Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 6/15 pp. 28-31
  • Ba Da Aiki Me Ya Sa Yake da Muhimmanci Kuma Yaya Za a Yi Hakan?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ba Da Aiki Me Ya Sa Yake da Muhimmanci Kuma Yaya Za a Yi Hakan?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Menene Ba da Aiki Yake Nufi?
  • Me Ya Sa Za a Ba da Aiki?
  • Abin da Ya Sa Wasu Suke Jinkiri
  • Yadda Za a Ba da Aiki
  • Ku Koyar da Wasu Kuma Ku Ba Su Aiki
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2020
  • Ka Bauta wa Allah Cikin Saukin Kai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Dattawa—Ku Koyar da Wasu Su Ɗauki Hakki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • “Ka Danka ma Mutane Masu-Aminci”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 6/15 pp. 28-31

Ba Da Aiki Me Ya Sa Yake da Muhimmanci Kuma Yaya Za a Yi Hakan?

AKWAI wanda yake ba da aiki da daɗewa kafin a halicci Duniya. Jehobah ya halicci Ɗansa makaɗaici kuma ya yi amfani da Ɗansa a matsayin “gwanin mai-aiki” ya halicci sararin samaniya. (Mis. 8:22, 23, 30; Yoh. 1:3) Sa’ad da Allah ya halicci ma’aurata na farko, ya gaya musu su “mamaye duniya, [su] mallake ta.” (Far. 1:28) Mahaliccin ya ba ’yan adam aikin faɗaɗa Aljanna na Adnin zuwa dukan duniya. Hakika, tun farko, ƙungiyar Jehobah tana ba da aiki.

Menene ba da aiki ya ƙunsa? Me ya sa ya kamata dattawa Kirista su koyi ba da wasu ayyukan ikilisiya ga wasu, kuma yaya za su yi hakan?

Menene Ba da Aiki Yake Nufi?

“Ba da aiki” yana nufin a ba mutum wani abu, naɗa mutum ya zama wakili, ko kuma ba da hakki ko iko. Saboda haka, ba da aiki ya ƙunshi cim ma buri tare da taimakon wasu. Hakan na sa wasu mutane su sami iko.

Ana bukatar waɗanda aka ba aiki a cikin ikilisiyar Kirista su cika aikinsu, su ba da rahoton yadda aikin ke ci gaba, kuma su tuntuɓi wanda ya ba su aikin. Amma ɗan’uwan da ya ba da aikin ne ke da hakkin ganin cewa an yi aikin. Yana bukatar ya tabbata cewa ana yin aikin kuma ya ba da shawara idan bukata ta kama. Duk da haka, wasu suna iya tambaya, ‘Me ya sa za ka ba da aiki idan za ka iya yi da kanka?’

Me Ya Sa Za a Ba da Aiki?

Ka yi tunani yadda Jehobah ya halicci Ɗansa makaɗaici kuma ya ba shi aikin sa hannu wajen halittar sauran abubuwa. Hakika “a cikinsa aka halitta dukan abu, cikin sammai da bisa duniya kuma, abubuwa masu-ganuwa da abubuwa marasa-ganuwa.” (Kol. 1:16) Mahaliccin yana iya yin komi da kansa, duk da haka, yana son Ɗansa ma ya samu farin cikin cim ma aiki mai kyau. (Mis. 8:31) Wannan ya taimaki Ɗan ya ƙara koya game da halayen Allah. A wani azanci, Uban ya yi amfani da wannan zarafin ya koyar da Ɗansa makaɗaici.

Sa’ad da yake duniya, Yesu Kristi ya yi koyi da Ubansa wajen ba da aiki. A hankali ya koyar da almajiransa. Ya aika manzanni goma sha biyu kuma daga baya ya aika almajirai saba’in don su yi ja-gora a aikin wa’azi. (Luk 9:1-6; 10:1-7) Sa’ad da Yesu ya kai wuraren nan, an riga an kafa tushe mai kyau a wuraren da zai yi wa’azi. Sa’ad da yake son ya bar duniya, Yesu ya ba almajiransa da ya koyar hakkin da ya fi muhimmanci, har da aikin wa’azi a dukan duniya.—Mat. 24:45-47; A. M. 1:8.

Ba da aiki da kuma koyarwa sun zama abin da ake yi a ikilisiyar Kirista. Manzo Bulus ya gaya wa Timothawus: “Sai ka danƙa wa amintattun mutane, waɗanda su ma za su koya wa waɗansu.” (2 Tim. 2:2) Hakika, waɗanda suka manyanta za su koyar da waɗanda har ila za su koyar da waɗansu.

Ta wajen ba da wasu ayyukan da aka ba shi, dattijo yana iya sa wasu su sami farin cikin koyarwa da kuwa ziyarar kiwo. Fahimtar cewa iyawa ta ’yan adam tana da iyaka, dattawa suna da ƙarin dalili na gaya wa mutane su taimaka a ayyuka na ikilisiya. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wurin masu-tawali’u akwai hikima.” (Mis. 11:2) Tawali’u ya ƙunshi mutum ya san kasawarsa. Idan kana ƙoƙarin ka yi komi da kanka, za ka gaji ainun kuma ba za ka sami lokacin tattaunawa da iyalinka ba. Saboda haka, yana da kyau ka ba da wasu ayyuka. Alal misali, ɗan’uwan da ke tsara ayyukan rukunin dattawa, yana iya gaya wa wasu dattawa su yi lissafin kuɗin da aka kashe a ikilisiya. Ta wajen yin hakan, waɗannan dattawan za su san yadda ake amfani da kuɗin ikilisiyar.

Yayin da ba da aiki yana ba wasu zarafin samun iyawa da ilimi, zai kuma sa wanda yake ba da aikin ya lura da iyawar waɗanda ya ba aikin. Saboda haka, ta wajen ba da ayyukan da suka dace a ikilisiya, dattawa suna iya “gwada” waɗanda suke burin zama bayi masu hidima.—1 Tim. 3:10.

A ƙarshe, ta wajen ba da aiki, dattawa suna nuna sun amince da wasu. Bulus ya koyar da Timothawus ta wajen yin wa’azi tare da shi a ƙasashen waje. Waɗannan maza biyu sun ƙulla dangantaka na kud da kud. Bulus ya kira Timothawus “ɗana na gaske cikin bangaskiya.” (1 Tim. 1:2) Hakanan ma, Jehobah da Yesu sun ƙulla gami mai ƙarfi sa’ad da suke aiki tare wajen halittar dukan sauran abubuwa. Ta wajen ba wasu aiki, dattawa suna iya ƙulla dangantaka na kud da kud da su.

Abin da Ya Sa Wasu Suke Jinkiri

Ko da sun san amfanin, yana yi wa wasu dattawa wuya su ba da aiki, wataƙila suna yin haka domin suna jin cewa ikonsu zai ragu. Suna iya tunanin cewa dole ne su zama masu yin ja-gora a koyaushe. Duk da haka, ka tuna cewa kafin ya hau sama, Yesu ya ba almajiransa iko su ɗauki hakki mai girma, domin ya san za su yi ayyuka da suka fi nasa!—Mat. 28:19, 20; Yoh. 14:12.

Mai yiwuwa wasu dattawa sun ba da aiki a dā amma ba su ga sakamako mai kyau ba. Suna iya jin cewa idan suka yi aikin da kansu, aikin zai fi kyau kuma zai yi sauri. Duk da haka, ka yi la’akari da misalin Bulus. Ya san amfanin sa wasu su yi aiki, amma ya kuma san cewa waɗanda ya ba aikin ba a koyaushe ba ne za su yi aikin yadda yake so ba. A tafiyar hidimarsa ta farko, Bulus ya koyar da abokin tafiyarsa Markus. Bulus ya yi baƙin ciki sa’ad da Markus ya bar hidimarsa ya koma gida. (A. M. 13:13; 15:37, 38) Har ila, hakan bai hana Bulus koyar da wasu ba. Kamar yadda aka ambata ɗazu, ya gayyaci matashi Timothawus ya zama abokin tafiyarsa. Sa’ad da Timothawus ya kasance a shirye ya ɗauki hakki mai girma, Bulus ya bar shi a Afisa, ya ɗanka masa ikon naɗa masu kula da bayi masu hidima a ikilisiya.—1 Tim. 1:3; 3:1-10, 12, 13; 5:22.

Hakanan ma, bai kamata dattawa na zamani su fid da rai wajen koyar da ’yan’uwa domin ɗaya daga cikinsu bai yi aikin da kyau ba. Yana da kyau da kuma muhimmanci a amince da wasu kuma a koyar da su. Amma, waɗanne abubuwa ne ya kamata dattawa su tuna sa’ad da suke ba wasu aiki?

Yadda Za a Ba da Aiki

Sa’ad da kake ba da aiki, ka yi la’akari da iyawar ’yan’uwa da kake son ka yi amfani da su. Sa’ad da bukata na raba abinci ya taso a Urushalima, manzannin sun zaɓi ‘maza bakwai waɗanda ake shaidarsu, cike da Ruhu Mai-tsarki da hikima.’ (A. M. 6:3) Idan ka gaya wa wanda ba a tabbata da shi ya yi wani aiki, wataƙila ba zai yi aikin ba. Saboda haka, ka ba shi ƙananan ayyuka tukuna. Idan mutum ya nuna shi amintacce ne, kana iya ba shi ƙarin hakki.

Amma, da ƙarin abubuwa da ake bukata. Halaye da iyawa sun bambanta. Mutane suna da ƙwarewa dabam-dabam. Ɗan’uwa mai fara’a yana iya yin aikin atenda da kyau, kuma wanda ya iya tsara abubuwa da kyau zai iya zama mataimakin sakatare na ikilisiya. Ana iya ba ’yar’uwa da take da iyawa na fasaha aikin shirya furanni a lokacin Tuna Mutuwar Yesu.

Sa’ad da ake ba da aikin, a gaya wa mutumin sarai abin da ake son ya yi. Kafin Yohanna Mai Baftisma ya aika da manzanninsa zuwa wurin Yesu, ya gaya musu abin da yake son ya sani, da irin tambayar da za su yi. (Luk 7:18-20) A wani ɓangare kuma, sa’ad da Yesu ya gaya wa almajiransa su tattara abincin mu’ujiza da ya rage, bai gaya musu dalilin ba. (Yoh. 6:12, 13) Hakan ya dangana da irin aikin da kuma iyawar mataimakin. Ya kamata wanda ya ba da aikin da wanda aka ce ya yi aikin su fahimci abin da ake son a cim ma kuma a riƙa gaya wa wanda ya ba da aikin yadda ake samun ci gaba a aikin. Ya kamata dukansu su san abin da wanda yake aikin zai iya yi da kansa da kuma wanda zai je ya tuntuɓi wanda ya ba shi aikin. Idan akwai ranan da ya kamata a gama aikin, zai fi kyau a tattauna batun kuma a yarda da hakan maimako a tilasta wa mutumin da yake aikin ya yi hakan.

Ya kamata a ba wanda aka ce ya yi aikin kuɗi, kayan aiki, da taimako yadda bukata ta kama. Yana iya kasance da taimako idan aka gaya wa sauran mutane shirin da ake yi. Sa’ad da Yesu ya ba Bitrus “muƙublai na mulkin sama,” ya yi hakan a gaban sauran almajirai. (Mat. 16:13-19) Hakanan ma, wani lokaci yana da kyau a sanar wa ikilisiya wanda yake da hakkin yin wani aiki.

Duk da haka ana bukatar a mai da hankali. Idan har ila kana ƙoƙarin ka yi aikin da ka sa wani ya yi, kana nuna masa cewa ba ka tabbata da shi ba. Hakika, wani lokaci ba za a yi aikin yadda kake so ba. Duk da haka, idan aka ba ɗan’uwa da aka ce ya yi aikin ɗan ’yanci daga baya zai kasance da tabbaci kuma zai san yadda ake aikin. Hakan ba ya nufin cewa ba za a damu da yadda mutumin yake aikin ba. Ko da Jehobah ya ba Ɗansa aiki a lokacin halitta, har ila shi ma ya yi aikin. Ya gaya wa Gwanin Mai Aiki: ‘Bari mu yi mutum a cikin surarmu.’ (Far. 1:26) Saboda haka, ta wurin kalmominka da ayyukanka, ka tallafa wa aikin da ake yi, kuma ka yaba wa mutumin don ƙoƙarce-ƙoƙarcensa. Ɗan maimaita sakamakon aikin tare da mutumin yana iya taimakonsa. Idan bai yi aikin da kyau ba, kada ka yi jinkirin ba da ƙarin shawara ko kuma taimako. Ka tuna cewa, kai da ka ba da aikin ne ke da hakki na ƙarshe.—Luk 12:48.

Mutane da yawa sun amfana daga ayyukan ikilisiya waɗanda dattawa da suka nuna suna ƙaunarsu sosai suka ce su yi. Hakika, dukan dattawa suna bukatar su koyi abin da ya sa za su ba da aiki da kuma yadda za su yi hakan, ta haka suna yin koyi da Jehobah.

[Akwati da ke shafi na 29]

BA DA AIKI

• hanya ce ta sa wasu su more farin cikin cim ma abu

• hanya ce ta ƙara cim ma abubuwa

• hanya ce ta nuna hikima da tawali’u

• hanya ce ta koyar da wasu

• hanya ce ta nuna cewa mun amince da wasu

[Akwati da ke shafi na 30]

YADDA ZA A BA DA AIKI

• A zaɓi mutane da suka dace don aikin

• A bayyana yadda za a yi aikin dalla-dalla/kuma wanda ya ba da aikin da mai aikin za su riƙa sadawa

• A bayyana abin da ya kamata a cim ma

• A yi tanadin kayan aiki da ake bukata

• Ka mai da hankali ga aikin, kuma ka furta ka tabbata da mutumin

• Ka kasance a shirye ka ɗauki hakki na ƙarshe

[Hotunan da ke shafi na 31]

Ba da aiki ya ƙunshi lura da yadda aikin ke ci gaba

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba