Ka Yi Murna Saboda Auren Ɗan Ragon!
“Bari mu yi murna mu yi farin zuciya ƙwarai, . . . gama auren Ɗan rago ya zo.”—R. YOH. 19:7.
1, 2. (a) Wane aure ne zai sa a yi farin ciki sosai a sama? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?
YANA ɗaukan lokaci sosai a yi shirin aure. Amma yanzu za mu mai da hankali ga wani aure na musamman da aka ɗauki kusan shekaru dubu biyu ana shirinsa. Ba da daɗewa ba, za a ɗaura wa angon da amaryarsa aure. Za a ji waƙa mai daɗi a ko’ina cikin fadar Sarki, kuma mala’iku za su yi waƙa suna cewa: “Halleluyah: gama Ubangiji Allahnmu, mai-iko duka, yana mulki. Bari mu yi murna mu yi farin zuciya ƙwarai, mu bada ɗaukaka gareshi: gama auren Ɗan rago ya zo, matatasa kuma ta shirya kanta.”—R. Yoh. 19:6, 7.
2 “Ɗan rago” da zai sa a yi farin ciki da waƙa a sama shi ne Yesu Kristi. (Yoh. 1:29) Aurensa zai sa a yi farin ciki sosai a sama. Wace ce amaryarsa? Ta yaya aka shirya ta don bikin auren? Yaushe ne za a yi auren? Da yake wannan auren zai sa a yi farin ciki a sama, to, amma waɗanda suke da begen rayuwa a duniya har abada a duniya su ma za su yi farin cikin ne? Muna dokin samun amsoshin waɗannan tambayoyin yayin da muke bincika Littafin Zabura ta 45.
‘TUFAFINSA SUNA ƘAMSHI’
3, 4. (a) Mene ne marubucin zabura ya faɗa game da tufafin Angon, kuma me ya ƙara sa shi farin ciki? (b) Su waye ne “’ya’yan sarakuna mata” da “sarauniya” da ƙawayenta, waɗanda suke taya Angon murna?
3 Karanta Zabura 45:8, 9. Angon wato, Yesu ya yi ado don bikin aurensa. Tufar da ya saka suna ƙamshin turare “mafi tsada” kamar su murra da saliha da ake amfani da su wajen yin māi mai-tsarki na shafe sarakuna a ƙasar Isra’ila.—Fit. 30:23-25.
4 Waƙa mai daɗi da ake yi a fadarsa tana sa angon farin ciki sosai da yake lokacin aurensa yana gabatowa. Yana farin ciki tare da “sarauniya” da ƙawayenta, wato ƙungiyar Allah ta sama da ta ƙunshi “’ya’yan sarakuna mata,” wato mala’iku. Abin farin ciki a ji muryoyi daga sama suna cewa: “Bari mu yi murna mu yi farin zuciya ƙwarai, . . . gama auren Ɗan rago ya zo”!
AMARYAR TA YI SHIRI DON AUREN
5. Wace ce ‘matar Ɗan ragon’?
5 Karanta Zabura 45:10, 11. Mun gane angon yanzu, amma wace ce amaryar? Ba wata mace ba ce ta zahiri, amma tana wakiltar Kirista shafaffu guda 144,000. Yesu ne shugaban ikilisiyar shafaffun Kiristoci. (Karanta Afisawa 5:23, 24.) Waɗannan shafaffun Kiristoci za su yi sarauta tare da Kristi a sama. (Luk 12:32) Waɗannan shafaffun Kiristoci 144,000 “sukan bi Ɗan rago inda ya tafi duka.” (R. Yoh. 14:1-4) Sun zama ‘matar Ɗan ragon’ kuma sun kasance tare da shi a sama.—R. Yoh. 21:9; Yoh. 14:2, 3.
6. Me ya sa ake kiran shafaffu “ɗiyar sarki,” kuma me ya sa aka ce su ‘manta da danginsu’?
6 An ƙira amaryar “ɗiya” da kuma “ɗiyar sarki.” (Zab. 45:13) Wane ne wannan ‘sarkin’? Ana ɗaukan Kiristoci shafaffu a matsayin ‘’ya’yan’ Jehobah. (Rom. 8:15-17) An gaya wa waɗannan shafaffun cewa: ‘Ku manta da danginku, da gidan ubanku.’ Da yake za su zama amarya a sama, an bukace su su ‘ƙalafa ransu ga abubuwan da ke bisa, ba wajen na ƙasa ba.’—Kol. 3:1-4.
7. (a) Ta yaya Kristi yake yin shiri don budurwar da zai aura? (b) Yaya amaryar take ɗaukan wanda za ta aura?
7 A ƙarnuka da yawa yanzu, Kristi yana ta shiri don amaryarsa da za a yi bikin aurensu a sama. Manzo Bulus ya bayyana cewa Kristi “ya ƙaunaci ikilisiya, ya ba da kansa domin ta; domin shi tsarkake ta, bayan da ya tsabtata ta cikin wankin ruwa ta wurin kalman, domin shi miƙo wa kansa ikilisiya, ikilisiya mai-daraja, ba tare da aibi ko cira ko kowane abu misalin waɗannan; amma ta zama mai-tsarki marar-aibi.” (Afis. 5:25-27) Bulus ya gaya wa shafaffun Kiristoci a Koranti cewa: “Ina kishinku da kishi irin na Allah: Gama na ɗaure aurenku ga miji ɗaya, domin in miƙa ku budurwa mai-tsabta ga Kristi.” (2 Kor. 11:2) Da yake bautar da take yi mai tsarki ce, Yesu Kristi yana ganinta kyakkyawa sosai. Amaryarsa tana ɗaukan sa a matsayin ‘Ubangiji’ kuma tana “yi masa sujada” a matsayin wanda zai aure ta.
AN ‘KAI AMARYAR WURIN SARKI’
8. Me ya sa aka kwatanta amaryar a matsayin mai “daraja ƙwarai”?
8 Karanta Zabura 45:13, 14. An yi wa amaryar ado mai “daraja ƙwarai” don bikin auren. A littafin Ru’ya ta Yohanna 21:2, an kwatanta amaryar da birni, wato Sabuwar Urushalima da aka mata ado don bikin aure. Wannan birni da ke sama yana da “ɗaukakar Allah” kuma yana da haske “dutse mai tsada mafifici, sai ka ce dutsen jasfer, garai kamar kiristal.” (R. Yoh. 21:10, 11) An kwatanta yadda Sabuwar Urushalima take da kyau a littafin Ru’ya ta Yohanna. (R. Yoh. 21:18-21) Babu shakka, shi ya sa marubucin zabura ya kwatanta amaryar a matsayin wadda take da “daraja ƙwarai.” Kuma za a ɗaura wannan auren a sama.
9. Wane ne wannan “sarki” da aka kawo masa amarya, kuma wane irin ado ne aka yi wa amaryar?
9 Angon da aka kawo masa amarya shi ne Sarki Almasihu. Ya shirya ta kuma ya “tsabtata ta cikin wankin ruwa ta wurin kalman.” Don haka ta “zama mai-tsarki marar-aibi.” (Afis. 5:26, 27) Za a yi wa amaryar nan ado mai kyau don wannan rana ta musamman. Hakika, “da zinariya aka yi jifar saƙar tufafinta” kuma “za a kai ta wurin sarki da zane na aikin zalwa.” An “yarda mata kuma ta yafa ma kanta linen mai-laushi, mai-walƙiya, mai-tsabta: gama linen nan mai-laushi ayyuka masu-adalci na tsarkaka ne” domin auren Ɗan ragon.—R. Yoh. 19:8.
AN ‘KAI AMARYAR WURIN SARKI’
10. Yaushe za a ɗaura auren Ɗan ragon?
10 Karanta Ru’ya ta Yohanna 19:7. Yaushe za a ɗaura auren Ɗan ragon? Ko da yake “matatasa kuma ta shirya kanta” don ɗaurin auren, ayoyin da suka bi bayan wannan ayar ba su yi magana a kan bikin auren ba. Maimakon haka, sun kwatanta abin zai faru a ƙarshen ƙunci mai girma ne. (R. Yoh. 19:11-21) Shin wannan yana nufin cewa za a yi auren kafin angon ya ci nasara? A’a. Abubuwan da aka ambata a littafin Ru’ya ta Yohanna ba a jera su ɗaya bayan ɗaya ba. Zabura ta 45 ta nuna cewa Sarki Yesu Kristi ya rataye takobinsa kuma ya ci magabtansa da yaƙi kafin a ɗaura auren.—Zab. 45:3, 4.
11. Mene ne Yesu zai yi kafin a yi auren?
11 Mun koya daga Littafi Mai Tsarki cewa abubuwa za su faru kamar haka: Da farko, za a halaka “babbar karuwa,” Babila Babba, wato dukan addinan ƙarya. (R. Yoh. 17:1, 5, 16, 17; 19:1, 2) Bayan haka, sai a halaka zamanin Shaiɗan a yaƙin Armageddon, wato “yaƙin babbar rana ta Allah Mai-iko duka.” (R. Yoh. 16:14-16; 19:19-21) A ƙarshe, Sarkin zai kammala nasararsa ta wurin jefa Shaiɗan da aljanunsa cikin rami marar matuƙa, inda ba za su iya hadassa mugunta ba.—R. Yoh. 20:1-3.
12, 13. (a) Yaushe ne za a ɗaura auren Ɗan ragon? (b) Su waye ne za su yi farin ciki a sama don auren Ɗan ragon?
12 A waɗannan kwanaki na ƙarshe, Kiristoci shafaffu waɗanda suka kasance da aminci har mutuwa za a ta da su zuwa sama. Bayan an halaka Babila Babba, kuma an yi yaƙin Armageddon, Yesu zai tattara dukan shafaffu 144,000 kuma ya kai su wajensa a sama. (1 Tas. 4:16, 17) Saboda haka, kafin a soma yaƙin Armageddon, duka ƙawayen “amaryar” za su tafi sama. Bayan yaƙin, sai a ɗaura auren Ɗan ragon. Za a yi farin ciki sosai a lokacin. Ru’ya ta Yohanna 19:9 ta ce: “Masu-albarka ne waɗannan da an kira zuwa bikin angonci na Ɗan rago.” Hakika Angon, wato Sarkin zai yi murna matuƙa don dukan abokansa shafaffu suna tare da shi a sama. (Luk 22:18, 28-30) Amma, ba Angon da amaryar ba ce kaɗai za su yi farin ciki don wannan bikin auren ba.
13 Kamar yadda muka karanta ɗazun, halittun sama sun rera waƙa suna cewa: “Bari mu yi murna mu yi farin zuciya ƙwarai, mu bada ɗaukaka gareshi [Jehobah]: gama auren Ɗan rago ya zo, matatasa kuma ta shirya kanta.” (R. Yoh. 19:6, 7) Bayin Jehobah da ke duniya kuma fa? Shin su ma za su yi farin cikin ne?
DA MURNA ZA A KAI SU
14. Kamar yadda aka ambata a Zabura ta 45, su waye ne “budurwai” na amaryar?
14 Karanta Zabura 45:12, 14, 15. Annabi Zakariya ya annabta cewa a kwanaki na ƙarshe, mutane na dukan duniya za su yi farin ciki suna bauta wa Jehobah tare da shafaffun da suka rage a duniya. Ya ce: “A cikin waɗannan kwanaki mutum goma daga cikin dukan harsunan al’ummai za su kama ƙafar wanda shi ke Ba-yahudi, su ce, Za mu tafi tare da ku, gama mun ji labari Allah yana tare da ku.” (Zak. 8:23) A littafin Zabura 45:12, wannan “mutum goma” suna wakiltar “Ɗiyar Tyre” da “mawadata a cikin jama’a.” Sun zo wurin shafaffu da suka rage a duniya da kyauta, kuma sun yi aiki don su sami amincewa da taimako don su bauta wa Jehobah. Tun daga shekara ta 1935, miliyoyin mutane sun yarda shafaffun da suka rage a duniya su “juya” su “zuwa adalci,” wato koya musu gaskiya game da Jehobah. (Dan. 12:3) Waɗannan mutanen sun kasance tare da Kiristoci shafaffu kuma sun tsarkake kansu daga bautar addinin ƙarya. Waɗannan “budurwai” na amaryar sun ba da kansu don su bauta wa Jehobah kuma sun kasance da aminci ga Angon, wato Sarkin.
15. Ta yaya “budurwai” na amarya suke aiki tare da shafaffu da suka rage a duniya?
15 Shafaffu da suka rage suna godiya sosai ga waɗannan “budurwai” na amarya domin yadda suke taimakawa a yin wa’azin ‘wannan bishara ta mulki’ da ƙwazo a duk faɗin duniya. (Mat. 24:14) “Ruhu da amarya suna cewa, Zo,” kuma masu ji suna cewa: “Zo.” (R. Yoh. 22:17) Hakan yana nufin cewa “waɗansu tumaki” sun ji shafaffu suna cewa “Zo,” kuma sun taya su cewa “Zo” ga dukan mazaunan duniya.—Yoh. 10:16.
16. Wane gata ne Jehobah ya danƙa wa waɗansu tumaki?
16 Shafaffu da suka rage a duniya suna ƙaunar waɗansu tumaki kuma suna farin ciki cewa Jehobah ya ba waɗansu tumaki gatan saka hannu a auren Ɗan rago. An annabta cewa za a kawo “budurwai” na amaryar “da murna da farin zuciya.” Hakika, waɗansu tumaki da suke da begen yin rayuwa a duniya har abada, za su yi farin ciki tare da mala’iku sa’ad da aka yi auren Ɗan ragon a sama. Littafin Ru’ya ta Yohanna ya ce “taro mai-girma” da suke bauta wa Jehobah a duniya, “suna tsaye gaban kursiyin da ke gaban Ɗan ragon.” Suna hidima ga Jehobah a farfajiyar duniya ta wannan haikali ta alama.—R. Yoh. 7:9, 15.
“’YA’YANKA ZA SU MAYE MATSAYIN UBANNINKA”
17, 18. Ta yaya mazaunan sabuwar duniya za su amfana daga auren Ɗan ragon, kuma Kristi zai zama uba ga su waye a lokacin Sarautarsa ta Shekara Dubu?
17 Karanta Zabura 45:16. “Budurwai” na amaryar Kristi a sama za su daɗa yin farin ciki sa’ad da suka ga sakamakon auren a sabuwar duniya. Yesu Kristi wanda shi ne Sarki zai ta da ‘ubanninsa’ na duniya kuma za su zama ‘’ya’yansa’ a duniya. (Yoh. 5:25-29; Ibran. 11:35) Yesu zai zaɓi wasu cikin waɗannan ‘’ya’yan’ su zama “sarakuna cikin dukan duniya.” Yesu zai kuma naɗa dattawa masu aminci a yau su yi ja-gora a sabuwar duniya.—Isha. 32:1.
18 Kristi zai zama uba ga waɗansu a lokacin Sarautarsa ta Shekara Dubu. A wace hanya? Waɗanda suka yi imani ga hadayar fansa ta Yesu za su yi rayuwa har abada a duniya. (Yoh. 3:16) A sakamako, Kristi zai zama “Uba madawwami” a gare su.—Isha. 9:6, 7.
ZA SU SO SU SANAR DA SUNANSA
19, 20. Ta yaya aukuwar da ke Zabura ta 45 ta shafi dukan Kiristoci?
19 Karanta Zabura 45:1, 17. Abin da ke Zabura ta 45 ya shafi dukan Kiristoci. Shafaffu da suka rage a duniya suna farin ciki domin sun san cewa nan ba da daɗewa ba, za su kasance tare da ’yan’uwansu da kuma Angon, wato Yesu Kristi. Waɗansu tumaki suna ci gaba da yin biyayya ga Sarkinsu kuma suna godiya don hidimar da suke yi tare da shafaffu da suka rage a duniya. Bayan auren, Kristi da waɗanda za su yi sarauta tare da shi za su albarkaci ’yan Adam a duniya sosai.—R. Yoh. 7:17; 21:1-4.
20 Yayin da muke jiran cikar wannan annabce-annabce game da Sarkin Mulkin Allah, babu shakka, hakan yana motsa mu mu sanar da sunansa. Bari mu yabi Sarkin “har abada abadin.”