Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 10/1 pp. 4-7
  • Za Ka Iya Kasancewa da Bangaskiya Ta Gaske

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Za Ka Iya Kasancewa da Bangaskiya Ta Gaske
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ‘Ka Nemi Allah . . . Kuma Ka Same Shi’
  • Kana Bukatar Littafi Mai Tsarki
  • “Bangaskiya fa Daga Wurin Ji Ne”
  • Za Ka Iya Koyon Bangaskiya ta Gaske
  • “Har Yaushe . . . Zan Yi Kira?”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Allah Ya Kira Ta Sarauniya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
  • Da Gaske Ka Ba Da Gaskiya Ga Bisharar?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • “Ka Kara Mana Bangaskiya”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 10/1 pp. 4-7

Za Ka Iya Kasancewa da Bangaskiya Ta Gaske

Sa’ad da Sarah Jayne take ’yar shekara 19, aka gaya mata tana da ciwon daji kusa da mahaifarta. Bayan da aka yi mata aiki, kamar ta samu sauƙi, ta yi murna da zato na nan gaba. Ta yi gaba gaɗi sosai, da ta kai shekara 20, ta soma zawarci kuma ta yi shiri za ta yi aure. A shekarar kuma sai ciwon ya dawo, sai aka ce mata makonni kawai suka rage mata ta mutu. Sarah Jayne ta mutu a Yuni, 2000 kafin ta kai shekara 21.

ABIN da ya burge baƙi da suka ziyarci Sarah Jayne a asibiti shi ne gaba gaɗinta game da nan gaba, da zurfafar bangaskiyarta ga Allah da kuma Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. Duk da wuyar da take sha, tana da gaba gaɗi a kan begen tashin matattu—cewa za ta sake ganin dukan abokananta. (Yohanna 5:28, 29) Ta ce: “Zan sadu da ku duka cikin sabuwar duniya ta Allah.”

Wasu sun ce irin bangaskiyar nan ruɗu ce kawai. “Imanin cewa akwai rai bayan mutuwa imani ne na marasa kwanciyar rai,” in ji Ludovic Kennedy, “wai bayan an hura ƙaho na ƙarshe za a more ababa masu armashi, wai za su more kuma cikin Adnin wanda ya cika da ganyaye lokatai ne na farin ciki tare da waɗanda suka mutu da kuma wasu da za su mutu a bayansu?” Saboda haka, dole ne mu yi tambayar nan da ta saɓa wa waccan. Wacce ta fi amfani—a gaskata cewa “rayuwar nan kawai muke da ita, domin haka ya dace mu more ta sosai,” yadda Kennedy ya ba da shawara, ko kuma a gaskata ga Allah da alkawarinsa na tashin matattu? Sarah Jayne ta zaɓi na ƙarshen. Ta yaya ta gina irin bangaskiyar nan?

‘Ka Nemi Allah . . . Kuma Ka Same Shi’

Don ka koyi bangaskiya da dogara ga wani, kana bukatar saninsa kuma ka koyi yadda yake tunani da kuma yadda yake aikata abubuwa. Wannan tsari ya shafi zuciya da kuma azanci. Ɗaya suke idan ya zo zancen koyon bangaskiya ta gaske ga Allah. Kana bukatar ka san shi, ka koyi game da halayensa da mutumtakarsa, ka sami tabbaci yadda za a iya dogara a gare shi a dukan abubuwan da ya faɗa da kuma ya yi.—Zabura 9:10; 145:1-21.

Wasu suna jin wannan ba zai yiwu ba. Sun ce, Allah yana da nisa ainun kuma ba a fahimtarsa—idan ma ya wanzu ke nan. “Idan da gaske Allah yana nan yadda ya kasance ga Kiristoci kamar su Sarah Jayne,” in ji mai sukār, “me ya sa bai sa sauranmu mu san shi ba?” Amma da gaske ne cewa Allah yana da nisa ainun da ba za a iya nemansa ba? A wani furci ga ’yan falsafa da haziƙai a Atina, manzo Bulus ya ce “Allah wanda ya yi duniya da abin da ke ciki duka” ya kuma yi tanadi da dukan mutane suke bukata don su ‘neme shi . . . kuma su same shi.’ Hakika Bulus ya ce: “Ba shi da nisa da kowane ɗayanmu ba.”—Ayukan Manzanni 17:24-27.

To, ta yaya za ka iya ‘neman Allah . . . kuma ka same shi’? Wasu sun yi haka ta lura da sararin samaniya da ya kewaye su. Ga mutane da yawa, tabbaci ne da zai tabbatar musu cewa da akwai Mahalicci.a (Zabura 19:1; Ishaya 40:26; Ayukan Manzanni 14:16, 17) Sun yi tunani daidai da na manzo Bulus, cewa “halittar duniya al’amura na [Allah] da ba su ganuwa, watau ikonsa madawwami da allahntakarsa, a sarari a ke ganinsu; ta wurin abubuwa da an halitta ana gane su.”—Romawa 1:20; Zabura 104:24.

Kana Bukatar Littafi Mai Tsarki

Don ka koyi kasancewa da bangaskiya ga Mahalicci, kana bukatar wani abu dabam da ya yi tanadinsa. Menene? Littafi Mai Tsarki—hurariyar Kalmar Allah, wadda a ciki ya bayyana nufi da kuma ƙudurinsa. (2 Timothawus 3:16, 17) “Amma dakata,” in ji wasu, “ta yaya za ka iya gaskata kome da Littafi Mai Tsarki ya faɗa yayin da ka ke ganin munanan abubuwa da mutanen da suke da’awar bin Littafi Mai Tsarki suke aikatawa?” Hakika, Kiristendam ba shi da tarihin kirki a batun riya, zalunci, da kuma lalata. Amma kowanne mutum mai hankali zai iya ganin cewa lamuni kawai Kiristendam suke yi cewa suna bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki.—Matta 15:8.

Littafi Mai Tsarki ya yi gargaɗi cewa mutane da yawa za su yi da’awar suna bauta wa Allah, amma, “suna musun Ubangijin da ya saye su.” “Saboda su,” in ji manzo Bitrus, “za a yi kushen hanyar gaskiya.” (2 Bitrus 2:1, 2) Yesu Kristi ya ce waɗannan “masu-aika mugunta” ne da ake saninsu ta mugunta da suke aikatawa. (Matta 7:15-23) Idan ka yi banza da Kalmar Allah saboda tarihin Kiristendam, kamar jefar da wasiƙa ce wadda aboki na kud da kud ya rubuta maka domin kawai wani mugu ne ya kawo maka wasiƙar.

Idan ba tare da Kalmar Allah ba, ba zai yiwu a koyi bangaskiya ta gaske ba. A cikin ayoyin Littafi Mai Tsarki ne kaɗai za a ce Jehovah ya bayyana abubuwa nasa. Ya bayyana amsoshin irin tambayoyin nan da sun daɗe kamar su, abin da ya sa ya ƙyale wahala da ciwo kuma abin da zai yi game da yanayin. (Zabura 119:105; Romawa 15:4) Sarah Jayne ta gaskata cewa Littafi Mai Tsarki hurariyar Kalmar Allah ce. (1 Tassalunikawa 2:13; 2 Bitrus 1:19-21) Ta yaya? Ba kawai domin iyayenta sun gaya mata ba, amma ta nemi lokaci ta bincika da gaske dukan tabbaci da sun nuna cewa Littafi Mai Tsarki wahayi ne mai girma daga Allah. (Romawa 12:2) Alal misali, ta lura da ikon da Littafi Mai Tsarki yake da shi a rayuwar waɗanda suke bin ƙa’idodinsa. Da taimakon littattafai kamar su The Bible—God’s Word or Man’s?,b ta kuma bincika a hankali tabbaci da sun tabbatar da hurewarsa daga Allah.

“Bangaskiya fa Daga Wurin Ji Ne”

Mutum ya kasance da Littafi Mai Tsarki kawai ko ya gaskata cewa an hure shi bai isa ba. “Bangaskiya,” in ji manzo Bulus, “daga wurin ji ne.” (Romawa 10:17) Jin Littafi Mai Tsarki, ba kawai kana da Littafi Mai Tsarki ba ne ke gina bangaskiya. Ka “ji” abin da Allah ke faɗa ta karanta Kalmarsa da kuma nazarinta. Har matasa ma za su iya yin haka. Bulus ya ce “daga jariri” uwar Timothawus da kakarsa suka koya masa “littattafai masu-tsarki.” Wannan ya nuna cewa an tilasta masa wata koyarwa ne? A’a! Ba a mallaki ko kuma ruɗe Timothawus ba. Ya “tabbata” abin da ya ji da kuma wanda ya karanta.—2 Timothawus 1:5; 3:14, 15.

Haka ma Sarah Jayne ta tabbata. Kamar mutanen Biriya na ƙarni na farko, ta “karɓi magana [daga iyayenta da wasu malamai] da yardar rai sarai.” Da take ’yar yarinya, babu shakka ta dogara ƙwarai ga abin da iyayenta suka gaya mata. Daga baya, da ta yi girma, ba ta bi kawai ba ko ta yarda da kome da aka koya mata ba. Tana ‘bincika Nassosi ko waɗannan al’amura haka suke.’—Ayukan Manzanni 17:11.

Za Ka Iya Koyon Bangaskiya ta Gaske

Kai ma za ka iya koyon bangaskiya ta gaske—irin bangaskiyar da manzo Bulus ya kwatanta cikin wasiƙarsa zuwa ga Kiristoci Ibraniyawa. Irin wannan bangaskiyar, in ji shi, ita ce “ainihin abin da mu ke begensa ne, tabbatawar al’amuran da ba a gani ba.” (Ibraniyawa 11:1) Kasancewa da irin wannan bangaskiyar, za ka tabbata cewa dukan begenka da zato har da alkawarin Allah na tashin matattu, za su cika. Za ka tabbata cewa irin begen nan tabbatattu ne, ba wani sha’awa kawai ba. Za ka sani cewa Jehovah bai taɓa kasa cika alkawuransa ba. (Joshua 21:45; 23:14; Ishaya 55:10, 11; Ibraniyawa 6:18) Sabuwar duniya ta Allah za ta zama da gaske a gare ka kamar kana cikinta. (2 Bitrus 3:13) Za ka gani sarai da idanun bangaskiya cewa Jehovah Allah, Yesu Kristi, da Mulkin Allah dukansu tabbatattu ne, ba ruɗu ba.

Ba da ƙoƙarin kanka kawai za ka gina bangaskiya ta gaske ba. Ban da ba da Kalmarsa ga kowa, Jehovah ya kuma yi tanadin ikilisiya a duniya duka da suke ba da kai a taimakon mutane masu zuciyar kirki su gina bangaskiya ga Allah. (Yohanna 17:20; Romawa 10:14, 15) Ka amince da dukan taimako da Jehovah ya yi tanadinsa ta wurin ƙungiyar nan. (Ayukan Manzanni 8:30, 31) Kuma tun da yake bangaskiya ɗiyar ruhu mai tsarki ne na Allah, ka yi addu’a dominsa kullum don ya taimake ka gina bangaskiya ta gaske.—Galatiyawa 5:22.

Kada ka girgiza don ba’a da masu sukā suke wa duk wani da yake da’awar bangaskiya ga Allah da kuma Kalmarsa. (1 Korinthiyawa 1:18-21; 2 Bitrus 3:3, 4) Hakika, bangaskiya ta gaske tana da amfani mai ƙarfafawa don ka iya tsayawa don irin farmakin nan. (Afisawa 6:16) Sarah Jayne ta iske wannan gaskiya, kuma kullum tana ƙarfafa waɗanda suka ziyarce ta a asibiti su gina bangaskiyarsu. “Ku maida gaskiya taku,” in ji ta. “Ku yi nazarin Kalmar Allah. Ku tsaya kusa da ƙungiyar Allah. Ku yi addu’a kullum. Ku yi ƙwazo cikin hidimar Jehovah.”—Yaƙub 2:17, 26.

Da ta ga bangaskiyarta ga Allah da kuma ga tashin matattu, ɗaya cikin nas da suke kula da ita ta ce: “Hakika kin tabbata da wannan.” Da aka tambaye ta abin da ya sa take da irin wannan begen duk da jarabobinta, ta ce: “Bangaskiya ce ga Jehovah. Aboki ne na gaske a gare ni, kuma ina ƙaunarsa sosai.”

[Hasiya]

a Duba littafin nan Is There a Creator Who Cares About You?, wanda Shaidun Jehovah suka buga.

b Wanda Shaidun Jehovah suka buga.

[Hoto a shafi na 6]

“Daga jariri” uwar Timothawus da kakarsa suka koya masa “littattafai masu-tsarki”

[Hoto a shafi na 6]

An yaba wa mutanen Biriya game da binciken Nassosi da suke yi kullum

[Inda aka Dauko]

Daga “Photo-Drama of Creation,” shekara ta 1914

[Hotuna a shafi na 7]

Ji da kuma bin Littafi Mai Tsarki ne, ba kasancewa da shi ne, ke gina bangaskiya ba

[Hoto a shafi na 7]

“Zan ga dukanku a sabuwar duniya ta Allah”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba