Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 10/15 p. 12
  • Tambayoyi Daga Masu Karatu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tambayoyi Daga Masu Karatu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Makamantan Littattafai
  • Aure, Kyauta ne Daga Allah Mai Kauna
    “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
  • Aure Kyauta Ne Daga Allah
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • “Almasihu Ne Shugaban Kowane” Namiji
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Rayuwar Iyali da ke Gamshe Allah
    Menene Allah Yake Bukata a Garemu?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 10/15 p. 12

Tambayoyi Daga Masu Karatu

Wane darassi ne aka koyar a Karin Magana 24:27?—Littafi Mai Tsarki.

Sa’ad da yake ba da shawara ga wani saurayi, marubucin Misalai ya ce: “Ka shirya aikinka a waje, ka shirya wa kanka kuma cikin gona; daga baya kuma ka gina gidanka.” Wane darassi ne wannan hurarren misali ya koyar? Ya kamata namiji ya yi shiri sosai kafin ya yi aure kuma ya soma nasa iyalin, ya fahimci cewa irin wannan wa’adi na kawo hakki.

A dā, an bayyana cewa wannan ayar tana nufin cewa miji kuma uba ba wai kawai zai kula da aikinsa ba ne ba amma kuma zai yi ƙoƙari ya ƙarfafa iyalinsa, alal misali ta wajen koya musu game da Allah da kuma Littafi Mai Tsarki. Ko da yake hakan gaskiya ne kuma yana bisa Nassi, kamar dai ba ainihi abin da wannan ayar take nufi ba ke nan. Me ya sa? Ka yi la’akari da dalilai biyu.

Na farko, ayar ba ta maganar ginawa ta wajen ƙarfafa iyalin da aka riga aka kafa ba. Maimakon haka, yana nufin gina gida na zahiri ne. Kalmar da aka fassara “gina” tana iya kasancewa da ma’ana ta alama, kafa iyali, wato, yin aure da kuma haifan yara.

Na biyu, ayar ta nanata yin abubuwa bisa tsari, kamar tana cewa “Da farko ka yi wannan; sai ka yi wancan.” Saboda haka, ayar tana nufin cewa ya kamata ne mu cika hakkinmu na zahiri kafin na ruhaniya? A’a!

A lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, idan namiji yana son ya ‘gina gidansa,’ ko kuma ya kafa iyali ta wajen yin aure, yana bukatan ya tambayi kansa, ‘Ina shirye na kula da kuma tallafa wa mata da kuma yaran da za mu haifa a nan gaba?’ Kafin ya samu iyali, yana da aikin da zai yi, wato, kula da filaye ko hatsinsa. Saboda haka, Littafi Mai Tsarki ya fassara wannan ayar kai tsaye cewa: “Kada ka gina gidanka ka kafa shi, sai ka gyara gonakinka, ka tabbata za ka sami abin zaman gari.” Za a iya amfani da wannan ƙa’idar a yau kuwa?

Ƙwarai kuwa. Namijin da yake son ya yi aure yana bukatan ya yi shiri sosai don wannan hakkin. Idan yana da koshin lafiya, dole ne ya yi aiki. Hakika, aiki tuƙuru da namiji zai yi don ya kula da iyalinsa bai kamata ya zama tanadin batutuwa na zahiri kawai ba. Kalmar Allah ta nuna cewa mutumin da ba ya kula da bukatun iyalinsa na zahiri, na sosuwar zuciya, da na ruhaniya, gwamma marar bangaskiya da shi! (1 Tim. 5:8) Saboda haka, sa’ad da yake shirin aure da rayuwar iyali, ya kamata saurayi ya yi wa kansa irin waɗannan tambayoyin: ‘A shirye na ke na yi tanadin abubuwan jiki ga iyalina? Ina shirye na ja-goranci iyali a batutuwa na ruhaniya? Zan cika hakkin gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai da matata da yarana?’ Kalmar Allah ta nanata waɗannan hakkoki masu muhimmanci.—K. Sha 6:6-8; Afis. 6:4.

Saboda haka, saurayin da yake son ya yi aure ya kamata ya yi tunani sosai a kan ƙa’idar da ke Misalai 24:27. Hakazalika, ya kamata budurwa ta tambayi kanta ko tana shirye ta ɗauki hakkokin zama uwargida da uwa. Ya kamata ma’aurata da ba su daɗe da yin aure ba su yi wa kansu irin waɗannan tambayoyi sa’ad da suke tunanin renon yara. (Luk 14:28) Bin irin wannan hurarriyar ja-gora zai taimaka wa mutanen Allah su guji matsaloli da yawa kuma su more rayuwar iyali mai gamsuwa.

[Bayanin da ke shafi na 12]

Waɗanne tambayoyi game da aure ne ya kamata saurayi ya yi wa kansa?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba