An Gano Dukiyoyin da Aka Ɓoye
KA TAƁA gano dukiyar da aka ɓoye a wurin da ba ka yi tsammanin za ka same ta ba? Hakan ya faru ga Ivo Laud, wani Mashaidin Jehobah a Estonia, a ranar 27 ga Maris, 2005. Yana taimaka wa Alma Vardja, wata Mashaidiya tsohuwa, ta rushe wata tsohuwar rumfa. Sa’ad da suke ciccire bangon daga waje, sun lura cewa an rufe wani gefen bangon da allo. Da suka cire allon sun ga rami mai faɗin inci 4 da tsawon inci 50 da kuma zurfin inci 4 da aka rufe da katako da ya yi daidai da shi. (1) Tarin dukiyoyi ne da aka ɓoye! Menene dukiyoyin? Wanene ya ɓoye su a wurin?
A cikin ramin, da akwai ƙunshi masu yawa da aka ɗaure sosai da takarda. (2) Ƙunshin na ɗauke da littattafan Shaidun Jehobah, yawancinsu talifofin nazari na Hasumiyar Tsaro ne, har da wasu na shekara ta 1947. (3) An rubuta su da yaren Estonia. Wasu littattafai da ke cikin ƙunshin suna ɗauke da bayanan da suka nuna wanda ya ɓoye kayan a wajen. Rubuce-rubucen tuhumar da aka yi wa Villem Vardja ne, mijin Alma. Bayanan da suka ƙunshi shekarun da ya yi a kurkuku suna cikin abubuwan da aka gano. Me ya sa aka jefa shi kurkuku?
Villem Vardja yana da hakki sosai a cikin Shaidun da ke Ikilisiyar Tartu da kuma Ikilisiyar Otepää a Estonia da ke cikin ƙasashen da ke ƙarƙashin Rasha a dā. Kamar dai ya koyi gaskiyar Littafi Mai Tsarki kafin Yaƙin Duniya na biyu. Bayan wasu shekaru, a ranar 24 ga Disamba, a shekara ta 1948, gwamnatin Kwaminis ta kama Ɗan’uwa Vardja don ayyukansa na addini. ’Yan sandan ciki sun tuhume shi kuma sun wulaƙanta shi yayin da suke ƙoƙarin su tilasta masa ya ba su sunayen ’yan’uwansa masu bi. Bayan sun ƙi ba shi zarafin kāre kansa a kotu, an yanke masa hukuncin ɗaurin shekara goma a sansanin kurkuku da ke Rasha.
Villem Vardja ya kasance da aminci ga Jehobah har mutuwarsa a ranar 6 ga Maris, a shekara ta 1990. Matarsa ba ta sani ba cewa littattafan suna wajen. Kamar dai yana son ya kāre ta idan aka tuhume ta, shi ya sa bai gaya mata cewa ya ɓoye littattafan a wurin ba. Me ya sa ya ɓoye littattafan? Ya ɓoye su domin Kwamitin ’Yan Sandan Ciki na Ƙasar Rasha, (KGB), sau da yawa suna zuwa bincike a gidajen Shaidun Jehobah ba zato ba tsammani, suna neman littattafai na addini. Mai yiwuwa Ɗan’uwa Vardja ya ɓoye littattafan ne don ya tabbata cewa ’yan’uwansa suna da abinci na ruhaniya idan ’yan sanda suka kwashe kome. An gano tarin littattafan da farko a cikin rani ta shekara ta 1990. An gano ɗaya a Tartu, kudancin Estonia. Villem Vardja ne ya ɓoye su.
Me ya sa muka kira waɗannan littattafan dukiyoyi? Domin waɗannan littattafai da aka mai da hankali sosai kuma aka rubuta su da hannu da aka ɓoye, ya nuna cewa Shaidun suna ɗaukan abinci na ruhaniya da suke da shi a lokacin da tamani. (Mat. 24:45) Kana godiya don abinci na ruhaniya da kake samu yanzu a yankinku? Hasumiyar Tsaro da aka rubuta a yaren Estonia da wasu harsuna fiye da 170 yana cikinsu.