Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 8/15 pp. 28-29
  • Ka Guji Abubuwan Raba Hankali a Wannan “Ranar Albishir”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Guji Abubuwan Raba Hankali a Wannan “Ranar Albishir”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Damuwa Tana Iya Nauyaya Mu
  • Ka Guji Abubuwan da Ke Cinye Lokaci
  • Ka Yi Wa’azin Bishara Sosai
  • Kana Tuna Ka Ce Na Gode?
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
  • Kada Ka Manta da Abin da Ya Fi Muhimmanci a Rayuwarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Masu “Ɗauke Da Albishir Mai Daɗi”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ku Zama Magirba Masu Farin Ciki!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 8/15 pp. 28-29

Ka Guji Abubuwan Raba Hankali a Wannan “Ranar Albishir”

KUTARE huɗu sun yi tunani game da zaɓin da suke da shi. Babu wanda ya ba su sadaka a ƙofar birnin. Mutanen Suriya da suka kewaye Samariya sun hana abinci shiga ƙasar, don haka, ana matsananciyar yunwa a ƙasar. Babu amfanin shiga birnin domin farashin abinci ya yi yawa sosai. Sun riga sun ji labarin cewa wasu sun soma cin mutane.—2 Sar. 6:24-29.

Kutaren suka yi tunani ‘Me ya sa ba za mu je sansanin mutanen Suriya ba? Ba mu da wani rashi da za mu yi.’ Da dare ya yi, sai suka fita. Sa’ad da suka isa sansanin, ko’ina ya yi shuru. Babu masu gadi. An ɗaure dawakai da jakuna, amma babu sojoji. Kutaren huɗu suka duba cikin tanti. Babu kowa, amma da akwai abinci da abin sha barkatai. Suka ci suka sha. Kutaren suka ga zinariya, azurfa, tufafi, da kuma abubuwa masu amfani. Suka ɗauki waɗanda suke so suka ɓoye kuma suka sake komawa don su ƙara kwasan wasu. Sojojin sun riga sun gudu sun bar dukan sansanin. Ta hanyar mu’ujiza, Jehobah ya sa mutanen Suriya sun ji ƙarar rundunar sojoji. Domin suna tsammanin cewa an kawo musu hari ne, mutanen Suriya suka gudu. Suka bar komi don wanda yake so ya ɗauka!

Kutaren suna ɗaukan kaya masu amfani suna ɓoyewa. Amma, da suka yi tunanin mutanen Samariya da yunwa take kashewa, sai lamarinsu ya soma damunsu. Suka soma gaya wa juna: “Ba mu kyauta ba; yau ranar albishir ce.” Kutaren suka garzaya zuwa Samariya kuma suka gaya musu albishirin da suka gani.—2 Sar. 7:1-11.

Mu ma muna zaune ne a lokacin da za a kira “ranar albishir.” Da yake nuni ga fanni na musamman na “cikar zamani,” Yesu ya ce: “Za a kuma yi bisharan nan ta Mulkin Sama ko’ina a duniya domin shaida ga dukkan al’ummai. Sa’an nan kuma sai ƙarshen ya zo.” (Mat. 24:3, 14) Yaya ya kamata hakan ya shafe mu?

Damuwa Tana Iya Nauyaya Mu

Farin cikin da suke yi domin abubuwan da suka gano, ya sa kutaren suka ɗan mance da Samariya. Sun mai da hankali ga abin da za su iya samu. Hakan zai iya faruwa da mu kuwa? “Yunwa” tana cikin alamun da ke nuna cewa ƙarshen duniyar nan ta kusa. (Luk 21:7, 11) Yesu ya gargaɗi almajiransa: “Ku yi hankali da kanku, kada ya zama zukatanku su yi nauyi da zarin ci da maye da shagulgula na wannan rai.” (Luk 21:34) A matsayin mu na Kiristoci, muna bukatan mu mai da hankali kada mu ƙyale damuwa game da abubuwan rayuwa na yau da kullum su sa mu manta cewa muna zama a “ranar albishir.”

Wata Kirista mai suna Blessing ba ta ƙyale neman abin kanta ya nauyaya ta ba. Ta yi hidima na majagaba, ta gama makarantarta, kuma daga baya ta auri wani da ke hidima a Bethel, kuma ta zama ɗaya daga cikin iyalin Bethel na ƙasar Benin. Ta ce: “Ni mai adana ɗaki ce, kuma ina jin daɗin aikina sosai.” A yanzu, Blessing tana farin ciki cewa ta yi shekaru 12 tana hidima na cikakken lokaci kuma tana murna cewa ta mai da hankali ga “ranar albishir” da muke zaune a ciki yanzu.

Ka Guji Abubuwan da Ke Cinye Lokaci

Sa’ad da yake aika almajiransa saba’in, Yesu ya ce: “Girbi dayawa ya ke, amma ma’aikata kadan suke: ku yi addu’a fa ga Ubangijin girbi shi aiki ma’aikata cikin girbinsa.” (Luk 10:2) Kamar yadda yin jinkiri a lokacin girbi zai iya sa a yi hasarar abubuwan da aka shuka, yin sakaci a aikin wa’azi zai iya sa mu yi hasarar rayuka. Saboda haka, Yesu ya daɗa: “Kada ku gaida kowane mutum a kan hanya.” (Luk 10:4) Yare na asali na kalmar nan “gaida” ba ya nufin “sannu” ko “barka dai” kawai. Ta ƙunshi runguma da dogon taɗi da za a iya yi idan an sadu da aboki. Saboda haka, Yesu ya gargaɗi mabiyansa su guji abubuwa marar muhimmanci da za su raba hankalinsu kuma su yi amfani da lokacinsu da kyau. Saƙon da za su yi wa’azinsa na gaggawa ne.

Ka yi tunanin yawan lokacin da abubuwan raba hankali suke ɗauka. Shekaru da yawa yanzu, talabijin ne yake kan gaba a cikin abubuwan da ke cin lokaci a wurare da yawa. Tarho na selula da kuma kwamfutarmu fa? A wani binciken da aka yi na mutanen da suka girma a ƙasar Britaniya, an gano cewa “yawancin mazauna Britaniya na kashe mintoci 88 kowace rana a tarhon da ke gida, minti 62 a tarho na selula, minti 53 wajen aika saƙo ta kwamfuta da kuma minti 22 wajen aika saƙo ta wayar selula.” Adadin sau biyu ya ɗara yawan sa’o’in da majagaba na ɗan lokaci yake ba da wa a hidima kowace rana! Yaya kake amfani da waɗannan abubuwa?

Ernst da Hildegard Seliger sun mai da hankali ga yadda suke amfani da lokacinsu. Idan aka haɗa shekarun da su biyun suka yi a sansanin Nazi da kuma kurkuku na Kwaminis, hakan ya ɗara shekara arba’in. Bayan an sake su, sun yi hidima na majagaba har suka gama hidimarsu a duniya.

Mutane da yawa a yau suna so su yi kamar waɗannan ma’auratan. Ma’auratan suna iya yin amfani da yawancin lokacinsu su yi karatu kuma su rubuta wasiƙu. Amma, abubuwa na ruhaniya sun fi muhimmanci a rayuwarsu.

Hakika, dukanmu muna son mu samu wasiƙu daga waɗanda muke ƙauna ko kuma su kira mu da waya, kuma hakan ba laifi ba ne. Yin zaɓi masu kyau da suka bambanta a yau da kullum yana da amfani. Duk da haka, muna bukatan mu mai da hankali da abubuwan da ke cinye lokaci a wannan ranar wa’azin bishara.

Ka Yi Wa’azin Bishara Sosai

Albarka ce mu kasance a raye a “ranar albishir.” Kada mu ƙyale hankalinmu ya rabu kamar yadda kutaren nan huɗu suka yi da farko. Ka tuna cewa sun kammala: “Ba mu kyauta ba.” Hakazalika, ba shi da kyau mu ƙyale abubuwa na kai da muke biɗa ko kuma abubuwan da za su cinye lokacinmu su hana mu mu shagala a hidimar fage.

Muna da misali mai kyau da za mu bi a wannan batun. Da yake tunani game da shekara ashirin na farko da ya yi a hidimarsa, manzo Bulus ya rubuta: “Na yi wa’azin bisharar Kristi sarai.” (Rom. 15:19) Bulus bai ƙyale kome ya rage himmarsa ba. Bari mu kasance da himma kamarsa, yayin da muke sanar da saƙon Mulki a wannan “ranar albishir.”

[Hotunan da ke shafi na 28]

Blessing ba ta ƙyale abubuwa na kanta su hana ta hidima na cikakken lokaci ba

[Hotunan da ke shafi na 29]

Iyalin Seliger sun mai da hankali da yadda suka yi amfani da lokacinsu

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba