Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 7/1 pp. 30-31
  • Mutum Mai Tawali’u da Gaba Gaɗi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mutum Mai Tawali’u da Gaba Gaɗi
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Darasi Game da Jin Ƙai na Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Halakar Saduma Da Gwamarata
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Yesu ya Warkar da Mutane ta Hanyar Mu’ujiza
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Yesu Ya Yi Tsayayya da Gwaji
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 7/1 pp. 30-31

Domin Matasa

Mutum Mai Tawali’u da Gaba Gaɗi

YUNANA—SASHE NA 1

Umurni: Ka yi wannan aikin a inda babu surutu. Sa’ad da kake karanta nassosi, ka sa kanka cikin yanayin. Ka yi tunanin yanayin a zuciyarka. Ka ji muryoyin mutanen. Ka ji yadda ainihin mutanen da ke ciki suke ji. Ka sa labarin ya kasance kamar yanzu yake faruwa.

1 KA YI TUNANI A KAN YANAYIN NAN.—KARANTA YUNANA 1:1-17; 2:10–3:5.

A ganinka, yaya ƙarar hadarin da yanayin yake?

․․․․․

A ganinka, wace irin murya ce kake jin take fitowa daga bakin Yunana da ta matuƙan jirgin ruwan?

․․․․․

Ka kwatanta abin da wataƙila Yunana yake tunani sa’ad da yake nitsewa cikin teku da kuma sa’ad da babban kifi ya haɗiye shi. (Karanta Yunana 2:1-9.)

․․․․․

2 KA BINCIKA SOSAI.

Waɗanne irin mutane ne suke zaune a Nineba, kuma menene wataƙila ya sa Yunana da farko ya yi jinkirin zuwa wurinsu? (Nahum 3:1)

․․․․․

Ta wace hanya ce kake ganin Nineba “babban birni” ne ga Allah? (Yunana 3:3; 2 Bitrus 3:9)

․․․․․

Menene fitowa fili da Yunana ya yi na yin magana game da kuskurensa da kuma Allahnsa ya nuna game da shi? (Sake karanta Yunana 1:9, 10.)

․․․․․

Ta yaya Yunana ya san abin da ya faru a cikin jirgin bayan an riga an jefa shi cikin tekun? (Sake karanta Yunana 1:15, 16.)

․․․․․

3 KA YI AMFANI DA ABIN DA KA KOYA. KA RUBUTA ABIN DA KA KOYA GAME DA . . .

Tsoron mutum.

․․․․․

Tawali’u.

․․․․․

Gaba gaɗi.

․․․․․

Ra’ayin Jehobah game da mutane, har da waɗanda suke kamar ba sa ƙaunarmu.

․․․․․

4 WANE ƁANGAREN WANNAN LABARIN NE YA FI MA’ANA A GARE KA, KUMA ME YA SA?

․․․․․

Don ƙarin bincike, ka duba Hasumiyar Tsaro, ta Janairu-Maris, 2009, shafuffuka na 25-28.

KA ƘARA KOYO GAME DA LITTAFI MAI TSARKI, A DUNIYAR GIZON www.watchtower.org DA www.jw.org

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba