Rana Mafi Muhimmanci a Tarihi
Rana ce da Yesu Kristi ya mutu. Me ya sa mutuwar Yesu take da muhimmanci haka? Domin wasu dalilai.
Amincin Yesu har mutuwa ya tabbatar da cewa mutum zai iya kasancewa da aminci ga Allah.
Mutuwar Yesu kuma ta buɗe hanya domin wasu mutane su zama abokan sarautarsa a samaniya. Ƙari ga haka, ta buɗe hanya da wasu kuma masu yawa za su more rayuwa har abada a aljanna ta duniya.
A daren mutuwarsa, Yesu ya yi amfani da gurasa marar yisti da kuma jan ruwan anab domin alamar hadayar rayuwarsa. Kuma ya gaya wa mabiyansa: “ku yi wannan abin tunawa da ni.” (Luka 22:19) Za ka tuna wannan abin mai muhimmanci?
Shaidun Jehobah suna gayyatarka ka zo ka Tuna Mutuwar Yesu tare da su. Ranar tunawa ta wannan shekarar ranar Alhamis, 9 ga Afrilu, bayan faɗuwar rana. Za ka iya halarta a Majami’ar Mulki da take kusa da kai. Don Allah ka tambayi Shaidun Jehobah da suke yankinku domin lokaci da kuma wurin da za a yi.
www.watchtower.org