Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 10/15 pp. 13-17
  • “Ku Ne Abokaina”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ku Ne Abokaina”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Misalin Yesu na Zama Abokin Kirki
  • Yaya Almajiran Suka Karɓi Abotar Yesu?
  • Abota da Kristi a Yau
  • Inda Za Mu Samu Abokan Kirki
  • “Ina Ce da Ku Abokai”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Yadda Za A Ci Gaba Da Abuta A Duniya Marar Ƙauna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ka Yi Abokantaka da Masu Kaunar Allah
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Ka Yi Koyi da Yesu Don Ka Kasance da Kwanciyar Rai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 10/15 pp. 13-17

“Ku Ne Abokaina”

“Ku ne abokaina idan kun yi abin da na umurce ku.”—YOH. 15:14.

1, 2. (a) Waɗanne irin mutane ne abokan Yesu? (b) Me ya sa yake da muhimmanci mu zama abokan Yesu?

MAZAN da suke tare da Yesu a gidan bene, mutane ne iri iri. Bitrus da Andarawas masu kamun kifi ne. Matta a dā mai karɓan haraji ne, yana aikin da Yahudawa suka tsana. Wasu cikinsu, kamar Yaƙub da Yohanna, wataƙila sun san Yesu tun yana yaro. Sauran, kamar Natanayilu, wataƙila sun san shi na ’yan shekaru kawai. (Yoh. 1:43-50) Duk da haka, dukansu da suka taru a wannan dare na Idin Ƙetarewa mai muhimmanci a Urushalima suna da tabbaci cewa Yesu ne Almasihu da aka yi alkawarinsa, Ɗan Allah mai rai. (Yoh. 6:68, 69) Babu shakka, ya daɗaɗa zuciyarsu da suka ji ya gaya musu: “Na ce da ku abokai; gama dukan abin da na ji daga wurin Ubana, na sanar muku da su.”—Yoh. 15:15.

2 Waɗannan kalaman Yesu ga manzanninsa masu aminci sun shafi dukan shafaffu Kiristoci a yau da kuma abokanansu “waɗansu tumaki.” (Yoh. 10:16) Ko menene tushenmu, za mu iya samun gatar zaman abokan Yesu. Abotarmu da shi tana da muhimmanci sosai domin zaman abokansa yana sa mu zama abokan Jehobah ma. Hakika, ba zai yiwu ba mu kusaci Jehobah idan ba mu fara kusaci Kristi ba. (Karanta Yohanna 14:6, 21.) To, menene muke bukatar mu yi don mu zama abokan Yesu kuma mu ci gaba da zama hakan? Kafin mu tattauna wannan batu mai muhimmanci, bari mu bincika misalin Yesu na zama abokin kirki kuma mu ga abin da za mu iya koya daga yadda almajiransa suka aikata domin yin abuta da shi.

Misalin Yesu na Zama Abokin Kirki

3. Menene aka san Yesu da shi?

3 Sarki Sulemanu mai hikima ya rubuta: “Mai-arziki yana da abokai da yawa.” (Mis. 14:20) Waɗannan kalaman sun nuna halin ’yan adam ajizai, suna ƙulla abota don abin da za su samu maimakon abin da za su iya bayarwa. Yesu bai nuna irin wannan kasawar ba. Arzikin mutum ko kuma matsayinsa bai rinjaye shi ba. Hakika, Yesu ya ƙaunaci masarauci saurayi mai arziki kuma ya gayyace shi ya zama mabiyinsa. Amma, Yesu ya gaya wa wannan mutumin ya sayar da abin da yake da shi ya ba talakawa. (Mar. 10:17-22; Luk 18:18, 23) Yesu sananne ne ba don tarayyarsa da mawadata da kuma mashahurai ba amma don yana abokantaka da matalauta da waɗanda aka rena.—Mat. 11:19.

4. Me ya sa za a ce abokan Yesu masu yin kuskure ne?

4 Hakika, abokan Yesu masu yin kuskure ne. A wani lokaci Bitrus bai ɗauki al’amura yadda Allah ya yi ba. (Mat. 16:21-23) Yakubu da Yohanna sun nuna suna son iko sa’ad da suka gaya wa Yesu ya ba su matsayi masu girma a Mulkinsa. Abin da suka yi ya sa sauran manzannin fushi, kuma sun ci gaba da yin jayayya game da batun matsayi. Amma, Yesu ya yi ƙoƙari ya daidaita tunanin abokansa cikin haƙuri kuma bai yi saurin fushi da su ba.—Mat. 20:20-28.

5, 6. (a) Me ya sa Yesu ya ci gaba da abota da yawancin manzanninsa? (b) Me ya sa Yesu ya daina abokantaka da Yahuda?

5 Yesu bai ci gaba da abota da waɗannan mutane ajizai domin yana ƙyaliya ko kuma bai ga ajizancinsu ba. Maimakon haka, ya zaɓa ya mai da hankali ga muradinsu da halinsu masu kyau. Alal misali, Bitrus, Yaƙub, da Yohanna sun yi barci maimakon su tallafa wa Yesu a lokaci mafi wuya a rayuwarsa. Babu shakka sun ɓata wa Yesu rai. Duk da haka, ya ga cewa suna da muradi mai kyau, kuma ya ce: “Ruhu lallai ya yarda, amma jiki rarrauna ne.”—Mat. 26:41.

6 Akasin haka, Yesu ya daina abota da Yahuda Iskariyoti. Ko da yake Yahuda ya nuna a waje cewa shi abokin kirki ne, Yesu ya lura cewa wannan amininsa na dā ya ƙyale zuciyarsa ta lalace. Domin Yahuda ya zama abokin duniya, ya mai da kansa maƙiyin Allah. (Yaƙ. 4:4) Saboda haka, Yesu ya riga ya sallami Yahuda sa’ad da ya sanar da abotarsa ga sauran manzanninsa goma sha ɗaya masu aminci.—Yoh. 13:21-35.

7, 8. Ta yaya Yesu ya nuna ƙaunarsa ga abokansa?

7 Yesu bai mai da hankali ga laifin aminansa ba amma ya yi abin da zai fi musu kyau. Alal misali, ya yi addu’a ga Ubansa ya kāre su a lokacin da suke fuskantar gwaji. (Karanta Yohanna 17:11.) Yesu ya yi la’akari da kasawarsu. (Mar. 6:30-32) Bai gaya musu ra’ayinsa ba kawai amma ya so ya ji kuma ya fahimci abin da suke tunani da kuma yadda suke ji.—Mat. 16:13-16; 17:24-26.

8 Yesu ya yi amfani da rayuwarsa da kuma mutuwarsa don ya amfani abokansa. Hakika, ya san cewa dole ne ya miƙa ransa a matsayin abin da doka take bukata don ya gamsar da mizanan adalci na Ubansa. (Mat. 26:27, 28; Ibran. 9:22, 28) Amma Yesu ya ba da ransa don ya nuna ƙaunarsa. Yesu ya ce: “Ba wanda yake da ƙauna wadda ta fi gaban wannan, wato mutum ya bada ransa domin abokansa.”—Yoh. 15:13.

Yaya Almajiran Suka Karɓi Abotar Yesu?

9, 10. Yaya mutane suka aikata ga alherin Yesu?

9 Yesu ya ba da lokacinsa, ƙauna, da abubuwan biyan bukata sosai. A sakamakon haka, mutane sun kusace shi kuma sun yi farin ciki su yi masa hidima da dukiyarsu. (Luk 8:1-3) Saboda abin da ya shaida, Yesu ya ce: “Ku bayar, za a ba ku, mudu mai-kyau, danƙararre, girgizajje, mai-zuba, za su bayar cikin ƙirjinku. Gama da mudun da ku ke aunawa, da shi za a auna muku.”—Luk 6:38.

10 Hakika, wasu sun yi ƙoƙari su yi tarayya da Yesu don kawai abin da za su samu daga wajensa. Waɗannan abokan ƙarya sun yasar da Yesu sa’ad da ba su fahimci abin da ya faɗa ba. Maimakon su amince da Yesu sa’ad da ba su fahimci abin da ya faɗa ba, sai suka kammala yadda bai dace ba kuma suka ƙi shi. Akasin haka, manzanninsa sun kasance da aminci. Sau da yawa an gwada abotarsu da Kristi, amma sun yi iyakar ƙoƙarinsu don su tallafa masa a lokacin farin ciki da kuma na baƙin ciki. (Karanta Yohanna 6:26, 56, 60, 66-68.) A darensa na ƙarshe a matsayin mutum a duniya, Yesu ya furta yawan yadda yake ƙaunar abokansa, yana cewa: “Ku ne waɗanda kun lizimce ni a cikin kuncina.”—Luk 22:28.

11, 12. Yaya Yesu ya sake tabbatar wa almajiransa, kuma yaya suka aikata?

11 Ba da daɗewa ba, bayan Yesu ya yabi almajiransa don amincinsu, sai suka yashe shi. Sun ƙyale tsoron mutane ya sha kan ƙaunarsu ga Kristi na ɗan lokaci. Yesu kuma ya gafarta musu. Bayan mutuwarsa da kuma tashinsa daga matattu, ya bayyana musu kuma ya sake tabbatar musu da abotarsa. Bugu da ƙari, ya ɗanka musu aiki mai tsarki, wato, su almajirtar da mutanen “dukan al’ummai” su zama shaidunsa “har kuma iyakan duniya.” (Mat. 28:19; A. M. 1:8) Yaya almajiransa suka aikata?

12 Almajiransa sun yi iyakar ƙoƙarinsu don su yaɗa saƙon Mulkin. Da taimakon ruhu mai tsarki na Jehobah, ba da daɗewa ba suka cika Urushalima da koyarwarsu. (A. M. 5:27-29) Har barazanar kisa bai hana su bin umurnin Yesu na almajirantarwa ba. Cikin ’yan shekaru na samun umurnin Yesu, manzo Bulus ya rubuta cewa an yi wa’azin bishara “cikin dukan halitta da ke ƙarƙashin sama.” (Kol. 1:23) Babu shakka, waɗannan almajirai sun nuna cewa sun ɗauki abotarsu da Yesu da tamani!

13. Almajiran Yesu sun ƙyale koyarwar Yesu ta shafe su a waɗanne hanyoyi?

13 Waɗanda suka zama almajirai sun ƙyale koyarwar Yesu ta shafi rayuwarsu. Ga mutane da yawa, hakan yana nufin yin canje-canje sosai a halinsu da kuma mutuntakarsu. Wasu sababbin almajiran a dā ’yan luwaɗi ne, mazinata, mashaya, ko ɓarayi. (1 Kor. 6:9-11) Wasu sun canja irin mugun halin da suke nuna wa ’yan wata ƙabila. (A. M. 10:25-28) Duk da haka, sun yi biyayya ga Yesu. Sun tuɓe halinsu na dā kuma suka saka sabo. (Afis. 4:20-24) Ta hakan sun san “nufin Kristi,” suka fahimci da kuma yi koyi da yadda yake tunani da aikatawa.—1 Kor. 2:16.

Abota da Kristi a Yau

14. Menene Yesu ya yi alkawari zai yi a “cikar zamani”?

14 Yawancin Kiristoci a ƙarni na farko sun san Yesu ko kuma sun gan shi bayan tashinsa daga matattu. Hakika ba mu samu irin wannan gatar ba. To, ta yaya za mu iya zama abokan Kristi? Hanya ɗaya ita ce ta kiyaye umurnin da bawan nan mai-aminci, mai-hikima yake bayarwa, waɗanda sun haɗa da ’yan’uwan Yesu shafaffu da har ila suke raye a duniya. Yesu ya yi alkawari cewa a “cikar zamani,” zai naɗa wannan bawan “bisa dukan abin da ya ke da shi.” (Mat. 24:3, 45-47) A yau, yawancin mutane da suke nema su zama abokan Kristi ba sa cikin rukunin wannan bawan. Ta yaya yadda suke aikata ga umurnin da suka samu daga rukunin bawan nan mai aminci yake shafan abotarsu da Kristi?

15. Menene yake nuna cewa mutum zai kasance cikin rukunin tumaki ko kuma awakai?

15 Karanta Matta 25:31-40. Yesu ya kira waɗanda za su kasance cikin rukunin bawan nan mai aminci ’yan’uwansa. A cikin kwatancin da ya yi game da ware tumaki da awakai, Yesu ya bayyana sarai cewa yana ɗaukan yadda muke bi da ’yan’uwansa a matsayin muna bi da shi ne. Ya kuma ce abin da zai bambanta tumaki da awakai zai zama yadda mutum yake bi da ‘waɗannan ’yan’uwansa mafiya ƙanƙanta.’ Saboda haka, hanya ta musamman da waɗanda suke da begen zama a duniya suke nuna cewa suna son su zama abokan Kristi ita ce ta wajen tallafa wa rukunin bawan nan mai aminci.

16, 17. Ta yaya za mu iya nuna abotarmu ga ’yan’uwan Kristi?

16 Idan kana da begen zama a duniya a cikin Mulkin Allah, ta yaya za ka iya nuna abotarka ga ’yan’uwan Kristi? Bari mu bincika hanyoyi uku kawai. Na farko, ta wajen sa hannu a cikin aikin wa’azi da zuciya ɗaya. Kristi ya umurci ’yan’uwansa su yi wa’azin bishara a dukan duniya. (Mat. 24:14) Amma, zai yi wa ’yan’uwan Kristi da suka rage a duniya a yau wuya su cim ma wannan hakki ba tare da taimakon abokansu waɗansu tumaki ba. Hakika, a kowane lokaci da waɗanda suke cikin rukunin waɗansu tumaki suka yi aikin wa’azi, suna taimakon ’yan’uwan Kristi su cika aikinsu mai tsarki. Rukunin bawan nan mai aminci mai hikima suna godiya don wannan hali na abota yadda Kristi yake godiya.

17 Hanya ta biyu da waɗanda suke cikin rukunin waɗansu tumaki za su iya taimaka wa ’yan’uwan Kristi ita ce ta wajen tallafa wa aikin wa’azi ta ba da kyautar kuɗi. Yesu ya ƙarfafa mabiyansa su yi abokai ta wurin “dukiya ta rashin gaskiya.” (Luk 16:9) Hakan ba ya nufin cewa za mu iya sayan yin abota da Yesu ko kuma Jehobah. Maimakon haka, ta wajen yin amfani da dukiyarmu don mu tallafa wa al’amuran Mulki, muna nuna abotarmu da ƙaunarmu, ba kawai ta maganar baki ba amma “da aiki da gaskiya kuma.” (1 Yoh. 3:16-18) Muna ba da irin wannan taimakon kuɗi sa’ad da muke aikin wa’azi, sa’ad da muka ba da kuɗi don gina da kuma kula da wuraren taronmu, da kuma sa’ad da muka ba da kuɗi don aikin wa’azi na dukan duniya. Ko da kuɗin da muka ba da kaɗan ne ko kuma da yawa, Jehobah da Yesu suna godiya don bayarwarmu da farin ciki.—2 Kor. 9:7.

18. Me ya sa za mu bi umurni da ke bisa Littafi Mai Tsarki da dattawan ikilisiya suka ba mu?

18 Hanya ta uku da dukanmu za mu nuna cewa mu abokan Kristi ne ita ce ta wajen ba da haɗin kai ga ja-gorancin dattawan ikilisiya. Ruhu mai tsarki ne ya naɗa waɗannan maza ta wajen ja-gorar Kristi. (Afis. 5:23) Manzo Bulus ya rubuta: “Ku yi biyayya da waɗanda ke shugabanninku, ku sarayar da kanku gare su.” (Ibran. 13:17) A wasu lokatai, yana iya yi mana wuya mu yi biyayya ga ja-gora da ke bisa Littafi Mai Tsarki da dattawa suka ba mu. Mai yiwuwa, mun san da ajizancinsu, kuma hakan na iya sa kada mu bi gargaɗinsu. Duk da haka, Kristi, Shugaban ikilisiya yana farin cikin yin amfani da waɗannan maza ajizai. Saboda haka, yadda muke aikatawa ga ikonsu yana shafan abotarmu da Kristi kai tsaye. Sa’ad da muka ƙyale laifofin dattawa kuma muka bi ja-gorarsu da farin ciki, muna nuna ƙaunarmu ga Kristi.

Inda Za Mu Samu Abokan Kirki

19, 20. Menene za mu iya samu a cikin ikilisiya, kuma menene za mu bincika a gaba?

19 Yesu ya ci gaba da kula da mu ba kawai ta kulawar dattawa ba amma ta wajen uwaye na ruhaniya da kuma ’yan’uwa maza da mata a cikin ikilisiya. (Karanta Markus 10:29, 30.) Sa’ad da ka fara tarayya da ƙungiyar Jehobah, yaya dangoginka suka aikata? Mai yiwuwa, sun tallafa wa ƙoƙarce-ƙoƙarcenka na kusantar Allah da Kristi. Amma Yesu ya yi kashedi cewa a wani lokaci “maƙiyan mutum za su kasance daga iyalin gidansa.” (Mat. 10:36) Yana da ban ƙarfafa mu san cewa a cikin ikilisiya, za mu samu waɗanda za su ƙaunace mu fiye da ’yan’uwa na zahiri!—Mis. 18:24.

20 Kamar yadda gaisuwar Bulus a ƙarshen wasiƙarsa zuwa ga Romawa ta nuna, ya ƙulla abota da yawa na kud da kud. (Rom. 16:8-16) Manzo Yohanna ya kammala wasiƙarsa ta uku da waɗannan kalmomi: “A gaida abokai da sunansu.” (3 Yoh. 14) Babu shakka, shi ma ya yi abota masu yawa da suka daɗe. Ta yaya za mu iya yin koyi da misalin Yesu da almajirai na farko ta wajen ƙulla da kuma ci gaba da yin abota da ’yan’uwanmu na ruhaniya? Talifinmu na gaba zai ba da amsar wannan tambayar.

Yaya Za Ka Amsa?

• Wane misali ne Yesu ya kafa na zama abokin kirki?

• Yaya almajiran suka aikata ga abutar Yesu?

• Ta yaya za mu nuna cewa mu abokan Kristi ne?

[Hotunan da ke shafi na 14]

Yesu yana son ya san tunanin abokansa da kuma yadda suke ji

[Hotunan da ke shafi na 16]

Ta yaya za mu nuna cewa muna son mu zama abokan Kristi?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba