Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 4/1 p. 21
  • Uban Marayu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Uban Marayu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Makamantan Littattafai
  • Jehobah Ne “Baban Marayu”
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Jehobah Ya Ƙi Jinin Rashin Adalci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 4/1 p. 21

Ka Kusaci Allah

Uban Marayu

Fitowa 22:22-24

“UBAN marayu ne Allah cikin mazauninsa mai-tsarki.” (Zabura 68:5) Waɗannan hurarrun kalaman suna ɗauke da darussa game da Jehobah Allah da yake sa mu kusace shi, don yana kula da gajiyayyu. A Dokar da ya ba Isra’ila ya nuna cewa yana ƙaunar yara marayu. Bari mu duba inda Littafi Mai Tsarki ya ambata kalmar nan “maraya,”a da farko a cikin Fitowa 22:22-24.

Allah ya yi gargaɗi: “Ba za ku ƙuntata ma kowane . . .maraya” ba. (Aya 22) Wannan ba roƙo ba ne ake yi don mutane su taimaki marayu; doka ce daga wurin Allah. Yaron da mahaifinsa ya rasu, kuma ba shi da wanda zai kula da shi, zai iya faɗawa cikin wahala a hannun wasu. Babu wanda ya kamata ya “ƙuntata” wannan yaro a kowace hanya. A wasu fassara na Littafi Mai Tsarki, kalmar nan “ƙuntata” tana nufin “tsananta,” “wulaƙanta,” da kuma “yin amfani da zarafin.” Allah ba ya son a wulakanta maraya. Menene ra’ayin Allah game da irin wannan wulakanci?

Dokar ta ci gaba: “Idan ka ƙuntata musu ko kaɗan, sun kuwa yi mini kuka da ko ƙaka, hakika zan ji kukarsu.” (Aya 23) An yi amfani da jam’i “ku” a aya 22, amma a aya 23 an yi amfani da tilo “ka.” Kowanne mutum da kuma duka al’ummar suna bukata su yi biyayya ga wannan doka ta Allah. Jehobah yana kallo, yana saurarar marayu kuma a shirye yake ya taimake su.—Zabura 10:14; Misalai 23:10, 11.

Menene zai faru, idan wani ya wulakanta maraya, har ya sa yaron ya kai kuka ga Allah? “Fushina kuma za ya ƙuna da zafi,” in ji Jehobah, “zan kashe ku da takobi.” (Aya 24) Wani aikin bincike na Littafi Mai Tsarki ya ce, wannan furcin “‘hancina kuma zai yi zafi’ zahiri ne, kuma yana nufin fushi sosai.” Ka lura cewa Jehobah bai ƙyale alƙalai na Isra’ila su zartar da wannan dokar ba. Jehobah da kansa zai hukunta duk wanda ya wulakanta maraya.—Kubawar Shari’a 10:17, 18.

Jehobah bai canja ba. (Malachi 3:6) Yana damuwa da marayu. (Yaƙub 1:27) Shi ya sa yake haushi idan aka wulakanta marayu. Duka waɗanda suka wulakanta marayu ba za su tsira daga “fushin Ubangiji mai-zafi” ba. (Zephaniah 2:2) Waɗannan miyagu za su fahimci cewa “abin ban tsoro ne a fāɗa cikin hannuwan Allah mai-rai.”—Ibraniyawa 10:31.

[Hasiya]

a Wannan furcin “maraya” ya bayana sau 40 a cikin Littafi Mai Tsarki. Ko da yake kalmar nan na Ibrananci tana nufin na miji ne amma ta shafi ’ya’ya mata da suka rasa mahaifinsu. Dokar Musa ta shafi yara mata marayu.—Litafin Lissafi 27:1-8

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba