Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 12/15 pp. 29-31
  • Littafi Mai Tsarki Ya Kai Babban Tsibirin Madagascar

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Littafi Mai Tsarki Ya Kai Babban Tsibirin Madagascar
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • An Soma Fassara
  • Jimrewa da Abubuwan da ke Jawo Koma Baya
  • Abin Ban Mamaki, Sai Kuma Baƙin Ciki
  • Mutanen Madagascar Suna Ƙaunar Littafi Mai Tsarki
  • Sun Ba da Kansu da Yardar Rai​—a Madagaska
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Jehobah, Allah Ne Mai Ma’amala da Mutane
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 12/15 pp. 29-31

Littafi Mai Tsarki Ya Kai Babban Tsibirin Madagascar

MADAGASCAR tana da nisan misalin mil 250 daga gaɓar teku na kudu masu gabashin Afirka, kuma tana ɗaya daga cikin manyan tsibirai huɗu da muke da su a duniya. Mutanen Madagascar sun san sunan Jehobah tun da daɗewa, domin fiye da shekaru 170 suna da fassarar Littafi Mai Tsarki na yaren Madagascar da yake ɗauke da sunan Allah. Yadda aka wallafa fassarar yaren Madagascar, labari ne na naciya da ba da kai.

An soma ƙoƙarce-ƙoƙarcen fassara Littafi Mai Tsarki zuwa yaren Madagascar ne a tsibirin Mauritius da ke kusa. Tun farkon shekarun 1813, Sir Robert Farquhar, gwamnan Mauritius ɗan Britaniya ne ya sa aka soma fassarar Linjila zuwa yaren Madagascar. Daga baya, ya ƙarfafa sarkin Madagascar, Radama na ɗaya, ya gayyaci malamai daga London Missionary Society (Ƙungiyar ’Yan Mishan a Landan) zuwa Babban Tsibirin Madagascar.

A ranar 18 ga Agusta, a shekara ta 1818, masu wa’azi a ƙasashen waje guda biyu, ’yan ƙasar Wales, David Jones da Thomas Bevan daga Mauritius suka isa tashar jirgin ruwa da ke birnin Toamasina. A wajen sun sami mutane masu bin addini sosai, waɗanda bautar kakanni da al’adar baki ta zama cibiyar rayuwarsu ta kullum. Mutanen Madagascar suna yin yare mai daɗi wanda ainihi tushensa daga ƙasashen Malayo da Polynesia ne.

Ba da daɗewa ba da buɗe wata ƙaramar makaranta, Jones da Bevan suka kawo matansu da yaransu daga Mauritius zuwa Toamasina. Amma, abin baƙin ciki, zazzaɓin cizon sauro ya kama dukan rukunin, kuma matar Jones da ’yarsa suka mutu a Disamba, a shekara ta 1818. Watanni biyu bayan hakan, ciwon ya kashe dukan iyalin Bevan. David Jones ne kaɗai ya tsira daga cikin rukunin.

Jones bai ƙyale bala’in ya hana shi ci gaba da abin da yake yi ba. Ya ƙudurta sa mutanen Madagascar su samu Kalmar Allah. Bayan ya koma Mauritius don ya warke daga ciwonsa, Jones ya soma aiki mai wuya na koyon yaren Madagascar. Ba da daɗewa ba, ya soma shirin aikin fassara Linjilar Yohanna.

A watan Oktoba na shekara ta 1820, Jones ya koma Madagascar. Ya sauka a babban birnin, Antananarivo, kuma ba da daɗewa ba ya buɗe sabon makaranta na ’yan mishan. Yanayin ba shi da kyau. Babu littattafai, allo, ko kuma tebura. Amma tsarin karatun yana da kyau sosai, kuma yaran suna ɗokin su samu ilimi.

Bayan ya yi aiki shi kaɗai wajen watanni bakwai, Jones ya samu wani sabon abokin aiki da zai ɗauki matsayin Bevan, wani ɗan ƙasar waje mai suna David Griffiths. Waɗannan mutane biyu sun ba da kansu sosai wajen fassara Littafi Mai Tsarki zuwa yaren Madagascar.

An Soma Fassara

A farkon shekarun 1820, ana kiran yaren Madagascar da ake rubutawa kaɗai sorabe, wato, kalaman yaren Madagascar da ake rubutawa da haruffan Larabci. Mutane kalilan ne kawai suke iya karanta shi. Saboda haka, sa’ad da ’yan mishan suka yi magana da Sarki Radama na ɗaya, sarkin ya ba da izinin yin amfani da harafi na Roma maimakon sorabe.

An soma fassarar a ranar 10 ga Satumba, a shekara ta 1823. Jones ya fassara Farawa da Matta, kuma Griffiths ya ɗauki Fitowa da Luka. Mazan sun yi aiki tuƙuru. Ban da yin yawancin fassarar da kansu, sun ci gaba da koyarwa a makarantar da safe da rana. Suna kuma shirya da kuma gudanar da ayyukan coci a harsuna uku. Duk da haka, sun fi mai da hankali ga aikin fassara fiye da kome.

Da taimakon ɗalibai 12, mutane biyun ’yan mishan sun fassara dukan Nassosi na Helenanci da kuma littattafai masu yawa na Nassosin Helenanci a cikin watanni 18 kawai. A shekara ta gaba, aka gama fassara dukan Littafi Mai Tsarki. Hakika, ana bukatar a yi gyara da canje-canje. Saboda haka, aka aiko da gwanayen harsuna guda biyu, David Johns da Joseph Freeman, daga Ingila don su ba da taimako.

Jimrewa da Abubuwan da ke Jawo Koma Baya

Sa’ad da aka gama fassarar, Ƙungiyar ’Yan Mishan a Landan suka aika da Charles Hovenden ya kafa inda ake wallafa littattafai na farko a Madagascar. Hovenden ya isa a ranar 21 ga Nuwamba, 1826. Amma, ya kamu da zazzaɓin cizon sauro kuma ya mutu cikin wata guda da isa wajen, kuma babu wanda zai iya tafiyar da na’urar. Shekara ta gaba, wani ƙwararren ɗan kasuwa, James Cameron daga Scotland, ya yi ƙoƙari ya tafiyar da wurin wallafa littattafan da taimakon littafin da ya gani a cikin na’urar. Bayan gwaje-gwaje masu yawa, Cameron ya wallafa sashen Farawa sura ta 1 a ranar 4 ga Disamba, shekara ta 1827.a

Wani ja da baya da aka samu ya faru ne a ranar 27 ga Yuli ta 1828, sa’ad da Radama ya mutu. Sarki Radama ya tallafa wa aikin fassarar sosai. David Jones ya faɗa a lokacin cewa: “Sarki Radama mutumin kirki ne kuma yana da fara’a. Ya goyi bayan samun ilimi sosai, da kuma ɗaukaka koyarwar mutanensa a fasaha na wayewar kai fiye da Zinariya da Azurfa.” Amma, matarsa Ranavalona ce ta gāji sarautar, kuma ba da daɗewa ba ya kasance a bayyane cewa ba za ta tallafa wa aikin ba yadda mijinta ya yi.

Ba da daɗewa ba, bayan da aka ɗaura sarauniyar a kan karaga, wani baƙo daga Ingila ya nemi izinin ya tattauna da sarauniyar game da aikin fassara. An ƙi ba shi izinin. A wani lokaci, sa’ad da ’yan mishan suka gaya wa sarauniyar cewa har ila suna da abubuwa da yawa da za su koya wa mutanen, har da Helenanci da Ibrananci, ta ce: “Ba ruwana da Helenanci da kuma Ibrananci, amma zan so na sani ko za ku iya koya wa mutanena wani abu mai amfani, kamar yin sabulu.” Da suka fahimci cewa ana iya tilasta musu su bar ƙasar kafin a gama Littafi Mai Tsarki a yaren Madagascar, Cameron ya ce a ba shi mako guda ya yi tunani game da abin da sarauniyar ta faɗa.

Bayan mako guda, Cameron ya nuna wa manzannin sarauniyar ƙananan sabulun yanka guda biyu da suka yi daga kayayyakin yankin. Wannan da wasu ayyuka da ’yan mishan suka yi sun sa sarauniyar farin ciki har suka gama wallafa kusan dukan littattafan Nassosin Ibrananci, kaɗan kawai ya rage.

Abin Ban Mamaki, Sai Kuma Baƙin Ciki

Duk da cewa da farko ta ƙi shawarar ’yan mishan, a Mayu a shekara ta 1831, sarauniyar ta ba da doka mai ban mamaki. Za ta yarda a yi wa talakawanta baftisma a matsayin Kiristoci! Amma wannan shawarar ba ta daɗe ba. In ji littafin nan A History of Madagascar, “yawan mutanen da suka yi baftisma ya tsorata fadawan sarki da ba sa son canje-canje, kuma suka ruɗi sarauniyar cewa cin jibi, yin rantsuwa ne na amincewa da mulkin Britaniya.” Saboda haka, a ƙarshen shekara ta 1831, an janye izinin yin baftisma na Kirista, watanni shida kawai da ba da izinin.

Rashin manne wa shawarar da sarauniyar ta tsai da, tare da ƙaruwar tasirin waɗanda suke bin al’ada a cikin gwamnatin, ya ƙarfafa ’yan mishan su hanzarta kammala buga Littafi Mai Tsarkin. An riga an gama Nassosin Helenanci na Kirista, kuma an soma rarraba dubbansu. Amma, an samu wani mahani a ranar 1 ga Maris, a shekara ta 1835, sa’ad da Sarauniya Ranavalona ta ɗaya ta haramta Kiristanci kuma ta ba da umurni a miƙa wa masu mulki dukan littattafai na Kirista.

Umurnin sarauniyar yana kuma nufin cewa dukan ’yan Madagascar masu koyan aiki ba za su ƙara yin aiki a inda ake wallafa littafin ba. Tun da yake ’yan mishan kalilan ne suka rage su gama aikin, sun yi aiki dare da rana har sai a ƙarshe, a watan Yuni na shekara ta 1835, aka fito da Littafi Mai Tsarki da aka fassara gabaki ɗaya a yaren. A ƙarshe an wallafa Littafi Mai Tsarki a yaren Madagascar!

Sa’ad da ake shirin a kafa hanin, an rarraba Littafi Mai Tsarki nan da nan, kuma aka binne Littafi Mai Tsarki guda 70 don kada a halaka su gabaki ɗaya. Hakan shawara ce mai kyau domin kafin shekara guda ’yan mishan guda biyu ne kawai suka rage a tsibirin. Amma, kalmar Allah tana yaɗuwa a Babban Tsibiri Madagascar.

Mutanen Madagascar Suna Ƙaunar Littafi Mai Tsarki

Abin farin ciki ne mutanen Madagascar su karanta Kalmar Allah a yarensu! Akwai kuskure a fassarar, kuma yanzu ana ɗaukan yaren a matsayin tsohon yayi. Duk da haka, da kyar ne a ga gidan da babu Littafi Mai Tsarki, kuma mutanen Madagascar da yawa suna karanta shi a kai a kai. Abu na musamman game da wannan fassarar shi ne cewa ta yi amfani da sunan Allah, Jehobah, sosai a dukan Nassosin Ibrananci. A littattafai na asali, sunan Allah yana cikin Nassosin Helenanci kuma. Saboda haka, yawancin mutanen Madagascar sun san sunan Allah.

Hakika, sa’ad da aka buga littattafan Nassosin Helenanci na farko a inda ake buga littattafai, mai buga littattafan, Malam Baker, ya ga yadda mutanen Madagascar suke farin ciki kuma ya ce: “Ba na nufin yin annabci, amma ba zan gaskata ba cewa za a taɓa kawar da kalmar Allah daga wannan ƙasar ba.” Kalamansa sun zama gaskiya. Zazzaɓin cizon sauro da kuma ƙalubalen koyon yare mai wuya har da dokoki masu tsanani na sarki ba su hana Kalmar Allah ta wanzu a Madagascar ba.

Yanzu yanayin ya ƙara yin kyau. Ta yaya? A shekara ta 2008, an fito da cikakken fassarar New World Translation of the Holy Scriptures a yaren Madagascar. Wannan fassara ci gaba ne mai girma domin an fassara shi a yare na zamani mai sauƙin fahimta. Saboda haka, an ƙafa Kalmar Allah sosai a Babban Tsibirin Madagascar.—Isha. 40:8.

[Hasiya]

a Dokoki Goma da Addu’ar Ubangiji, da aka wallafa a birnin Mauritius a misalin watan Afrilu/Mayu na shekara ta 1826, sune sashe na farko na Littafi Mai Tsarki da aka wallafa a Malagasy. Amma an rarraba littattafan ne kawai ga iyalin Sarki Radama da wasu manyan ma’aikatan gwamnati.

[Hotunan da ke shafi na 31]

Fassarar “New World Translation” a yaren Madagascar ta ɗaukaka sunan Allah, Jehobah

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba