Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 4/15 pp. 15-19
  • Hikimar Jehobah Ta Bayyana A Halittarsa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Hikimar Jehobah Ta Bayyana A Halittarsa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Yesu, “Gwanin Mai-Aiki”
  • Darassi na Yin Aiki Tuƙuru
  • Kāre Dangantakarmu da Allah
  • Dagewa Duk da Hamayya
  • ‘Ka Lizimci [Manne wa] Abin da Ke Nagari’
  • Darussa Daga Halitta
  • “Ina Misalin Zurfin . . . Hikimar Allah!”
    Ka Kusaci Jehobah
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 4/15 pp. 15-19

Hikimar Jehobah Ta Bayyana A Halittarsa

“Al’amura nasa da ba su ganuwa . . . ta wurin abubuwa da an halitta ana gane su.”—ROM. 1:20.

1. Ta yaya hikimar duniya ta shafi mutane da yawa a yau?

DUNIYA gabaki ɗaya tana ɗaukan mutanen da suke da ilimi sosai a matsayin masu hikima. Amma, gaskiya ne cewa suna da hikima? A’a, domin waɗannan da ake ganin suna da hikima sun kasa taimaka wa mutane kuma ba za su iya ba da shawara mai kyau ba ta sanin ainihin ma’anar rayuwa. Akasin haka, waɗanda suka ƙyale mutanen nan su rinjaye su sun zama “waɗanda ana wofadda su suna shillo ga kowace iskan sanarwa.”—Afis. 4:14.

2, 3. (a) Menene ya sa Jehobah shi ne “kaɗai mai-hikima”? (b) Yaya hikimar Allah ta bambanta da ta duniya?

2 Hakan ya bambanta da waɗanda suke da hikima ta gaske, wadda Jehobah Allah ne Tushen ta! Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Jehobah ne “kaɗai mai-hikima.” (Rom. 16:27) Ya san komi game da sararin samaniya, har da yanayinta da yadda aka halicce ta. Ƙa’idodin halitta da muke gani, waɗanda ke taimaka wa mutane a binciken da suke yi, duk halittun Jehobah ne. Saboda haka, abubuwan da ’yan adam suka ƙirƙiro ba sa burge shi, kuma ussan ilimi da ake ganin mutane suna da shi ba ta ba shi mamaki. “Hikimar wannan duniya wauta ce ga Allah.”—1 Kor. 3:19.

3 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Jehobah “yana bada hikima” ga bayinsa. (Mis. 2:6) Ba kamar ilimin falsafa ta ’yan adam ba, hikimar da ake samu daga Allah cikakkiya ce. Ta ƙunshi sanin ya kamata da ke bisa cikakken sani da fahimi. (Karanta Yaƙub 3:17.) Manzo Bulus ya yi mamaki game da hikimar Jehobah. Ya rubuta: “Ya zurfin wadata na hikimar Allah duk da na saninsa! ina misalin wuyan binciken shari’unsa, al’amuransa kuma sun fi gaban a bi sawu!” (Rom. 11:33) Domin Jehobah shi ne mafi hikima, muna da tabbaci cewa dokokinsa suna yi mana ja-gora ne don mu yi rayuwa mafi kyau. Ballantana ma, fiye da kowa, Jehobah ya san abin da muke bukata da zai sa mu farin ciki.—Mis. 3:5, 6.

Yesu, “Gwanin Mai-Aiki”

4. A wace hanya ce za mu iya ganin hikimar Jehobah?

4 Za mu iya ganin hikimar Jehobah, tare da sauran fitattun halayensa a abubuwan da ya halitta. (Karanta Romawa 1:20.) Daga babba zuwa ƙarami, ayyukan Jehobah sun nuna halayensa dabam dabam. Duk wurin da muka duba, daga sama har zuwa ƙasar da muke takawa, muna ganin abubuwa masu yawa da suka nuna cewa da akwai Mahalicci mafi hikima kuma mai ƙauna. Za mu iya koyan abubuwa da yawa game da shi ta wajen tattauna abubuwan da ya halitta.—Zab. 19:1; Isha. 40:26.

5, 6. (a) Ban da Jehobah, wanene kuma ya saka hannu a halitta? (b) Menene za mu tattauna, kuma me ya sa?

5 Jehobah yana tare da wani sa’ad da “ya halitta sama da ƙasa.” (Far. 1:1) Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa tun da daɗewa kafin ya halicci abubuwan da muke gani, ya halicci wani ruhu wanda ya yi amfani da shi wajen ‘halittan dukan abu.’ Wannan ruhun shi ne Ɗa makaɗaici na Allah, wato, “ɗan fari . . . gaban dukan halitta,” wanda daga baya ya yi rayuwa a duniyar nan a matsayin Yesu. (Kol. 1:15-17) Kamar Jehobah, Yesu ma yana da hikima. A littafin Misalai sura 8, an kwatanta shi da hikima. Wannan surar kuma ta kira Yesu “gwanin mai-aiki” na Allah.—Mis. 8:12, 22-31.

6 Da haka, halittun da muke gani sun nuna hikimar Jehobah da na Gwanin Mai aikinsa, Yesu. Tana ɗauke da darussa masu kyau dominmu. Bari mu tattauna misalai huɗu na abubuwan da aka halitta da “azanci dayawa” a Misalai 30:24-28.a

Darassi na Yin Aiki Tuƙuru

7, 8. Waɗanne abubuwa ne game da tururuwa suke burge ka?

7 Sa’ad da muka bincika yadda aka tsara su da kuma ayyukansu, har abubuwa da za a iya kira “ƙanƙanana a duniya” suna koya mana darassi. Alal misali, ka yi la’akari da irin hikimar da tururuwa take da shi.—Karanta Misalai 30:24, 25.

8 Wasu masu bincike sun gaskata cewa tururuwa sun fi ’yan adam yawa sau dubu ɗari biyu, kuma dukansu suna aiki tuƙuru a duniya. Tururuwa sun kasu gidaje dabam dabam, kuma a yawancin gidajen za a iya samun tururuwa kala uku: sarauniya, maza, da kuma ma’aikata. Kowane rukuni yana nasa aikin don ya kula da bukatun gidan. Wata irin tururuwa da ke Amirka ta Kudu ta ƙware wajen aikin lambu. Wannan ’yar ƙaramar ƙwaron tana sa taki, tana yin dashe, kuma tana yi wa shuke-shuke aski don su yi girma sosai. Masu bincike sun gano cewa wannan gwani a “aikin lambu” tana yin ayyukanta ne daidai da yawan abinci da ake bukata a gidajen tururuwa.b

9, 10. Ta yaya za mu zama masu yin aiki tuƙuru kamar tururuwa?

9 Muna iya koyan wani abu daga tururuwa. Sun koya mana cewa muna bukatar mu ƙoƙarta sosai idan muna son mu samu sakamako mai kyau. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana: “Tafi wurin tururuwa, kai rago: Lura da al’amuranta, ka ɗauki hikima: Ita wadda ba ta da alƙali, ko shugaba, ko mahukumci, duk da haka tana tanajin cimakatta cikin damana, ta kan tattara abincinta da kaka.” (Mis. 6:6-8) Jehobah da Gwanin Mai aikinsa Yesu, suna aiki tuƙuru. Yesu ya ce: “Ubana yana aiki har yanzu, ni ma ina aiki.”—Yoh. 5:17.

10 A matsayin masu yin koyi da Allah da Kristi, ya kamata mu ma mu zama masu aiki tuƙuru. Ko wane irin aiki ne muke yi a ƙungiyar Allah, ya kamata dukanmu mu “yawaita cikin aikin Ubangiji.” (1 Kor. 15:58) Saboda haka, ya kamata mu bi umurnin da Bulus ya ba Kiristoci a Roma: “Cikin ƙwazo kada ku yi ragonci; kuna huruwa a cikin ruhu; kuna bauta ma Ubangiji.” (Rom. 12:11) Ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu wajen yin nufin Jehobah ba na banza ba ne, domin Littafi Mai Tsarki ya tabbatar da mu cewa: “Allah ba marar-adalci ba ne da za shi manta da aikinku da ƙauna wadda kuka nuna ga sunansa.”—Ibran. 6:10.

Kāre Dangantakarmu da Allah

11. Ka kwatanta wasu halayen rema.

11 Rema, wata dabba ce ƙarama da za ta iya koya mana darussa masu muhimmanci. (Karanta Misalai 30:26.) Ta yi kama da zomo babba, amma kunnuwanta ƙanana ne kewayayyu kuma tana da gajerun ƙafafu. Wannan ’yar ƙaramar dabbar tana zama ne cikin duwatsu. Iya hangen nesa da take yi yana kāre ta, kuma ramuka masu zurfi da take zama suna kāre ta daga dabbobin da za su iya kashe ta. An halicci rema ce ta zauna a wurin da za su iya tallafa wa juna don ta sami kāriya da kuma ɗumi a lokacin sanyi.c

12, 13. Waɗanne darussa ne za mu iya koya daga rema?

12 Menene za mu iya koya daga rema? Na farko, ka lura cewa wannan dabba ba ta kai kanta inda za a iya kai mata hari. Maimakon haka, tana yin amfani da idonta da ke ganin nesa don ta ga manyan dabbobi tun suna da nesa, kuma tana zama kusa da ramuka da za su zama mafaka don ceton rai. Hakazalika, muna bukatar mu kasance a faɗake a ruhaniya don mu fahimci haɗarurrukan da ke ɓoye cikin duniyar Shaiɗan. Manzo Bitrus ya faɗakar da Kiristoci: “Ku yi hankali shimfiɗe, ku yi zaman tsaro: magabcinku Shaiɗan, kamar zaki mai-ruri, yana yawo, yana neman wanda za ya cinye.” (1 Bit. 5:8) Sa’ad da yake duniya, Yesu ya kasance a faɗake, yana tsare kansa daga dukan ƙoƙarce-ƙoƙarcen da Shaiɗan yake don ya karya amincinsa. (Mat. 4:1-11) Yesu ya kafa misali mai kyau ga mabiyansa!

13 Hanya ɗaya da za mu iya kasancewa a faɗake ita ce ta yin amfani da kāriya na ruhaniya da Jehobah ya yi mana tanadinsa. Kada mu yi watsi da yin nazarin Kalmar Allah da kuma halartan taro na Kirista. (Luk 4:4; Ibran. 10:24, 25) Ƙari ga haka, kamar yadda rema take yin nasara ta wajen zama da sauran don su tallafa wa juna, muna bukatar mu kusaci ’yan’uwanmu Kiristoci don mu more “ƙarfafawa” da su. (Rom. 1:12) Ta wurin yin abin da ya kamata mu yi don mu sami kāriyar Jehobah, muna nuna cewa mun yarda da mai zabura Dauda, wanda ya rubuta: “Ubangiji pana ne, da kagarata, mai-cetona kuma; Allahna, pana mai-ƙarfi, a cikinsa zan dogara.”—Zab. 18:2.

Dagewa Duk da Hamayya

14. Ko da yake fara guda ba ta ba da tsoro, me za a iya cewa game da cincirindon fari?

14 Za mu iya koyan wani abu daga fara. Fara guda mai tsawon inci biyu ba ta ba da tsoro, amma idan suka yi cincirindo, hakan na ba da tsoro. (Karanta Misalai 30:27.) Da yake an san su da iya ci, fari masu yawa marasa gajiya, suna iya halaka gona da ta isa girbi. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta ƙarar ƙwari, har da fari da karusan yaƙi da kuma ƙarar harshen wuta wadda ke cinye ciyawa. (Joe. 2:3, 5) Mutane suna cinna wuta don su hana fari damunsu, amma a yawancin lokaci hakan ba ya taimakawa. Me ya sa? Domin farin da suka mutu suna kashe wutan, bayan haka sauran farin su ci gaba da tafiyarsu. Duk da cewa ba su da sarki ko shugaba, fari suna aiki ne kamar ƙwararrun sojoji, kuma suna shan kan duk wani ƙalubalen da suka fuskanta.d—Joe. 2:25.

15, 16. Yaya masu shelar Mulki na zamani suke kamar fari?

15 Annabi Joel ya kwatanta aikin bayin Jehobah da ayyukan fari. Ya rubuta: “Su kan yi gudu kamar ƙarfafan mazaje; su kan haura ganuwa kamar masu-yaƙi; kowane yana kāma nasa tafarki, gaba daya ne ba mai-ratsewa. Wani ba ya tura wani ba; kowane ya kan bi hanyar kansa: su kan huda hanyar makamai; ba su ratse hanyarsu ba.”—Joel 2:7, 8.

16 Wannan annabcin ya kwatanta masu shelar Mulkin Allah da kyau! Babu “ganuwa” na hamayya da za ta iya hana su yin wa’azi. Maimakon haka, sun yi koyi da Yesu, wanda ya dage a yin nufin Allah duk da cewa mutane da yawa sun rena shi. (Isha. 53:3) Hakika, wasu Kiristoci sun faɗi ta “hanyar makamai” domin an kashe su don bangaskiyarsu. Duk da haka, an ci gaba da aikin wa’azi, kuma adadin masu shelar Mulki ya ci gaba da ƙaruwa. Babu shakka, sau da yawa tsanani ya taimaka wajen yaɗa bishara ga mutanen da ba za su ji saƙon Mulki ba. (A. M. 8:1, 4) Ka taɓa dagewa a hidimarka kamar fari, har a lokacin da ka sadu da mutanen da ba sa son su ji saƙon ko kuma sa’ad da kake fuskantar hamayya?—Ibran. 10:39.

‘Ka Lizimci [Manne wa] Abin da Ke Nagari’

17. Me ya sa ƙafar tsaka take manne wa wurare masu santsi?

17 Kamar ƙarfin maganaɗisu ba ya shafan tsaka. (Karanta Misalai 30:28.) Hakika, masana kimiyya suna mamakin yadda wannan halitta ƙarama take tafiya a bango kuma ta haye silin ba tare da faɗuwa ba. Ta yaya ne tsaka take yin hakan? Ba wai tana da gam a kafa ba ne. Maimako haka, ƙafafuwan tsaka suna da kunya-kunya da ke ɗauke da darurruwan wasu abubuwa masu kama da gashi. Kowane daga cikin waɗannan abubuwa masu kama da gashi yana da ɗarurruwan tsirkiyoyi. Ƙarfin da ke fitowa daga waɗannan tsirkiyoyin ya isa ya riƙe abin da ya fi jikin tsakar nauyin har ma sa’ad da ta yiwo kasa a jikin gilashi! Domin tsaka ta ba su mamaki, masu bincike sun ce za a iya yin amfani da abubuwan da mutane suke ƙerawa da ke da ƙarfi kamar ƙafar tsaka a matsayin gam mai ƙarfi sosai.e

18. Yaya za mu tabbata cewa muna manne wa “abin da ke nagari” a koyaushe?

18 Menene za mu iya koya daga tsaka? Littafi Mai Tsarki ya gargaɗe mu: “Ku yi ƙyamar abin da ke mugu; ku lizimci [manne wa] abin da ke nagari.” (Rom. 12:9) Abubuwa marar kyau da ke ko’ina a duniyar Shaiɗan za su iya sa mu daina manne wa ƙa’idodin Allah. Alal misali, yin tarayya da waɗanda ba sa manne wa dokokin Allah, a makaranta, a wajen aiki ko kuma ta wurin nishaɗi marar kyau, yana iya shafan ƙudurinmu na yin abin da ke da kyau. Kada ka ƙyale hakan ya same ka! Kalmar Allah ta yi gargaɗi: “Kada ka ga kanka mai-hikima ne.” (Mis. 3:7) Maimakon haka, ka bi shawara mai kyau da Musa ya ba mutanen Allah a zamanin dā: “Sai ka ji tsoron Ubangiji Allahnka; shi za ka bauta ma; gareshi za ka lizima.” (K. Sha 10:20) Ta wajen manne wa Jehobah, muna yin koyi da Yesu, wanda aka ce game da shi: “Ka yi ƙaunar adalci, ka ƙi mugunta.”—Ibran. 1:9.

Darussa Daga Halitta

19. (a) Waɗanne halayen Jehobah ka gani a halitta? (b) Ta yaya hikima na Allah za ta amfane mu?

19 Kamar yadda muka gani, halayen Jehobah sun bayyana sarai a abubuwan da ya halitta, kuma abubuwan da ya halitta sun koya mana darussa masu kyau. Idan muka ƙara bincika ayyukan Jehobah, za mu ƙara yin mamaki game da hikimarsa. Mai da hankali ga hikima ta Allah zai zurfafa farin cikinmu a yanzu kuma zai kāre mu a nan gaba. (M. Wa. 7:12) Hakika, za mu shaida gaskiyar tabbacin da ke Misalai 3:13, 18, wanda ta ce: “Mai-farin zuciya ne mutum wanda ya ke samun hikima, da mutum kuma wanda ya ke ɗiban fahimi. Misalin itacen rai ta ke ga waɗanda sun kāma ta; Wanda ya ke riƙe da ita kuma mai-farin zuciya ne.”

[Hasiya]

a Matasa suna iya duba hasiya da ke gaba kuma su yi furci a kan binciken da suka yi sa’ad da ake tattauna wannan talifin a Nazarin Hasumiyar Tsaro a ikilisiya.

b Don ƙarin bayani game da tururuwa mai aikin lambu, ka duba Awake! fitowar 22 ga Maris, 1997, shafi na 31, da kuma 22 ga Mayu, 2002 shafi na 31 na Turanci.

c Don ƙarin bayani game da rema, ka duba Awake! na 8 ga Satumba, 1990, shafuffuka na 15-16 na Turanci.

d Don ƙarin bayani game da fari, ka duba Awake! na 22 ga Oktoba, 1976, shafi na 11 na Turanci.

e Don ƙarin bayani game da tsaka, ka duba Awake! na Afrilu 2008 shafi na 26 na Turanci.

Ka Tuna?

Wane darassi mai kyau ne muka koya daga . . . 

• tururuwa?

• rema?

• fara?

• tsaka?

[Hotunan da ke shafi na 16]

Kana aiki sosai kamar tururuwa?

[Hotunan da ke shafi na 17]

Rema tana samun kāriya ta wajen yin tarayya da juna. Kana yin hakan?

[Hotunan da ke shafi na 18]

Kamar fari, Kiristoci masu hidima suna nacewa

[Hotunan da ke shafi na 18]

Kamar yadda tsaka take manne wa abubuwa, Kiristoci suna manne wa abin da ke nagari

[Credit Line]

Stockbyte/Getty Images

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba