu’

Ubanmu na samaniya ya kuma yi tanadin “mai-taimako,” wato, ruhunsa mai tsarki. Zai “bishe ku cikin dukan gaskiya,” in ji Yesu. (Yoh. 14:15-17; 16:12, 13) Ruhu mai tsarki na Allah zai iya sa mu fahimci Ubanmu da kyau. Yana iya taimaka mana mu rushe abubuwa “masu-ƙarfi,” wato, ra’ayin da muke da shi, ra’ayin da ba daidai ba ko kuma na ƙarya, ta hakan mu “komo da kowane tunani cikin bauta ga biyayyar Kristi.” (2 Kor. 10:4, 5) Saboda haka, bari mu yi addu’a ga Jehobah don “mai-taimako” da ya yi alkawarinsa, da tabbaci cewa “Uban[mu] na sama za ya bada ruhu mai-tsarki ga waɗanda su ke roƙonsa.” (Luk 11:13) Ya kuma dace mu yi addu’a ruhu mai tsarki ya taimaka mana mu kusaci Jehobah.

Sa’ad da ƙaramin yaro yake tafiya da babansa kuma yana riƙe da hannunsa, ba ya jin tsoro. Idan ka ɗauki Jehobah a matsayin Ubanka da gaske, za ka iya kasance da tabbaci a waɗannan kalmomin ban ƙarfafa: “Ni Ubangiji Allahnka zan riƙe hannun damanka, in ce maka, Kada ka ji tsoro, ni taimake ka.” (Isha. 41:13) Za ka iya samun gata mai ban al’ajabi na yin “tafiya” da Allah har abada. (Mi. 6:8) Ka ci gaba da yin nufinsa, kuma za ka shaida ƙauna, farin ciki, da kwanciyar hankali da za ka samu daga ɗaukan Jehobah a matsayin Uba.

[Hasiya]

a An canja suna.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba