Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 8/15 pp. 30-32
  • Ka Taɓa Yin Hidima? Za Ka Iya Yi Kuma?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Taɓa Yin Hidima? Za Ka Iya Yi Kuma?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Kana Iya Sake Biɗar Yin Hidima
  • Jimre Yadda Kake Ji
  • Koyan Darassi Daga Abubuwa Masu Wuya da Aka Fuskanta
  • “Ya Roƙi Ubangiji Allahnsa”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • “Sa Zuciya ga Yahweh”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Darussa Daga Littafin Ayuba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ku Kasance da Kwanciyar Rai Idan Yanayinku Ya Canja
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 8/15 pp. 30-32

Ka Taɓa Yin Hidima? Za Ka Iya Yi Kuma?

KANA da gatan yin hidima a cikin ikilisiyar Kirista a dā? Wataƙila kai bawa ne mai hidima ko kuma dattijo. Mai yiwuwa a dā kana yin hidima na cikakken lokaci. Babu shakka, ka yi farin ciki kuma ka samu gamsuwa sosai a hidimarka, amma ka daina don wasu dalilai.

Wataƙila ka daina hidima don ka kula da waɗanda suke cikin iyalinka. A wata sassa, wataƙila ka yi hakan ne domin ka tsufa ko kuma kana rashin lafiya. Tsai da irin waɗannan shawarwarin ba alamar kasawa ba ce. (1 Tim. 5:8) A ƙarni na farko, Filibus ya yi hidima a matsayin mai yin wa’azi a ƙasar waje, amma daga baya ya tare a Kaisariya, inda ya kula da iyalinsa. (A. M. 21:8, 9) Sa’ad da ya tsufa, Sarki Dauda na Isra’ila ta dā ya yi shiri domin ɗansa Sulemanu ya ɗauki ragamar mulki. (1 Sar. 1:1, 32-35) Duk da haka, Jehobah ya ƙaunaci Filibus da Dauda kuma ya ɗauke su da tamani sosai, kuma har yanzu mutane suna daraja su.

Wataƙila an amshe gatan da kake da shi na yin hidima. Mai yiwuwa an yi hakan ne domin wani abu da ka yi da bai da kyau ko kuwa domin iyalinka tana da matsala. (1 Tim. 3:2, 4, 10, 12) Wataƙila ba ka amince da matakin da aka ɗauka ba, kuma har yanzu abin na ba ka haushi.

Kana Iya Sake Biɗar Yin Hidima

Idan mutum ya rasa gatan yin hidima hakan na nufin cewa ba zai iya sake yin hidima ba ne? Hakan ba ya faruwa a yawancin lokaci. Amma, domin ka soma yin hidima, dole ne ka biɗe ta. (1 Tim. 3:1) Amma me ya sa ya kamata ka yi hakan? Don dalilin da ya sa ka keɓe kanka ga Allah, wato, domin kana ƙaunar Jehobah da waɗanda suke bauta masa. Idan kana son ka nuna wannan ƙaunar ta wajen yin hidima, hakan zai sa Jehobah ya yi amfani da ƙwarewar da kake da ita kafin ka rasa gatanka da kuma bayan hakan.

Ka tuna tabbacin da Jehobah ya ba al’ummar Isra’ila bayan da ya ɗauke gata na musamman da suke da shi na hidima. Kalmarsa ta ce: “Ni Ubangiji ba mai-sākewa ba ne; domin haka ba a hallaka ku ba, ya ku ’ya’yan Yaƙub.” (Mal. 3:6) Jehobah yana ƙaunar Isra’ilawa kuma yana son ya ƙara yin amfani da su. Hakazalika, Jehobah yana son ya sake yin amfani da kai a nan gaba. Menene za ka yi da yanayinka na yanzu? Yin hidima na tsarin Allah ya dangana ne a kan kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah ba iyawa ba. Saboda haka, yayin da ba ka da ƙarin hakki a cikin ikilisiya ka mai da hankali wajen ƙarfafa ruhaniyarka.

Don ka “ƙarfafa” bangaskiyarka, dole ne ka “biɗi Ubangiji da ikonsa.” (1 Kor. 16:13; Zab. 105:4) Hanya ɗaya da za ka iya yin hakan ita ce ta yin addu’a da dukan zuciyarka. Sa’ad da kake magana game da yanayinka da Jehobah, ka gaya masa yadda kake ji, kuma ka roƙe shi ruhunsa. Ta yin hakan, za ka kusaci Jehobah, kuma hakan zai ƙarfafa ka. (Zab. 62:8; Filib. 4:6, 13) Wata hanya kuma da za ka iya ƙarfafa ruhaniyarka ita ce ta wurin kyautata nazarinka na Kalmar Allah. Da yake ba ka da hakki da yawa a yanzu, za ka iya kyautata nazari na kanka da na iyali, wataƙila ta wurin dawo da tsarin da yake maka wuyar bi a dā.

Hakika, har ila kana wakiltar Jehobah a matsayin Mashaidinsa. (Isha. 43:10-12) Gata mafi kyau da kowannenmu zai samu shi ne zama “abokan aiki na Allah.” (1 Kor. 3:9) Daɗa ayyukanka a hidimar fage wata hanya ce mai kyau ta ƙarfafa dangantakarka da Jehobah da kuma abokanka a hidima.

Jimre Yadda Kake Ji

Rasa gatan yin hidima za ta iya sa ka ji kunya ko kuma nadama. Kana iya ba da hujjar ayyukanka. Amma, idan ’yan’uwa masu hakki suka saurari abin da ka faɗa kuma har ila suka ga cewa bai kamata ka riƙe gatan ba fa? Kana iya soma jin haushin ’yan’uwan, kuma hakan zai hana ka biɗar samun ci gaba ko kuma ka ƙi koyan darassi daga abin da ya faru da kai. Bari mu bincika yadda abin da ya faru da Ayuba, Manassa, da kuma Yusufu zai taimaki mutum ya jimre da rashin jin daɗi.

Ayuba ya wakilci wasu a gaban Jehobah, kuma dattijo ne da alƙali a zamanin dā cikin mutane masu iko. (Ayu. 1:5; 29:7-17, 21-25) A lokaci na musamman a rayuwarsa, Ayuba ya yi hasarar arzikinsa, yaransa, da kuma lafiyarsa. Saboda haka, ya rasa matsayinsa a gaban mutane. Ayuba ya ce: “Yanzu na bāyana suna yi mani ba’a.”—Ayu. 30:1.

Ayuba yana ganin ba shi da laifi kuma yana son ya kāre kansa a gaban Allah. (Ayu. 13:15) Duk da haka, Ayuba ya dogara da Jehobah, kuma hakan ya kawo sakamako mai kyau. Ya koyi cewa yana bukatan a yi masa gyara, musamman don yadda ya aikata ga gwajin da ya fuskanta. (Ayu. 40:6-8; 42:3, 6) Tawali’un da Ayuba ya nuna ya sa Allah ya albarkace shi sosai.—Ayu. 42:10-13.

Idan ka yi rashin gatan ka ne domin wani laifin da ka yi, kana iya mamaki ko Jehobah da ’yan’uwanka Kiristoci za su taɓa gafarta maka da gaske kuma su mance da laifin. Ka yi la’akari da Sarki Manassa na Yahuda. Ya “aika mugunta dayawa a gaban Ubangiji, domin ya cakune shi.” (2 Sar. 21:6) Duk da haka, Manassa ya mutu yana sarauta a matsayin mutum mai aminci. Yaya hakan ya faru?

Manassa ya amince da horon da aka yi masa. Domin ya ƙi bin gargaɗin da aka yi masa, Jehobah ya sa Assuriyawa suka faɗa masa da yaƙi, suka ɗaure shi da sarka kuma suka kai shi bauta a ƙasar Babila mai nisa. A can, Manassa “ya roƙi Ubangiji Allahnsa, ya ƙasƙantar da kansa da gaske kuma a gaban Allah na ubanninsa. Ya kuwa yi addu’a gareshi.” Domin ya tuba da dukan zuciyarsa, hakan ya sa ya daidaita ayyukansa, kuma aka gafarta wa Manassa.—2 Laba. 33:12, 13.

Ba a kowane lokaci ba ne ake mai da dukan gatan da aka rasa a take ba. Amma, da shigewar lokaci, za a ba ka wasu hakkoki taƙaitattu. Karɓan wannan da kuma yin iyakar ƙoƙarinka sau da yawa zai sa a ba ka ƙarin ayyuka. Wannan ba ya nufin cewa komi zai daidaita nan da nan ba. Da akwai abubuwan da za su sa ka sanyin gwiwa. Amma, son rai da kuma nacewa za su kawo amfani mai kyau.

Yi la’akari da misalin Yusufu, Ɗan Yakubu. Sa’ad da yake ɗan shekara 17, ’yan’uwansa sun sayar da Yusufu zuwa bauta. (Far. 37:2, 26-28) Bai taɓa zaton cewa ’ya’yan babansa za su yi masa haka ba. Amma, yana shirye ya jimre da wannan yanayin, kuma da taimakon Jehobah ya kasance shugaba “cikin gidan ubangijinsa.” (Far. 39:2) Daga baya aka jefa shi kurkuku. Amma ya kasance da aminci kuma Jehobah yana tare da shi, don hakan daga baya aka ba shi hakkin kula da al’amuran kurkuku.—Far. 39:21-23.

Yusufu bai sani ba cewa dukan waɗannan abubuwan da suka same shi suna da manufa ba. Shi dai ya ci gaba da yin abin da zai iya yi. Jehobah ya yi amfani da shi ya tsare iyalin da za ta kai ga Zuriyar da aka yi alkawarinta. (Far. 3:15; 45:5-8) Ko da yake babu wani a cikin mu da zai iya samun irin wannan matsayi na musamman kamar Yusufu, hurarren labarin ya nuna cewa Jehobah yana sa hannu a gatan da bayinsa suke samu. Ka sa hakan ya faru ta wajen yin koyi da Yusufu.

Koyan Darassi Daga Abubuwa Masu Wuya da Aka Fuskanta

Ayuba, Manassa, da Yusufu sun fuskanci abubuwa masu jawo baƙin ciki. Waɗannan maza guda uku sun amince da yanayin da Jehobah ya ƙyale, kuma kowannensu ya koyi darussa masu amfani. Menene za ka iya koya?

Ka nemi abubuwan da Jehobah yake ƙoƙarin ya koya maka. Sa’ad da yake fama da rashin bege, Ayuba ya nuna son kai kuma ya mance batutuwa masu muhimmanci sosai. Amma, da Jehobah ya gyara shi cikin ƙauna, ya daidaitu, kuma ya ce: “Na fa furta abin da ban gane ba.” (Ayu. 42:3) Idan kana baƙin ciki don ka rasa wasu gata, ‘kada ka aza kanka gaba da inda ya kamata; amma ka tuna yadda za ka aza da hankali.’ (Rom. 12:3) Wataƙila Jehobah yana ƙoƙarin ya yi maka gyara a hanyar da har ila ba ka fahimta ba.

Ka karɓi horo. Mai yiwuwa Manassa da farko ya ji cewa bai dace a yi masa horo mai tsanani kamar haka ba. Duk da haka, ya karɓe ta, ya tuba, kuma ya bar mummunar tafarkinsa. Ko yaya kake ji game da horon da aka yi maka, ‘Ka ƙasƙanta a gaban Ubangiji, shi kuwa za ya ɗaukaka ka.’—1 Bit. 5:6; Yaƙ. 4:10

Ka yi haƙuri kuma ka kasance da yardan rai. Abubuwan da suka faru da Yusufu, suna iya sa ya ci gaba da yin fushi kuma ya rama. Maimakon haka, ya koyi basira da kuma jin kai. (Far. 50:15-21) Idan wani ya ɓata maka rai, ka yi haƙuri. Ka bari Jehobah ya koyar da kai.

Kana da matsayi a dā a cikin ikilisiyar Kirista? Ka ba Jehobah zarafin ba ka gata a nan gaba. Ka ƙarfafa ruhaniyarka. Ka kame yadda kake ji da haƙuri da tawali’u. Ka karɓi kowane aiki da aka ba ka da yardan rai. Ka kasance da tabbaci cewa “babu wani abu mai-kyau da [Jehobah] za ya hana ma masu-tafiya sosai.”—Zab. 84:11.

[Bayanin da ke shafi na 30]

Ka ƙarfafa bangaskiyarka ta wurin yin addu’a da dukan zuciyarka

[Hotunan da ke shafi na 31]

Ƙara ayyuka na hidimar fage hanya ce mafi kyau ta ƙarfafa ruhaniyarka

[Hotunan da ke shafi na 32]

Ka ba Jehobah zarafin ba ka gata a nan gaba

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba